Chapter 89

1.5K 87 19
                                    

Hassan

Zaune suke a penthouse din Jammal dashi da Sadik sunata faman tattaunawa, Alhaji ya dawo yana gari yazo da amaryarsa, daman tunda Jamal ya kirashi a waya ya shaida masa Alhaji yana son ganinsu ya nemi nutsuwarsa ya rasa, abunda yafi da'ga musu hankali shine har gida ya kawo amaryar inda hajiya Bahijja uwargidan Mahaifinsu take yace nan zata zauna for the time being kafun a gama yiwa amarya gyaran sabon gidanta, basu so hakan ba saidai babu yanda suka iya saboda sunsan halin mahaifin nasu sarai idan ya kafe akan abu sai yayi, babu wanda suka fi tausayawa illa Hajiya Bahijha, matar tana ganin abubuwa iri iri a wajen mahaifinsu sai dai duk tana shanyewa tana danne zuciyarta, sam ba'ta ta'ba nuna masa baccin ranta ko ta nuna damuwarta akan abubuwan da yakeyi, ko da aka kawo amaryar gidan hannu bibiyu ta tarbesu da yan'uwan nata bata nuna musu komai ba, suma suka ji dadin irin tarbar data musu, suka damka mata yar'uwar tasu amana sa'anan suka juya suka tafi.

Bayan an dire masa amarya, Alhaji ya kira yaran nasa duka maza biyar hardasu yaran Hajiya wanda ta haifa Ya' Bashar da Ya' Aliyu yayi assembling dinsu, Hamdan ne kadai da yake Europe bai samu zuwa ba, nan ya zaunar dasu ya soma  introducing dinsu ga sabuwar matar nasa, suna sauraronsa Babu wanda ya masa gadama a cikinsu don tun kafun suje su ganshi hajiya ta ja musu kunne tace bata son ko wanne a cikinsu ya ja dashi, kamar yanda suke bata daraja suna mutuntata hake takeso itama sabuwar matar su ba'ta wanan respect din, Sadik kamar zai hadiye rai ya mutu don bakin ciki, tunda ya daura idanunsa akan yarinyar da Alhaji ya auro yaji sam bata mishi ba daman tun  kafun a aurota yaji ya tsaneta, yarinya ce sosai sai dai akwai kyau, doguwa ce fara tana da dan' diri sunanta Rahma, tare da kanwarta wace take binta suka zo sunanta Nuratu, kamarsu da'ya har kace tagwaye komai nasu iri da'ya harta tsawon, sai dai Rahma ta fita cika ido, ta biyota zata zauna tare da ita ta cigaba da karatunta anan, Alhaji zai dau nauyi, Nuratu tunda ta dora idanunta kan Sadik taketa faman binsa da kallo, har satan kallonsa takeyi ko don yanayinsa ne yake ba'ta mamaki oho, ta kafeshi da dara daran idanunta yana lura sarai da yanda take binsa da kallo duk yabi ya tsargu suna ha'da ido sai ya sakar mata harara, yarinyar tasha jinin jikinta, jikinta yayi sanyi, daman tasan ba lallai bane ayi accepting dinsu ita da yayarta ba a gidan.

Tunda Alhaji ya fara magana suna sauraronsa uffan basu ce har ya gama, yace he doesn't want any form of disrespect from any of them, she's his wife and that's final, kowa ya kama kanshi musamman Sadik yace idan yaji an samu wani matsla daga wajensa zai sa'saba masa don he's aware of komai da Sadik yake nasan hanashi auren har zuwansa Jalingo da yayi yace he should behave himself. Yana gamawa ya sallamesu, yace kowa ya kama gabansa, haka suka mimike jiki a sanyaye suka tafi. Ya'Bashar ma daga nan yayi sallama dasu ya wuce airport, Aliyu kuma yana nan sai washe gari zai koma Abuja.

Su Hassan gidan Jammal suka wuce don su wuce takaici, shine suke nan har yanzu sunata faman tattaunawa yanda zasuyi su kwato wa Hajiya yan'ci akan wanan cin fuskar da mahaifin nasu yake mata, Sadik ya hakikance yace dole sai yasan yanda za'ayi yarinyar nan ta bar gidan bazasu zauna ba, dole ta koma inda ta fito, Hassan ya dakatar dashi yace "a'a ba haka za'ayi ba, tunda Alhaji ya rigada yayi wanan auren hakuri kawai zamuyi, babu abunda muka isa muyi akai"

Yace suyi yanda Hajiya tace kuma yanda yake gani yarinyar kamar tanada nutsuwa bazata kawo wani matsala ba.

"Haka kuke gani ai don baku zaku zauna da ita ba, nida Hajiya ne zamuyi facing duk wani wulakanci da challenges da zasu afku nan gaba, da zaran ta kwana biyu zata soma sheka ayarta ta bandare, tunda sun samu wuri. Matslan auro yan kauye kenan, ni inta mun I won't waste time maketa zanyi musamman wanan kanwartata mai idanun kyanwan nan sai shegen kallon tsiya kamar mayya"

Dariya suka sake "kadai bi a hankali Sadik ka rage wanan zafin ran naka, wace mace ce zata zauna dakai a hakan da wanan zafin rai haka? Haba ka dinga sassautawa mana"

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant