*Hibba
Loma da'ya biyu nayi naji na kasa daina cin abinci saboda bala'in da'din dana ji ya rasta kwakwalwata, tunda nake ban ta'ba cin abinci mai da'di irin wanan ba, gashi yazo ya hade mun da yunwa, sosai na dage ina ci, na da'go muka ha'da ido naga ya bar abincinsa ni yake kallo. Nan take naji kunya ya lulu'be ni ajiye cokalin na juya ina kallon wani gefe.
"Why did you stop? Kici abincinki mana"
"Ni ka daina kallona" ta fa'da ina turo baki, yayi shiru sa'anan yace
"When last did you eat? You look like you haven't for days"
"Ban ci ba... tunda na bar gida ban samu na zauna naci abinci ba" na fa'da mishi muryata kasa kasa na juyo ina kallon kwanunsa naga har ya kusan cinye abincinsa, bai sake cewa komai ba nikam na dawo da dubana ga abincina na cigaba da ci. Duk yawan abincin kwanuna sai dana cinye tass
"So you can eat like this?" Naji ya tambayeni da murmushi a gefen bakinsa, yana mamakin yanda na zage naci abincin da kyau
Kawar da fuskata gefe na sake yi, bazan iya denying cewa ina matukar son abinci ba, ko lokacin muna kanana, Ammar ya lakana mun suna "Ya' Hibba acici" sai na tashi da abincina shi yana zaune yana ci, sam bana wasa da cikina ina bashi hakinsa daidai gwargwado.
"Kin koshi?"
Gyada masa kai kawai nayi.
Murmushi ya cigaba dayi ganin yanda na kasa ha'da ido dashi ina kallon gefe, naga ya kira waiter, cikin sauri wanan ya karaso ya tambayeshi nawa bill dinmu, waitern ya sanar dashi, babu musu ya ciro card dinsa ya mika masa, ni kuwa na sake baki ina mamakin kudin da aka ambato, ko dayake ba komai bane a wajensa tunda yanada kudi.
"shall we?" Naji ya fa'da ha'de da mikewa bayan ya gama da waitern. Nan take naji cikina ya duru ruwa, nasan lokaci yayi dazan samu nayi magana da kanina amma sai na tsinci kaina da fargaban sanin halin da yake ciki.
Mikewa nayi, muka fito tare yana rike da hannuna, muna isa waje naji wani irin sanyin iska yana ratsa duk ilahirin jikina, a hankali naji ya daura hannunsa bisa kafadata ya sake matso ni jikinsa ya rike ni gam, na da'go na kalleshi, a raina ina fa'din meye matsalarsa ne da son kamo ni haka a bainin jama'a? Ni ba guduwa zanyi ba, ina ma zan gudu naje bayan inada kani da zan ceto a hannunsu.
Haka muka cigaba da tafiya, wani tunani ya fa'do mun nace " ya akayi kake bin Ammar bashin million da'ri?"
Juyawa yayi ya kalleni ha'de da da'ga mun gira, murmushi bayane a handsome face dinsa "so kike kisan details din?"
Tambayata yayi as if he's amused irin bazan iya gane yanda suke harkan business dinsu ba.
"Yes tell me, inaso na sani"
"Caca" ya fa'da mun kai tsaye
"Caca? Na maimaita "ai Ammar baya caca... be ma san yanda akeyi ba"
"No baya yi amma abokanansa"
Nan take naji wani irin abu ya tsargar mun. Abokanan Ammar....abokanan da yaketa mun maganarsu kafun yabar Maiduguri, sune suka jefa shi cikin wanan halin, dubansa nayi muryata a raunane nace "dan Allah ku tausaya masa...Ammar karamin yaro ne, baisan..."
"kema haka" ya katseni yana murmushi, nayi shiru don nasan yanada gaskiya, dukda shekaruna, nasan banida wayon da zan fahimce yanda suke abubuwansu. Na dawo da tunani kan Ammar, meyasa zai je ya jefa kanshi cikin wanan matslan da irin waenan mutanen? Ya akayi ma ya ha'du dasu har ya fara irin wanan harkan? Tambayoyin da naketa yiwa kaina kenan ban samu ansa ba na cigaba da tafiya, har mun doso inda yayi parking motarsa naji ya tsaya cak, cikin sauri na da'go ina dubansa naga faral da'ya mood dinsa ya canza, ya mayar da hankalinsa can wani gefe yana kallo, kafun nayi wata magana naji ya kamo hanuna ya soma jana cikin sauri yana kokarin karasa dani wajen motan, hankalina ya tashi ko meke shirin faruwa oho, ai kuwa kafun mu karasa naji wani irin karan tire na goguwa kan kwalta ya karade ko ina ban san sanda na saki kara ba nayi saurin boyewa a bayansa.

VOUS LISEZ
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
Roman d'amourHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...