Maryam
Sai faman zarya take tana kai kawo cikin daki zuciyarta na tafarfasa hankalinta a mugun tashe, idan akwai abunda tafi tsana a duniyar nan bai wuce yar iska shegiyar karuwan nan da Mr Sooraj ya kawo ya ajiye musu a gida ba, daman tun farkon zuwan yarinyar gidan, ranar data fara daura idanunta akanta taji sam bata kwanta mata, taji ta tsaneta kuma tsana mafi muni, ita babu abunda yafi da'ga mata hankali kamar yanda take zaune a gidan babu ranar tafiyarta, tun randa suka shigo da Hibba ta nemi nutsuwarta ta rasa a cikin gidan tana so ta gano takamame meye tsakaninsa da yarinyar amma ta gagara gano komai. Meyasa oga zai kawo musu cikin gida ya ajiyeta babu wani bayani? Tasan ogansu da mugun tausayawa da taimako kilan tun ranar data fara zuwa mishi ya sallamata bata daddara ba ta sake zuwa ta like masa, Ga wanan kayan haushin diyar tasa Faheema sai faman shishige mata takeyi, Maryam tanada tabbaci duk Faheema ce ta jawo aka kawo yarinyar gidan kuma dayake uban nata yana shegen jin maganarta ya amince mata. Maryam tasa hannu ta ciza yatsarta, dole ta mike tsaye bata ga ta zama ba, ita da takeda buri da dama akan Mr Sooraj, bata ta'ba tsintar kanta cikin kogin son wani da' namiji kamar yanda take mutuwar sonsa ba, tun ranar data fara dora idanunta akansa ta rikice taji duk duniya babu wanda takeso sama dashi.
Maryam bafulatana ce yar'Adamawa gaba da baya amma suna zaune anan Bariga dake cikin garin Lagos, bata fito gidan masu hali ba, su uku ne a wajen iyayensu kuma duk mata, babbar yayarsu Hajjo itace take daukar nauyinsu gabadaya gidan kasancewa tana auran wani hamshakin mai kudi suna zaune a VI, ita kanta Hajjo ba wani jin dadin zaman gidan miji takeyi ba don itace ta uku a wajen mijin nasu, kishiyoyi sun sata a gaba, basu zaman lafiya sam, sai dan abunda ta samu take dan banta'lowa ta kawo musu gida. Gata da shegen bin mallamai da bokaye, mahaifiyarsu wace suke cewa Adda itace ta dorata akan wanan gurba'taciyar hanyar. Maryam dayake Allah ya mata baiwar kyau sanadiyar haka yasa ta dorawa kanta girman kai tana daukar kanta tamkar wata sauraniya, wanan aikin ma data samu tanayi a gidan Hassan, Hajjo ce ta samo mata, dayake Madam Laide ta ta'ba aiki a kamfanin mijinsu Hajjo kafun ta dawo gidan Hassan da aiki yasa ta yiwa Hajjo magana sanda yake nemarwa Faheema Nany, Hajjo dataji irin makudan kudin da Hassan yace zai dinga biya don a kular masa da yar'sa yasa ta kira Maryam ta shaida mata, da farko Maryam tace bazatayi ba saboda a ganinta ta wuce level irin wanan aikin, da kyaunta da komai bazatayi aikin Nany ba, Hajjo tace toh ita dai idan bazata samu abunyi ba tana tallafawa a gida zata janye hannunta don itama fama takeyi, mijinta Alhaji shegen rowa ne dashi, sai da wayo da dabara suke samu daga wajensa, data nunarwa Maryam hakan da kuma irin kudin da zata dinga samu idan tana aiki a gidan yasa ta amince, farkon zuwanta gidan a ranar taje bata samu Hassan ba aka ce mata oga baya nan, sai washe gari data kuma zuwa yayi inviting dinta zuwa office dinsa, tayi shigarta irin classy shigar nan na cikkakiyar mace wanda duk namijin daya ya daura idanunsa akanta sai ya sake kwadayin kara kallonta, tanada irin dirin nan na cikakun mata masu tsananin ji da kansu, knocking tayi hade da sallama ta shiga ta sameshi zaune akan kujera yana duba wasu takardu dake zube akan table, yana dagowa sukayi ido biyu Maryam taji numfashinta ya tsaya cak na yan sekoni, bata ta'ba tunanin Mr Sooraj din matashi kuma kyakyawa ne kamar haka ba, baki ta sake tana binsa da kallo, a tunaninta wani tsoho zata tadda irin Alhajis dinan, shi kuwa kallo da'ya ya mata ya nuna mata wurin zama sa'anan ya mayar da hankalinsa kan takardun dake gabansa, ya dau' kusan 10 mins sai daya gama tukuna ya dawo da dubansa gareta, ya kafeta da mayyattun idanunsa, Maryam ta sake rikicewa, cikin i'ina ta soma gaidashi, duk wanan confidence din nata ta nema ta rasa a wanan lokacin, ya ansa mata in a calm manner, tambayoyi ya shiga mata tana bashi ansa, ta nuna mishi tana son yara zatayi delivering services dinta 100% kar ya samu damuwa, a wanan lokacin ya gamsu da yanayin data dinga bashi answer don haka ba tare da ba'ta lokaci ba ya dauketa aiki, murna a wajenta kam kamar meye ta kira Hajjo ta sanar da ita, ta zayane mata komai ciki kuwa har da zalamanta akan Hassan, tace bata ta'ba tunanin haka mutumin ya hadu ba, Hajjo tayi dariya tace "ai shiyasa kikaga na takura kije, kina tunanin ban san me nakeyi bane? da biyu na turaki ai idan kika samu shiga wanan gidan mun huta Maryama, Maryam cike da jin dadi tace "Allah ko yayarmu?"

YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...