8.

801 97 25
                                    


Sati daya da zuwan Fareeha Kano a wata ranar alhamis da daddare Anti Bebi ta shigo dakin da suke kwana ita da Anti Mami ta sanar musu cewa zasuyi bakuwa washegarin ranar.

"Kanwar Mama ce da take zama a America" cewar Anti Bebi a yayinda ta zauna a bakin gadon"Ta dan jima bata zo ba ne yanzu kuma jikin Hajiyar su yayi tsanani shine zata zo duba ta"

Anti Mami ta jinjina zancen "Allah sarki. Allah ya kawota lafiya"

"Ameen Ameen. InshaAllah wajen goma zata iso dayake jirgin nasu a Abuja zai sauka da asuba, so zata shigo wani jirgin zuwa nan"

Fareeha dai shiru tayi tana rike da Ahmadi a hannunta wanda yayi bacci tuntuni.

"Ina so ku taimaka min wajen shirya mata abinci tunda kunga su Anisa zasu tafi makaranta da safe"

"To Anti me da me za'ayi?"

Anti Bebi ta gyara zama. "An dai kawo kaji so ina tunanin muyi farfesu. Sannan ko za mu kara da Masa da miyar taushe. Sai ayi Kunun gyada ko kuwa?"

Anti Mami ta jinjina kai "Eh hakan ma yayi"

"To saura Lunch. Me zamuyi?"

Su ka danyi shiru kafin Anti Mami tace "Tunda kin ce ba'a nan take ba kuma ta dade bata zo ba ko za'a mata wani abincin gargajiya wanda ba kasafai zata same shi ba a can?"

"Eh kuma hakane. Ina tunanin ayi sakwara amma kar aikin yayi yawa ko?"

Anti Mami ta girgiza kai hade da yin wani guntun murmushi "Ba matsala Anti inshaAllah zamu iya. Fareeha zata taya mu"

Anti Bebi ta mayar da kallon ta kan Fareeha sai taga yarinyar ta mata murmushi alamar cewa babu komai.

"To Alhamdulillah. Allah ya kaimu goben. Mami ni da ke zamuyi breakfast sai Fareeha tayi kunun gyada. Sai Amina ta tayaki ko?"

Fareeha ta gyada kai. "Allah ya kaimu"

Hakan kuwa akayi, ana sallar Asuba suka shiga kicin aka fara aiki ba kakkautawa. Su Anisa ma suka saka hannu suka taya. Karfe bakwai tana yi kuma suka karya suka yi shirin makaranta driver ya mika su. Fareeha ta gama kunun gyada tsaf sannan aka hada ta da yanka fruits.

Ba bata lokaci suka kammala komai sai aka bar Amina da Fareeha su karasa wanke-wanke da goge kitchen. Anti Bebi ta shiga wanka bayan ta bar wa driver sako cewa nan da wasu lokuta zai mika ta airport zata dauko bakuwa.

Ko da ta fito karfe tara ta dan gota don haka da sauri ta kimtsa suka fi ce. Mami suka kara gyara gidan aka saka turaren wuta sannan suma suka yi wanka. Sai a lokacin ne suka samu sukunin karyawa.

Wata annashuwa da bata san daga inda ta zo ba taji ta lullubeta a lokacin da ta shaki iskar garin Kano. Bahaushe yayi gaskiya da ya ce duk wanda ya bar gida, gida ya barshi.

Dan siririn murmushi ne a dauke a kan fuskarta a lokacinda take tura dan karamin akwatinta wanda tayi hand luggage dashi zuwa wajen daukan sauran kayan ta.

Fasinjojin da suko shigo jirgin tare da su duk sunyi cirko-cirko kowa yana jiran kayansa a wajen Baggage Claim. Zuwa wani dan lokaci kayan suka fara zuwa suna tahowa ta conveyor belt. Idonta na kai har sai da ta hango nata kayan. Tayi kokarin jawosu saidai sun yi nauyi. Wani mutum ta samu ya tayata kafin kayan su wuce. Sai a lokacin ta kara jin dama da Muazzam dinta suka taho.

Mutumin ya jejjara mata su a trolley. Ta mishi godiya mai dimbin yawa kafin ta nufi hanyar fita.

Batayi minti biyar da fitowa ba ta hango Anti Bebi tana isowa gareta. Cikin daukin ganin juna suka rungume junansu suna dariya.

"Oyoyo Mama Amma" Anti Bebi ta fada lokacin da ta ke kokarin karban jakar hannun Amma.

Murmushin da ya kasa kaucewa daga fuskarta ta kara fadadawa tana fadin "Bebi na sameku lafiya?"

MaktoubWhere stories live. Discover now