Chapter 107

1.1K 57 0
                                    


Suna cikin mota yana driving zasu koma gida, Faheema sai faman hawaye take tana fadin kar ya sake kawota wanan wajen bata so, idan sun koma gida sai ta gayawa daddynta cewa ya kawota wajen wanan matar, hakuri da rarashi ya shiga bata yace anyi na karshe bazai kuma kawota ba.

Har ya shawo kan kwana da zai sada shi da express from nowhere yaga motocci guda biyu sunzo sun sha mishi gaba, cikin sauri ya taka birki hankalinsa a tashe ya soma kokarin lekawa yaga kosu waye, wasu maza kattai guda shida yaga sun fito da bindigogi a hannunsu suka karaso inda yake, kara Faheema ta sake ganin bindigar dake rike a hannunsu, Sadik yayi saurin kamota kirjinsa na bugun tara tara, "if you move i'll bury this bullet in your head!" Daya daga cikinsu ya karaso yana nunawa Sadik, cikin sauri daya daga cikinsu ya zagayo ya bude murfin mota yana kokarin ya dauke Faheema, Ihu Faheema tasa Sadik na ganin haka bai damu da bindigar da aka nuna masa ba ya soma kokarin janyo Faheema, ai kuwa na gaban bai tsaya ba'ta lokaci ba ya buga masa gefen bindigar da iyakacin karfinsa, wani irin kara Sadik ya sake ya fa'di a wajen bai kara motsawa ba, cikin zafin nama suka dauke Faheema suka toshe mata baki sai cikin mota suka tafi suka bar Sadik a wajen.

Hassan yana office har kusan magrib baiji kiran Sadik ba, ya kira gida yana tambayar Hibba kosun karaso gida, tace bata gansu ba, hankalinsa ya tashi don last wayar da yayi dashi ya shaida masa gasu nan sun baro asibitin suna kan hanyar dawowa gida, sai kiran layin yake ba'a dagawa, ya kira Hajiya yana tambayarta ko sun karaso nan gida Hajiya tace bata gansu ba, hankalin Hassan yakai kololuwar tashi, ba jima ba sai ga kira nan ya shigo wayarsa ta layin Sadik cikin sauri ya da'ga ya kara kunne, wani bakon murya yaji ana tambayarsa ko yasan me wayar yace eh ya sani ina shi me wayar yake, aka ce dashi gashi nan dai kwance a gefen hanya rai a hannun Allah, it seems like he had an accident, zuciyar Hassan ta tsaya cak ta daina bugawa na huccin gadi daga bisani tazo ta cigaba da bugawa "what?!!!" Ya furta a razane

"Where is he now?!!!"

Aka ce dashi gashi gashi suna kan dai dai titin da zai sadasu da Magodo, a kidime Hassan yace musu gashi nan zuwa, zuciyarsa kamar zata harba kirjinsa ta fito, duk yabi ya rude, a 360 ya baro office ya kira Ndagi ya sanar dashi abunda yake faruwa akan su tattaro men suzo su taddashi, yana isa wurin yaga dan'uwansa kwance rai a hannun Allah, ya fara ware ido baiga Faheema ba, hankalinsa a mugun mugun tashe yasa Sadik a mota sai asibiti at the same time yana kokarin kiran mahaifiyar Afrah.

***************************
Bangaren Afrah kuwa tana faken idanun uwarta ta samu tayi escaping daga asibitin, daman ta rigada ta tsara komai tayi executing plan dinta perfectly ba tare da kowa ya sani ba, tana barin harabar asibitin ta soma kiran gang leader din akan suna ina, yace mata gasu nan sun samu sun kwace Yarinyar tana hannunsu, tace good su ha'du a airport, "sai dai hajiya wanda yake rike da yarinyar yayi mana gaddama fa, mun dauke masa wuta"

"What? Me nace muku?!! Bana ce karku ta'ba lafiyan kowa ba, yarinyata kawai nace ku karbo mun"

"Toh wlh mun kawar dashi, yana kokarin ya ba'ta mana aikin mu"

"Shit!!" Ta fada tana cizon yatsa hankalinta a tashe "amma dai ba harbinsa kukayi ba ko?"

"A'a kawai mun dan kwantar dashi ne, zai farfado"

Tace okay ku bani nan da 15 minutes gani nan karasowa ku jirani"

Yace toh sai ta taho, a gurguje ta soma karasawa aiport din, Hajiya Rabi na zaune shuru shuru bataga yar'ta ba, mikewa tayi ta soma kwankwasa kofar bayin tana kiran sunanta amma bata ji an ansata ba, hannu tasa ta murde handle kofar ta tura ta leka taga wayam, hankalinta ya soma tashi "Afrah!! Afrah!!!!"

Cikin sauri ta fito daya dakin tana leka leke ko zata ganta amma ko mai kama da ita bata hango ba, a guje ta karasa wajen nurses tana tambayarsu suka ce basu ganta ba, nan akayi raising alarm cewa baga Afrah ba hankalin kowa ya tashi. Ana cikin wanan commotion din wayarta ta fara ringing ta dauko taga Hassan ne ke kiranta ta kara kunne, tsawa ya daka mata yana tambayarta ina yar'shi

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now