Hibba
Tun a restaurant na soma gyan gyadi, da kyar Hassan ya kamo hannuna muka fito, gabadaya a gajiya nake, a hanyar mu ta dawowa har baccci ya tafi dani, bansan sanda muka iso ba, naji ya dauke ni cak ya fito dani daga cikin motar muka karasa zuwa sama, akan gado ya ajiyeni, naji saukan lips dinsa bisa saman goshina yana kai mun kiss kamar yanda ya zame masa sabo, a hankali ya janyo bargo ya kara lulubeni dashi, ya dauko remote ya da'an kara gudun ac dakin sa'anan ya shafi fuskata ya juya ya tafi, ban sake sanin inda kaina yake ba sai washe gari dana farka, babu alamun Hassan da kyar na mike ina sallati na fa'da bayi na wanke fuskata na fito na zauna gefen gado, "Hassan...." na kira sunansa can kasan raina abubuwan da suka faru jiya suka soma dawo mun, na rungume hannuna bisa kirjina inajin feelings na taso mun tare da matsanancin sonsa, Yanda ya dinga yi dani yana riritani jiya tamkar zai maidani cikinsa, nafi 10 mins zaune a hakan tunani kala kala namun yawo aka.
Yanzu dai gabadaya yanayin da Hassan yake treating dina ya sauya sosai. Ya soma sawa ina sakewa dashi, wanan firgicin da nake yawan ji a game dashi ya ragu sosai. Sai dai I'm still confused about him, sam bana iya sanin meke tafe dashi cikin zuciyarsa, I can't predict him.
Whereas ni kallo da'ya zai iya mun ya gano meke tattare dani, I so much want to know what he's feeling, his intentions towards me amma har yanzu na kasa fahimtar inda ya dosa, ajiyar zuciya na sauke na mike daga zaune da nake, na fito parlour nayi dialling landline nayi order breakfast sa'anan na dawo daki na soma dan' gyara gyaren inda na kwanta kafun a kawo mun abun kari. Ina gamawa na fada bayi nayi wanka na fito na shirya cikin daya daga cikin kayakin da Hassan ya siyo mun na sanya na zauna gefen gado ina zaman jira, kararawar parlor ne da yayi ringing yasa na mike na fito cikin sauri nazo na bude kofa naga breakfast dina ne aka kawo mun, ba tare da ba'ta lokaci ba na karba nayi ma wanda ya kawo mun godiya na juya na karaso ciki nazo na kalmashe kafa, shayi ne mai kauri, da dankalin turawa da ketchup da kuma soyayyen kwai, da four sliced bread a gefe. Sai dana cinye tass tukuna na mike na dauki kwanukan na kai kitchen sink na daureye, na kawo parlour na ajiye musu, idan sunzo sua dauka.
Ina cikin haka na sake jin kararawar parlourn ya ka'da, a tunanina Hassan ne na karsa jiki na ba'ri, ina budewa maimakon naga Hassan, naga Habib tsaye yana ganina cike da girmamawa ya soma gaisheni, ni yanda yake gaisheni yana kirana Hajiya naji gabadaya abun yayi mun nauyi, don a shekaru ya girmeni sosai zaiyi kanwa dani, nace ya dinga kirana Hibba kawai babu wani Hajiya, murmushi kawai yayi yace "toh Hajiya...yau ina kikeso a kaiki? Kodai asibiti zamu fara zuwa?"
Ba'ta fuska nayi ganin bai daina kirana da Hajiyan ba amma ban sake cewa komai ba nace"eh kaini asibiti kawai" juyawa nayi na koma ciki don na dauki abunda zan bukata, gabadaya tunanina nakan Hassan, ina ya shiga da safiyan nan? kodai business ne ya rikeshi? Zan sake ganinshi kuwa yau or he's going to disappear again for some days. Da wanan tunanin a raina muka karasa muka fito lobby din hotel tare da Habib, har mun iso daidai inda akayi parking motar, Habib ya bu'de zai shiga naji murya a gefena yana fadin "I'll take over from here Habib"
Cikin sauri na waiga na ganshi tsaye muna ha'da ido ya sakar mun tsadadiyar murmushin nan nasa dake sa numfashina tsarkuwa, kirjina ya shiga harbawa da karfin gaske, he looks so handsome sanye neatly cikin white shirt da tie da bakin wando "good morning sweetheart, kin tashi lafiya? Sorry ina sauri da safen nan I left early, na manta na sanar dake i'll be your driver for today" ya fada yana Shafar gefen fuskata, ya karsa a tsanake wajen driver inda Habib yake tsaye, Cike da girmamawa Habib ya mika masa makulin motar "Sai ka dawo oga" ya dawo da dubansa gareni yana murmushi yace "and you too Hajiya" sa'anan ya juya ya koma ciki. Yanayin da Habib yake treating dina is quite different, sam bashida matsala, he makes me feel at ease ba kamar sauran bodyguards din ba.
