Hibba
Ina isa gidan, naci karo da wata makeken gate, wani irin tsoro da firgici ne ya ziyarce ni danaga yanayin girman gate din, daga wajen bana iya hango ciki amma babu tantama gidan nada girma, na sake dubawa naga daidai ne da address din da aka turo mun.
Kokarin kawowa zuciyata jarumta nayi na karso wajen gate din na soma kwankwasa, nafi minti goma tsaye a wajen ina kwankwasawa ba ansa ba, idanuna suka sauka kan wani abu mai kamar kararawa an manna a jikin gate din naje na danna, cikin sa'a kuwa bafi minti biyu ba naji murya ance waye. Waige waige na somayi naga babu alamun mutum nayi shiru zuciyata cike da fargaba, can na sake jin murya ance "who is there".
Fidda tsoro nayi, nayi gyaran murya sa'anan nace "bakuwa ce, nazo ganin mai gidan ne".
"Kinada appointment dashi?" Ya tambayeni cikin kakausan murya.
Saurin hadiya nayi nace " a'a amma..."
"Babu appointment, babu ganin mai gida"
Nan take gabana ya yanke ya fa'di jin ansar daya bani nayi saurin fa'din "dan Allah tsaya, shi da kanshi ya turo mun da sako yace nazo"
Shiru yayi sai kuma can naji ance "ya sunanki?"
"Hibba...Hibba Abdullahi" nayi saurin bashi ansa.
"Ki jira nan da yan mintuna". Yana gama fa'din haka ban sake jin komai ba. Nayi shiru ina tsaye a wajen cike da mamakin yanda yake mun magana ba tare da ya ganni ba? Nafi minti shida tsaye a wajen sai faman waige waige nakeyi, zuciyata cike da fargaba, gabadaya a tsorace nake, ga unguwar ma wata duniya ce ta daban, can sai naji murya ance mun "kina iya shigowa".
Karar gate dana ji ya soma buduwa ne yasa na matsa baya cikin sauri, ba tare da ba'ta lokaci ba na dauki yar jakata na shige ciki. Ina shiga ciki numfashi kusan daukewa yayi, wata katuwar makeken gida na gani a gabana, an ginata da fararan dutswatsu sai faman kyali take, tsayawa lissafa hwansa nawa ma ba'ta lokacine, ga wutan lantarki na haskaka ko ina, na tsaya curuss ina bin ko ina da kallo, wanan ai ba gida bane, gari guda ne na fada cikin raina ina karewa ko ina kallo, zuciyata ta harba da karfin gaske,
daga bakin gate zuwa gidan, wata katuwar abu ne daban san sunansa ba zagaye da flowers yana fidda wuta da ruwa. A hankali na soma takowa ina motsa kafata har na zo tsakiyar farfajiyar gidan, daga inda nake tsaye ina iya hango wata katuwar filli mai dauke da kwantaciyar ciyawa ga lilo kala kala na yara, da kujeru kala kala na shakatawa, hade da lambu da bishiyoyi iriri, ta damata kuma wata rumfa ne mai dauke da tsdadun motocci kala kala akala zasu kai goma motocin nan. Ga wata katuwar swimming pool cike da ruwa.Gabadaya abubuwa da nake gani cikin gidan yayi mugun dauke mun hankali har na manta inda nake, sai faman kalle kalle nake ina bawa idanuna abinci ina jin wani irin nauyi a can kasan zuciyata, tsoro da firgice ne suka ziyarceni lokaci guda ina tunanin wanda zanje na tadda a ciki, don nasan ba karamin mutum bane dazai mallaki irin wanan duniyar.
Inama inama na shiga tambayar kaina, inama babu wata bashin million da'ri a kasa, inama iyayen mu basu mutu a wanan hatsarin ba, inama Anty Ladi bata tsanemu haka ba, inama kawu Abu baiyi kokarin cin zarafin mu ba.....inama inama
Numfashi naja na sauke, babu gudu babu jada baya tunda na kawo kaina, yau za'a yita ta kare. Ina cikin wanan tunanin na soma jin haushi daga bayana, cikin sauri na waiga naga wata katuwar kare baka ta nufo ni gadan gadan, wani irin razana nayi hantar cikina ta kada, kafa me naci ban baka ba a guje na arce ko waiwaya bana yi karen nan na bina a baya, gudu nakeyi gudun tsira gudun ceton rai, har na kawo daidai wata bishiya ina kokarin na haura don na saba hawa bishiya bata mun wahala, wani abu ne naji ya ta'de mun kafa sai gani nan ni nan warwars a kasa kan jikaken ciyawa, Ban ruwa ne kwance a wurin yana bawa ciyawu da flowers ruwa yasa ko ina ya jike, Duk dattin ruwan ta'bon nan haka naji ta fuskata, har cikin bakina na soma kokarin tofarwa. Sai faman zaro ido nakeyi ina kokarin fahimtar abunda ya faru, gabadaya jikina ya bace da datti. Ga karen nan ya tsaye ta daga can gefe sai faman haushi yake mun.

VOUS LISEZ
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
Roman d'amourHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...