Hassan
Hassan yana barin lounge din straight apartment din Ak ya nufa don neman Hibba, tunda Ammar ya shigo yana masa wanan borin akan contract jikinsa ya bashi bata je wajen spa kamar yanda ya umar ce ta ba, taje ganin kaninta.
Shi kanshi da yake rubuta mata wanan note din yasan da wuya taje, zata gwamace ta kasance da dan uwanta, tun safe daya farka yaga bata tashi ba tanata faman baccinta ya bata space bai wani dameta ba don yasan tana bukatan hutu sosai, sai dai throughout zaman shi da AK suna hira, tunaninta ne fal a ransa, ta kasa barin kwakwalwarsa, abun yazo ya ha'de masa da maganar Ammar akan kawunsu da yake molesting dinta, yaji sam zuciyarsa bata zauna da batun wani na kokarin ta'ba masa Hibba ba, wani irin zallar baccin rai ne da haushi ke ziyartarsa a duk sanda ya tuna, abubuwa na neman kwance masa, yanzu ji yake duk duniya babu wanda ya tsana sama da kawun nasu tunda har yanada guts din da zai ta'bata.
Lift din na kaiwa floor na apartment din yaja ya tsaya, ya fito ya karaso bakin kofar ya soma kwankwasawa a hankali, yana jin yanda kirjinsa ke harbawa d matsanancin karfin gaske yana Allah Allah yaga yarinyar da take kokarin rikita masa lissafinsa.
Yana cikin wanan tunanin kofar ta dan' budu ya jiyo lalausar muryarta na fa'din "Ammar?" yanayin data kira sunan cike da so da kauna da damuwa akan dan'uwanta ya sashi tunanin ko wata rana shima zata kira sunanshi cike da so da kauna haka? Wanan tunanin na fado masa immediately ya kawar dashi daga ransa, meyasa zai dinga irin wanan tinanin akanta bayan ga abunda yake tsakninsu? she's just his mistress in exchange for that money, no strings attached, no emotions.
A hankali ta idasa bude kofar,idanunsa suka sauka kan lovely face dinta mai dauke da busashen hawaye, tana ganinshi ta zaro ido cike da tsoro, nan take Hassan yaji kirjinsa ya masa wani irin tight, wani abu yazo ya toshe mishi makoshi, sam bai son ganinta cikin irin wanan yanayin firgici da tsoro, musaman idan ya kusantota, sai yanzu ya gano dalilin tsoron nata, kawunta....duk shine ya hadasa mata tsoron namji a cikin zuciyarta, shi kanshi tunda Ammar ya sanar dashi irin abun data dinga facing tasowarta yaji gabadaya kansa ya ri'ke, yanzu da yake tsaye a gabanta suna kallon cikin kwayar idanun juna ji yake kamar ya janyo ta jikinsa ya rungume, ya kwantar mata da hankali, ya bata assurance na cewa everything is going to be alright as long as she's with him, ya tsura mata tsumamin idanunsa yana kallonta cike da matsanancin shaukinta yana jin yanda kirjinsa ke bugawa da matsanancin karfi akanta, ya rasa gane kan waenan feelings din, ji yayi gabadaya duniyarsa na neman canzawa akanta.
A hankali yaga ta gyada kanta gefe tana kokarin leka bayansa ta dawo da dubanta gareshi tana fa'din "oh na zata Ammar ne...ina ka baroshi yana ina?"
He couldn't help it, wani irin abu ne yaji yana tasar masa game yanda take nuna damuwarta kadai akan dan'uwanta, batada tunani kuma batada maganar kowa sai nashi, gabadaya Hassan yaji abubuwa sun hargitse masa, Ammar! Ammar!! Wani irin kishi na kokarin taso masa yayi kokari ya danne, ya za'ayi ace yana kishi da son da take yiwa dan'uwanta? Bai ta'ba jin yayi kishi game da wani abu a rayuwarsa ba sai wanan karon, yanada tabbacin babu wanda zai iya replacing Ammar a ranta. Toh taya ma? You can't compare a siblings love to another, Ammar ne kadai familyn da take dashi, wa kake tunanin zata damu da bayan shi? wata zuciyar ta tambayeshi.
Dogon numfashi yaja ya fezar, a halin da ake ciki yanzu, she only needs comfort, don haka ya mika hannu ya janyota ya rungumeta bisa kirjinsa yana ajiyar numfashi ya lumshe ido yana shakar dadaden kamshin turaren jikinta yana jin wani irin sanyi na ratsa duk ilahirin jikinsa, sunfi 5 minutes a hakan ya da'go yana duban kyawawar fuskarta yana shafa a hankali yana jin yanda zallar tausayinta ke ratsa shi, gabadaya he's confused yana cikin dilemma da feelings dinsa, sam baison yayi sakaci da zuciyrsa, yana tsoron abunda zai biyo baya don tausayi shi ke rikidewa ya zama so, shi kuma he's not ready for that kind of emotion, saurin kawar da tunanin yayi ya gyara tsayuwarsa still yana shafar fuskarta yace "are you ready for lunch?"Shiru tayi tana dubansa daga bisani ta girgiza masa kai "a'a ina jiran Ammar"
Ammar again.... ya fada can kasar zuciyarsa, saurin kawar da tunanin yayi yace "Bazaki ga Ammar yanzu ba, he's busy with AK"
"Oh.. sai yaushe kenan zan samu ganinshi?" ta tambayeshi fuskarta cike da damuwa.
"Later" kawai ya ba'ta ansa ya kamo hannunta ya jata suka fito tare.
Sorry for the delay lovelies❤️ Anty Nabila, ema binu🥺

YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...