29.

796 145 78
                                    


29.

Da sallama a bakin sa ya shiga falon. Yana sauke idon shi a kanta ya tsaya cak ganin tashin hankalin da ke shimfide akan fuskarta. Ko sallamar ta shi ma kasa amsa masa ta yi, sai idanu data zuba mishi wanda babu komai a cikin su sai rudani.

Shi dai yasan da ya tashi a aiki ya tura mata sako akan cewa zai biya ta gidansu don haka ba zai samu dawowa da wuri ba. Kuma bayan da yayi sallar Maghreb ya sake tura mata wani sakon cewa zai dan yi dare. Don haka baya tunanin tashin hankalin dake bayyane akan fuskar ta na da alaka da rashin dawowar sa da wuri.

A hankali ya furta "Me ya faru?"

Wani abu mai nauyi Wafiyya ta hadiya kafin idanunta suka ciko da hawaye. "Ummi ce..."

Bata karasa maganar ba wani kuka ya kwace mata. Ai bai san lokacin da ya cike space din da ke tsakaninsu ba, ganinta kawai yayi a cikin rikonshi.

Kuka take sosai wanda hakan yasa hankalin sa ya tashi. Sai kuma a lokacin ne ma ya lura da cewa Ummi bata falon. Ba haka ya saba gani ba don tunda tazo gidan nan ne wajen zaman ta. Ganin hakan yasa zuciyar shi ta kara bugu.

"Kiyi shiru Wafee ki fada min meya sameta?" Ya tambayeta yana kokarin share hawayen da ya wanke mata fuska.

Cikin shesheka ta ke fadin "Tun safe wata kawar ta tazo ta dauke ta wai zasu je siyayyan kayan kitchen, shiru-shiru har la'asar banji ta ba na kira tace wai sun je salon wanke kai da yin lalle. To tun da lokacin kuma idan na kira wayar a kashe. Gashi har yanzu bata dawo ba"

Wani nannauyan numfashi Ashraf ya sauke.

Kai Ya Subhanallah.

Har ga Allah ya zaci wani mummunan abu ne ya samu Ummin don babu irin tunanin da bai yi ba a wannan lokacin, amma ashe abin ma da sauki.

Ya kalli Wafiyya ta kasan idonshi da guntun murmushi a bakinsa. "Yanzu dama saboda Ummi bata dawo bane shi ne kike kokarin bani heart attack?"

Kara kankame shi tayi tana matsar kwalla. "Kayi hakuri wallahi na tsora ta ne shiyasa."

"To shine hadda kuka? Ai Addu'a zakiyi Allah yasa ta dawo lafiya. Kuma ma dai Ummi kam ba bata zatayi a garin Kano ba, maybe wayar ce ta mutu. Don haka ki kwantar da hankalinki"

Ita ko ta san ba bata zatayi ba, kawai dai bata so ya gane cewa mahaifiyar tata ta bude wata sabuwar harkalla ce a yanzun don itama sai a safiyar yau dinnan ta fahimci hakan ganin an turo direba da katotuwar mota don a zo a dauketa.

Koke-koken da take duk dan kar Ashraf yayi tunanin wani abune idan Ummin ta dawo can dare, wanda kuma hakan take fata don idan ta sake ta kwana a wani wajen to ta zubar mata da mutunci a idon mijinta da ma zuri'arsa baki daya.

Sake narkewa tayi a jikinsa tana addu'ar Allah ya dawo da ita lafiya. Sannan kuma ta kudurci cewa a yau dinnan zasuyi maganar da suka dade basuyi ta ba, don ita kam bada ita za'ayi wannan aika-aikar ba. Ko ta bar mata gida ko ta koma inda ta fito, ita kam ta fara gajiya.

Cikin tausashiyar murya tace "In kawo maka tea? Nasan kaci abinci a gida"

Ya shafi gefen kumatunta. Wajen har yanzu da damshin hawayen ta. "Ya akayi kika san naci abinci a gida?"

"Kana ta warin miyar kuka"

Dariya ce ta kubce masa wanda ta ke jin shi har cikin bargonta. "Allah ya kamaki to ba ma miyar kuka naci ba"

"Ni dai abin da hancina ya jiye min kenan"

Ya lakaci hancin nata "Wannan hancin to ya fada miki karya. Yanzu dai bari naje nayi wanka don kin sa ma tsargu da kaina"

MaktoubWhere stories live. Discover now