Chapter 63

1.3K 71 7
                                    

Maryam

Sai wuraren karfe uku na rana Hajje ta dawo gida ta ja Maryam zuwa daki suka rufe kansu ciki, nan ta soma yiwa Maryam bayanin abunda boka yace "ai na gaya miki akwai wata a kasa don ni nasan aikin Ojakinwa , aikinshi kamar yankan wuka yake, yanzu naje wajensa na masa bayanin yanda ake ciki, ya kara bincikawa yana dubawa kuwa ya gano, ashe yanada tsari ne sosai a jikinsa kinsan Mahaifinsu dan mafiya ne kamar yanda mutane suke zato don haka bai bar yaransa haka ba tunda ya daurasu kan business dinsa dole ya nemo musu tsari, shiyasa kikaga abun baiyi tasiri akansa ba, kuma yanda Ojakinwa ya nunar mun dole sai an karya wanan tsarin dake jikinsa tukuna a samu magani ya shigeshi, yanzu dai yace mu kwantar da hankalinmu yasan me zaiyi, yace ana bukatar saniya guda uku da za'a yanka, da kuma kawunan kada suma guda uku, da dai sauran abubuwa nidai nace mishi bazamu iya kawo masa waenan abubuwan ba amma ga kudi nan na aje a siya, wlh Maryam sai dana ajiyewa Ojakinwa naira dubu dari takwas cash don a samu a siyo waenan abubuwan.."

"Kai yayarmu" Maryam ta fada tana zaro ido.

" wlh amma karki damu, ai don gaba ake yinta mun kusan cin moriyar abun don haka ki kwantar da hankalinki kar kiji komai, I didn't even think twice nayi masa transfer din kudin, yanzu dai yace nan da kwana uku mu dawo zuwa lokacin ya kamala aiki, sai muzo yayi mana bayani, sha kuruminki kinji ko, ki saki ranki"

"Toh yayarmu, nagode nagode. Allah ya bar mun ke yayata, Allah yasa kifi haka"

Maryam ta fada a sanyaye can kasan ranta tana tunanin ita nata plan din data rigada ta ha'da, dazun sukayi magana da Kawu Abu suka gama tsara komai don haka bata wani damu kanta sosai ba don tasan komai zai tafi daidai, bata sanar da Hajje batun Kawu Abu ba sai komai ya kankama tukuna zata fada mata, da wanan suka tsayar da maganarsu, Hajje ta cigaba da bata baki tana kokarin kwantar mata da hankali.

********************

Hibba

Misalin karfe hudu da rabi na yamma, Ina kwance a daki na idar da sallah kenan, gabadaya naji yanayina sai a hankali, tunda Hassan suka fita naji gabadaya na nemi nutsuwata na rasa, gabana nata yankewa yana faduwa, ina jin wani irin fargaba na ziyartata from time to time.

Ni kadai ce a dakin don tun dazun na shirya Faheema, driver ya kaita Islamiya, daga ni sai masu aikin gida dasu Madam Laide suna kasa. Tunanina ya koma ga Hassan naji bugun kirjina ya dada karuwa, ko dayake yace sai zuwa Yamma zai dawo, don ko dazun ma ya kirani yaji ya jikina nace mishi da sauki, ni bansan meyasa duk yabi ya damu kansa haka ba don nidai nasan lafiyata kalau.

A hankali na mike na sauka kasa na karasa kitchen na tadda Baraka tana faman girke girke na leka naga rice and stew take kokarin hadawa, ga dankali da fere a gefe zata soya da sauce daman most of the time abinci kusan kala uku ake dafawa a gidan a ko wani lokaci, sai ka zaba wane zaka ci, Baraka na ganina ta washe baki daman tunda nazo gidan naji jinina ya hadu da ita, muna hira sosai da ita don ita batada matsla, barairabiya ce kuma tana bani respect sosai.

Tambayata ta soma yi ko akwai wani abun da nakeso ta dafa mun naci nace da ita a'a, I'm okay don a lokacin bana wani jin yunwa sosai kawai marmarin biscuit nakeyi, daman akwai ragowar cookies dana bari cikin fridge naje na dauko da lemu mai sanyi na fara sha, nasha sosai sa'anan na sake haurawa sama zuwa daki na dan watsa ruwa a jikina, shigana daki kenan ina kokarin tube kaya naji sako ya shigo mun waya, a tunanina Hassan ne don haka cike da doki na karasa naje na dauka naga ba shi bane, bakuwar number ce, bude messages din nayi na soma karanta sakon ciki, kamar haka

"Ya'Hibba Ammar ne.... dan Allah ki taimaka ina cikin wani hali, gani nan nazo garin Lagos, zaman Abuja ya gagareni mutanen nan suna neman su hallakani, abun ya isheni bazan iya ba kuma, dan Allah kizo ki sameni, please kizo ke kadai karki sanar da kowa gani nan a wani wuri ana ce masa Ijora bustop, kowa kika tambaya zai miki kwatancen wuri kizo ina jiranki, dan Allah karki sanar da Mr Sooraj nazo"

kusan yarda wayar nayi na dafe kirjina ina zaro ido, nan take naji wani irin zufa ya soma karyo mun ina karanta sakon ciki over and over again, jikina na ba'ri na soma dialing number amma naji number busy, na jira na kuma trying still layin busy ake dana mun hankalina ya kara tashi, a kidime na lalubo normal number Ammar da nake dashi na soma kira naji a kashe, na rasa yanda zanyi. Lokacin na duba naga biyar saura naje wajen wardrobe dina na ciro hijab, ha'de da daukan dan canjin daya rage mun daban san ma iya adadinsu ba na cusa cikin jaka na fito a guje, ban tsaya yiwa su Baraka wani bayani ba nace musu ina zuwa yanzu zanje na dawo, haka na fita kirjina na dokawa hankalina a matukar tashe na bar gidan don neman kanina.

Not edited
Read and vote please ❤️

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now