Announcement

745 63 57
                                    

Assalamu Alaikum my loves😍❤🥰.

Nasan da yawa daga cikin ku basu so ance an gama littafin nan ba, ku sani cewa ina daya daga cikinsu. Wasu kuma sun ce sam sam wannan labari bai cika ba akwai sauran rina a kaba; wannan kuma haka yake.

A yadda na tsara labarin Fareeha yana da tsawo amma duba da yanayin yanda nayi ta jan labarin yasa na tsagaita da shi a haka ko wasu sa samu su karanta saboda akwai wanda sun kasa karantawa saboda ba'a gama ba.

Da haka ne kuma nake so na sanar da ku cewa labarin Fareeha zai ci gaba (idan kuna so ayi part 2 ko kuma a cigaba a wannan littafi) don kuwa akwai sarkakiya dayawa danakeso na warware (please don't tell me you've forgotten about Misriyya because she's a relevant part of this story and also Ashraf and Wafiyya's story has not ended too. Uwa Uba ga Anti Mami again).

Duk wanda kuka zaba hakan za'a yi sai dai ku sani ba'a nan kusa ba don yanzu na saka wani sabon project ne a gaba.

Ina da littafai biyu sabbi wanda na fara.

Na farko shi ne UNINTENDED VOWS wanda zaku same shi a shafin Bakandamiya wanda na rubuta shi da harshen turanci. Chapter kwaya daya ce, ina bukatar mutane dayawa su karanta shi kafin na cigaba da shi (at least 500 reads). Wannan littafi kyauta ne.

Sannan littafi na biyu shine BUGUN ZUCIYA wanda nake rubuta shi a harshen hausa. Wannan littafi na kudi ne kuma zan rubuta shi a manhajar Telegram. Domin neman karin bayani a kan littafin sai ku ziyarci shafina na Instagram @miryamah.writes

Duk wani bayani zaku same shi a can ta yanda zaku biya da yanda za'a shigar da ku cikin group din littafin.

Ina fata masoya Fareeha da Uncle Captain zasuje su nunawa sabbin littatafai na kauna kamar yanda kuka nuna min anan.

Ina alfahari da ku matuka. You guys have made my writing journey an eventful one. Allah ya saka muku da mafificin alheri.

Taku a kullum,
Miryamah

PS: Don't ask me about Loving Zarah, ina sane dashi😂.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 08 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MaktoubWhere stories live. Discover now