Hibba
Kofar lift din na buduwa muka shiga tare ina biye dashi a baya, ya juyo ya danna button zuwa sama, gabadya jikina a mace yake, tunani kala kala na mun yawo aka, ji nake kamar a mafarki waenan abubuwan dake faruwa, tun daga dauko hanyata daga Maiduguri zuwa Lagos har yau, ban ta'ba tunani ko a mafarki irin wanan abun zai samemu ba nida Ammar.
Ina cikin wanan tunanin, naji hannaye sun zagayeni hade da janyo ni ya ha'de ni da kirjinsa, dumin jikinsa na ratsa ko wani ilahirin jikina, ajiyar zuciya na sauke na da'go a hankali ina dubansa shima ya zube mun kyawawan idanunsa yana kallona, cikin kwayar idanunsa ina iya hango zallar damuwarsa akaina, a hankali naji ya furta "kin gaji ko?"
Gyada masa kai kawai nayi, gabadaya a gajiya nake, zuciyata, kwakwalwata dama gangar jikina gabayaa. I feel mentally exhausted.
Ammar yaron kirki ne baiyi deserving waenan abubuwan da suke faruwa dashi ba, yanada rikon gaskiya bai ta'ba sa kanshi cikin wani aikin ha'inci ko na haram ba. Shiyasa tun ranar dana ji kiransa ha'de da sakon da aka turo mun cikin waya na nemi kwanciyar hankalina na rasa, duniyar ta tsaya mun cak!, har yau ban sake samun nutsuwa cikin zuciyata ba, Ammar ne kadai wanda nake mutuwan so har cikin raina tun bayan mutuwar iyayen mu, shiyasa bazan ta'ba barin shi cikin wanan halin ba, sai dai a kashe mu tare.
Ina cikin wanan tunanin Lift din yaja ya tsaya muka fito, wanan floor decoration din kusan iri da'ya ne da inda muka baro, Hassan yana gaba ina biye dashi a baya naga yaja ya tsaya a bakin wata kofa ya ciro wata kati yayi swiping a jikin kofar, nan take kofar ta budu muka karasa ciki, muna shiga na soma bin ko ina da kallo, babban parlour ne duk wani abu na more rayuwar dan' Adam akwaisa cikin parlourn, harta kujeru, makeken tv jikin bango, tiless dake shimfide ta ko ina, wutan lantarki komai yaji, wani da'ki na hango ta daga can gefe da kofa a bude, daga inda nake tsaye ina iya hango tsaruwansa, na soma tunanin inda zan kwana don naga da'ki daya ne bayan parlourn
"Hassan..?" Na kira sunansa a hankali
"Hmm.." naji saukan muryarsa a kunnena, cikin sauri na waiga naganshi dab dani, banyi tunanin har ya karaso inda nake ba, kallona yakeyi da wani irin expression idanunsa kyam akaina.
Kokarin kawowa kaina nutsuwa nayi nace "uhmm....akwai inda zaka kaini na kwana ne?"
Murmushi ya sakar mun wanda ya kara kawaita fuskarsa,
"No.. you're staying here with me" ya bani ansa yana kallon cikin kwayar idanuna.
"ban gane ba, kana nufin daki da'ya zamu kwana?" Na tambayeshi ina zaro ido
Daga mun gira da'ya yayi yana kallona, murmushi bayane a kyakywar fuskarsa, hankalina ya tashi ganin da gaske yake yasa na soma fa'din "nidai gaskiya bazamu kwana daki da'ya ba, ko a contract din babu inda aka rubuta zamu dinga kwana a shimfida da'ya".
Dariya ya sake yana girgiza kai, sai da yayi mai isarsa tukuna yasa hannu a habba'ta ya dago fuskata yana kallon cikin kwayar idanuna "you're tired Hibba, ki samu ki huta, I'll be in the parlour"
Sai a lokacin hankalina ya kwanta na juya zan tafi naji ya rikeni gam yaki sakina, cikin sauri na da'go ina dubansa ya sakar mun murmushi ha'de da tallafo gefen fuskata da lalausar hannunsa yana shafawa a hankali ya matso da fuskarsa dab da nawa har muna shakar numfashin juna, bai tsaya bata lokaci ba ya ha'de bakin mu wuri da'ya yana kai mun soft kiss a baki wanda yasa kafafuna suka ka'ge, gabadaya jikina yayi weak, ina jin yanda kirjina ke bugawa da matsanancin karfin gaske, a hankali yaja baya yana ajiyar numfashi yana kallon cikin kwayar idanuna, munfi two mins tsaye a hakan naji yace "go and rest"
Jiki a sanyaye na sungumi yar'jakata shi kuwa ya karasa wajen fridge ya bude ya ciro bottle water mai sanyi ya soma sha, a hankali na karasa cikin dakin ina bin ko ina da kallo, wajen gadon na nufa na ajiye jakata na zauna nayi shiru ina nazari sai faman ajiyar zuciya nake, nafi 10 mins a hakan daga bisani na janyo jakata na bude na soma ciro brush da kayan da zan canza, ina gamawa na mike na shige bayin, ko ina fess, wani irin kamshi ne na musman ke tashi na karasa wajen tangamemen madubi dake manne jikin bango na tsaya ina karewa kaina kallo, duk na galabaita, fuskata duk ta ko'kode da busheshen hawaye, ajiyar zuciya na sauke na soma cire kayan jikina na ajiyesu a gefe daga bisnai na karasa wajen bathtub na kuna na shiga na soma wanka, wankan 10 mins nayi sai dana dirje jikina tass tukuna na fito na wanke bakina na dauro alwala, farar towel da akayi wrapping a gefe na dauko na bude na soma goge jikina dashi na fito daga bayin na karasa inda na ajiye kayana na dauko mai da turare na fara shafe jikina tukuna na sanya kaya na zira hijab, na hau kan sallaya na tada sallah, magrib da isha na gabatar na jima cikin sojood ina kaiwa Allah kukana, ina idarwa na mike na duba lokaci naga sha da'yan dare har ya kusa, na mike na dauko remote na rage sanyin ac dakin tunanina ya karkata ga Hassan a hankali na karasa wajen kofar, na bude na leka, na hangoshi yana kan sallaya sanye cikin jalabiya yana salollinsa hankalinsa kwance, shiru nayi ina dubansa na yan mintuna daga bisani na tura kofar nasa key na dawo cikin dakin nabi lafiyan gadon, na lulube kaina da tausashen bargon, kamar auduga, ajiyar zuciya na sauke abubuwan da suka faru yau suna mun yawo a kwakwalwa, ina tunanin maganganun Ammar inda yake cewa zai samu yayi settling komai kafun na tafi, ban san me yake nufi da hakan ba amma ina fatan koma meye Allah yasa ya samu ya warware cikin sauki. Da wanan tunanin na samu wani wahalalen bacci ya yayi awon gaba dani.

YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...