Hassan ne ya juyo yana dubana yamun alamu dana shigo motar, ban musanta ba nasa hannu na bude murfin motar na shiga na zauna na jawo seat belt ina kokarin sakalawa, ya tada motar muka bar harbar hotel din. Shiru ne ya ziyarce mu, kowa da tunanin da yake masa yawo aka, it was a comfortable silence tho, bansan me yake tunani ba don a koda yaushe he's always deep in his own thoughts baka taba sanin abunda yake tafe cikin zuciyarsa, ni kuwa tunanina baya wuce da'ya cikin biyu, it's either ina tunaninsa ko ina tunanin Ammar.
Da wanan muka karasa asibitin, muna isa Hassan yayi excusing kansa yace yanada urgent call, don tuntuni wayarsa taketa faman ringing, nace dashi babu matsla zan haura naje na sami Ammar. Gyada mun kai kawai yayi, na haura sama na barshi don yayi answering call dinsa, ina tunanin irin yanayin aikinsa, sam baya samun hutu. Ina shiga ciki na soma haurawa step hankalina ya karkata zuwa ga Ammar, ina tunanin yanayin jikinsa yanzu, yaushe za'a sallameshi? Yanzu idan aka sallameshi what next? Zan zauna anan na cigaba da kasancewa tare dashi ne ko kuwa zamu koma gida? Sai dai nasan abu mai kamar wuya ne su iya barin Ammar ya tafi a wanan halin da ake ciki, tunani ya karkata zuwa ga Hassan, toh shifa? Zai cigaba da zama anan Abuja ko kuwa zai ce mu koma Lagos? Ni sam bana so nayi nisa da kanina.
Da wanan tunanin na idasa haurawa sama zuwa floor din da Ammar yake, as usual nurses da doctors sai faman kai kawo suke a wajen, har na karasa wajen kofar dakin Ammar juyawan da zanyi na hango yarinyar dana hadu da jiya zaune a waiting area da bodyguard dinta tsaye a gefe, mutsuke idanuna nayi don na tabbatar itace na gani confirm ita dince a zaune sanye cikin atamfa riga da skirt, ta daura dan'kwali sai gyalen data yafa a saman kafada, kamar ance ta juyo tana waigowa muka ha'da ido, tayi saurin zaro ido daga bisani naga ta sakar mun lalausar murmushi hade da da'ga mun hannu, nima da'ga mata hannu nayi, har zan juya na shige ciki naga ta mike cikin sauri ta yiwa bodyguard dinta magana, ta karaso inda nake tsaye, muryarta a sanyaye tace " sannu sister Hibba...barka da Safiya" ta fa'da mun cikin harshen turanci.
"Yauwa barka Hafsah, ya karfin jiki?"
"Da sauki Alhamdulillah... daman nace bari na karaso na miki godiya na jiya"
"A'a babu komai... da fatan kinji sauki sosai yanzu?"
Gyada mun kai tayi, ni kuwa na baza ido naga ko Lukman zai bu'llo amma banga alamunsa ba.
"Kema anan kike da zama?" Naji ta watso mun tambayar. Shiru nayi ina tunanin ansar da zan bata, sai kawai na tsinci kaina da bata ansar eh. Naga murmushi ya bayana a kyakyawar fuskarta
"Idan bazaki damu ba, zan iya samun number wayarki mu dinga gaisawa?"
Gabana ne ya yanke ya fadi jin abunda tambayeni, daga ganin alamu so take ta kula abota dani amma nikam zan iya da wanan halin da nake ciki? me Hassan zai ce idan ya samu labarin na bawa wata bakuwa numbata, bakuwar ma yarinyar friendenemy dinsa tunda naga ba shiri sosai yake da Lukman ba, tunani kala kala ne suka shiga mun yawo aka, sai dai yanda yarinyar take bina da kallo cike da hope a kwayar idanunta yasa naji bazan iya ce mata a'a ba, na ciro wayata na soma kira mata number, nan da nan ta karba tayi saving hade da mun godiya ta juya ta tafi, ni kuwa na tsaya nayi shiru ina tunanin abun yi, a hankali na juya na karasa cikin dakin Ammar jiki a sanyaye.

BẠN ĐANG ĐỌC
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
Lãng mạnHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...