Hibba
Tafiya nake ina tunani, sai faman waige waige nake don bansan inda na nufa ba, ga yamma ya gabato, gashi ban samu nayi sallah ba duk cikin wanan rud'anin, babu abunda yake mun yawo a kwakwalwa ila million da'ri da kuma inda zan nemo.... badai zaki amshi wanan offer din mutumin nan ba? Wata zuciyar ta tambayeni. Saurin kawar da tunanin nayi ina fa'din Allah ya sawwake, bazan ta'ba saida jikina ba, bazan ta'ba zama karuwarsa ba tunda abunda yake nufi kenan.
"Amma kin gwamace kaninki ya cigaba da zama a hannunsu? Kin gwamace su azabtar dashi? Kada ki manta Komai zai iya faruwa... Ammar kaninki ne, ya kamata ace komai zaki iya masa don ki ceci ransa" wata zuciyar ta fa'da mun.
Hannu nasa ina share hawayen da ya gangaro mun, hakika zan iya yin komai don naga na ceto kanina, shi kadai ne gareni, bazan iya barin wani abu ya sameshi ba, yana bukatata a rayuwa kamar yanda nima nake bukatansa. Dole na nemo musu kudinan kota halin yaya ne.Cigaba nayi da tafiya, kafafuna da kyar suke iya daukata, ga makoshi na ya bushe saboda rashin ruwa, ga wani azababen yunwa daya sani a gaba, dubawa nake ko zan samu shago da ake siyar da biscuits na siya naci don nasan idan na cigaba da tafiya a hakan zan iya sulalewa kasa na fa'di, na tsaya na bude jakata na ciro yar dubu daya data rage mun na cigaba da tafiya.
Sai danayi tafiyan kusan 30 mins tukuna na kawo bakin titi, na hango wata shago cikin sauri na karasa cikin shagon nace su ban biscuits da lemo kwalba, jikina har ba'ri yakeyi na samu wuri a gefe na zauna na soma ci. Ina gama ci na mike na kakaba jikina na dauki yar jakata, na cigaba da tafiya ina tunanin ko masallaci zan samu na shige na kwana. Tunanina ya sake komawa ga Ammar, can kasan raina ina addu'a Allah yasa yana lafiya, gashi an bani zuwa jumm'a, ya zanyi? In badai fashi zanyi ba a banki ina zan samu ku'di?, ina cikin wanan tunanin naji karan tire na goguwa kan kwalta, cikin sauri na waiga naga wata bakar mota ta doso ni, zaro ido nayi, nidai na shiga uku da motoccin garin nan dake neman suga bayana. Cikin sauri na matsa, Wani irin reverse motar tayi, ta sake yo kan gefen hanya inda nake, kara na sake ina kokarin kaucewa mahaukacin naga yazo yayi parking dab dani, Raina in yayi dubu ya bacci dukda firgicin da nake ciki bai hanani rufe ido ba na soma sauke ruwan bala'i "wani irin hauke ne wani irin iskanci ne wanan? Drivern zai ce bai gani bane ina tafiya a gefen hanya ko meye?"
ina tsaye ina jiran naga wa zai fito na zazzage masa daman a cike nake kiris nake jira, mutumin daya bayana a gabana ne yasa naji kayan cikina sun ka'da, zaro ido nayi ina binsa da kallo kamar naga dodo, bai tsaya wata wata ba ya karaso yana fa'din
"shiga mota"."Akan me?" Na tambayeshi ina binsa da kallo, kamar yasan zan musanta shiyasa yazo a shirye, yasan abunda zai fa'da mun wanda bazan ta'ba ce masa a'a ba, waya ya miko mun yace "Kaninki yana son magana dake".
Wani irin farin ciki ne naji ya lulubeni na mika hannu zuciyata cike da hope ina kokarin karban wayar ya dauke hannunsa nan take naji zuciyata ta karaya "ka bani waya nayi magana dashi"
"Zakiyi magana dashi amma ba yanzu ba sai kinyi deciding, now shiga mota mu tafi karki bata mun lokaci". Shiru nayi naki motsawa yace "ko sai na taimaka miki ne?"
Bai jira yaji answer da zan bashi ba, ya kamo karamar hannuna cikin nasa, wani irin yarrrr naji cikin sauri na soma kokarin janyewa naji ya rike ni gam, a hankali ya soma ja' na, tsintar kaina nayi da bin bayansa ya bude motar ya zaunar dani, kafun nayi wata magana yayi saurin rufe motar, yaje ya zagayo ya bude wajen driver ya shiga ya zauna.
Juyowa nayi ina dubansa, ina jiran naga ya kira mun Ammar, naga ya tada engine mota, "ina zaka kaini? "Wajen Ammar zamu? Na tambayeshi hankalina a tashe
Juyowa yayi yana dubana da kyawawan idanunsa, ya da'ga mun gira da'ya, a hankali ya soma matsowa da fuskarsa daidai nawa nayi saurin matsawa baya, kara matsowa yayi idanunsa kyam a kaina naji ya furta "seat belt"

STAI LEGGENDO
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
Storie d'amoreHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...