The End

2.6K 122 18
                                        

Hibba

Ammar sati biyu ya kara a lagos kafun ya wuce Singapore, wata rana ana zaune kwatsam Hafsah ta kirani da kyakywan albishir ta shaida mun zasu Ilorin ita da Lukman, zaije yaga yan'uwanta ya nemi aurenta, nayi murna sosai na nuna farin cikina, na jima ina sata a addu'a gashi Allah ya anshi addu'armu, nayi mata nasiha sosai na fadakar da ita akan su samu suyi istibrai' kafun ayi aure tace insha Allah zatayi, tayi mun godiya sosai mun jima munata hira da ita, da Hassan ya dawo tsabar farin ciki ban ma bari ya zauna ba na soma shaida masa abunda Hafsah ta sanar dani, murmushi yayi yace ai it's high time ace ya aureta, watan mu biyu da dawowa daga Maiduguri muka fara shirye shiryen tafiya Misra wajen mahaifiyarsa, kafun tafiyar mu I was so nervous ya dinga kwantar mun da hankali, muna isa Cairo first time dina na barin kasar kenan tun daga airport tazo ta tarbemu, surprisingly naga har yanzu da kuruciyarta bazaka ce itace mahaifiyarsa ba, da gani tana kula da kanta sosai, don kama kam suna kama da Hassan don ita ya biyo, ta karbemu hannu bibiyu ta dauki Faheema da Faheam ta rungumesu, tace rabonta da Faheema tun tana karama, da Hassan yayi introducing dina gareta kamar zata maidani ciki, tanata murna, matslar dai babu Hausa don da turanci muke communicating, harta Hassan ma da turanci suke magana da ita, satin mu da'ya a Misra muka wuce U.S wajensu Anty Zaliha, yaran sukayi murna sosai ganinmu, barin ma Faheema, sai da muka kara two weeks a U.S tukuna muka dawo Nigeria. Faheam yana cika shekara biyu da wata hudu muka sashi a makaranta, yanzu maganarsa yana fitowa zaizai babu wanda baya yiwa hira, makaranta daya aka sashi da yayarsa a lokacin ita tana J.s.s 1, idan ka ganta bazaka ce tana secondary school ba don tayi kankanta sosai sai dai akwai kokari, Faheema is extremely smart and intelligent for her age, aka rayuwa ta cigaba da gudana. Lokacin da aka sa ranar bikin Hafsah da Lukman har ilorin mukaje muka sha biki, Hafsah tayi kyau sosai kamar ba ita ba, Abuja muka kaita ta suka cigaba da rayuwarsu gwanin ban sha'awa da sahibinta Lukman.

***********************************

5 years later

A kwana a tashi babu wuya wajen Allah, rayuwa nata tafiya, ina zaune hankali kwance tare da mijina da yarana, tunda na haifi Farhan har yanzu shiru ban kuma samun wani cikin ba, gashi yaran namu duk sun girma sunyi wayo sosai, yanzu haka Faheema tana neman shekarata goma sha biyar kenan tana S.S.S 2, tana gama J.S.S dinta mahaifinta ya mayar da ita boarding na Queens college dake Yaba, da yayi niyan ya nema mata makaranta a U.S sai muka canza shawara akan a bari ta gama anan in yaso jami'a sai taje tayi acan, yanzu sai hutu zuwa hutu take zuwa gida, Faheam yanzu shekararsa bakwai zai shiga na takwas yana primary 5, Farhan kuma shekararsa biyar yana primary 2, dayake yanada tsawon kafa idan ka ganshi tare da yayansa sai ka aza tagwayene domin kansu da'ya, komai tare sukeyi, dakin kwanansu da'ya tare suke zuwa school su dawo, Hafsah an samu karuwa ta haifi danta namiji kyakywa dashi yanzu haka ma tana dauke da ciki na biyu, from time to time muke kawowa juna ziyara, Ammar tunda ya gama karatunsa na degreee ya tsaya ya kara da M.Sc yanzu haka ya kusan kammalawa at anytime zai gama ya dawo. Na yiwa Hassan magana akan karatuna ina so na koma makaranta bai musanta ba ya tambayeni course da nakeso nace masa ni any course related to education inaso, dariya yayi yace iya course din da nakeso kenan nace mishi eh daman tun ina karama burina bai wuce koyarwa ba na zama mallamar makaranta, yaji dadi sosai yace na fara karatun tukuna, haka yasa aka samo mun admission a wani private university na fara zuwa ina karatuna hankali kwance, ana cikin haka zancen auren Sadik da Nuratu ya taso wace ta gama makaranta har tana service dinta, soyayya ce mai kar'ko suka kulla tsakaninsu, yanzu haka Sadik ya gina kansa da kyau har yana neman ya kamo kafar yayinsa, ya gina dankareren gida anan cikin Island, yanzu haka he's one of the youngest billionaire in that area, sai dai wani ikon Allah Nuratu tayi sa'a baya kulla wasu matan, tunda ya tsaya akanta shikenan, ita kadai take samun attention dinsa, ga miskilanci, duk miskilancin da Hassan yakeda ina fama dashi bai kai na Sadik ba don ya ninka shi, daman Hajiya na yawan gaya mata sai ta kara da hakuri, kuma a hakan take bala'in sonsa ji take duk duniya babu wanda ya kaita sa'ar samun namiji kamarsa, rai da rai yana kan hanyar zuwa da'yan gidan mahaifinsa, dayake Rahama ta jima da tarewa a gidan nata, sai dai tunda tayi ba'ri sau da'ya har yanzu shiru bata kuma samun wani cikin ba, yanzu haka shirye shiryen bikin muketa faman yi, saura wata biyu a daura.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now