Chapter 10

1.8K 96 5
                                        

Hassan

A hankali Hassan ke bin Hibba da kallo har ta idasa haurawa sama, yana jin wani irin feelings akanta na ratsa ko wani ilahirin jikinsa, a ko wani second kara kwadaituwa da ita yakeyi, gabadaya yanayin jikinsa ya canza, ya sallam ya fa'da yana dafe kai, he just couldn't help himself when it comes to her, wani irin zallan sha'awarta yakeji yana tsargar masa, kyakyawar fuskarta na masa a kwakwalwa, ya jawo coffee dinsa ya cigaba da kurba tunani kala kala na masa yawo aka, murmushi ne ya bayana akan fuskarsa daya tuno wayar da sukayi da AK, ya girgiza kai "Ak is just crazy ".
Ya tabbata Hibba tayi misunderstanding situation din tana tunanin AK na azabtar da yaron, whereas he's just playing with him, shi haka yake koda men dinsa ne, wani irin bahagon mutum ne. Duk tabi ta rike ce a wayar.. sai kuma ya tuno yanda take zubda hawaye a lokacin nan take yaji zuciyarsa ta masa wani irin nauyi, sam baisan yaga kukanta, ya rasa gane meyasa yake jin irin waenan feelings din akanta, it's so unlike him.

Kokarin kawar da tunanin Hiba yayi daga ransa ya dauko waya ya soma dialing gida, bayan yan sekoni yaji Madam Laide ta da'ga yace ta bawa yar'sa wayar, can bayan yan' mintuna yaji muryar Faheema a kunnensa

"Hello Daddy..."

"Hello sweetheart" ya fa'da a hankali yana murmushi

"Daddy ka ganta?" Ka ganta, Daddy?" Ta soma jero masa tambayoyi kamar tana jira

Dariya ya sake yace "yes na ganta".

Murna ne yaji ya cikata "Toh yaushe zata zo Daddy...tayi mun alkawari zamu ci dinner tare, ina jiranta tazo....we're going to have so much fun together"

Girgiza kansa yayi, Faheem is just too cute

"Zan kawo miki ita sweetheart amma ba yau ba... she's busy"

Yasan bazai iya kawo Hibba ainin gidansa ba, yarinyar tana bukatan nutsuwa da hutu, she's still confused gwanda ya barta tayi sorting out feelings dinta da abunda ya kamata tayi. Kafun haduwarsa da Hibba, his plan was to recover the 100mill da Ammar ya batar masa, amma tunda ya ganta yaji komai ya kwance masa, he's so attracted to her kuma yana jin bazai iya hakura ba har sai ya sameta shiyasa yayi mata offern wanan contract din, a yanzu haka he doesn't care about the 100mill, kai 100mil is nothing to him, a da're daya yasan zai iya making fiye ga haka, matsala da'ya anan shine yanda duk yabi ya damu akan yarinyar da son kare lafiyarta.

Ganin yanda Lukman, da wasu mutane suke bibiyanta yasa yaji gabadaya he's tensed, yarinyar ma bata ma san suna biye da ita ba, she's so naive, daba din ya biyo bayanta da yaman nan ba, ko Lukman ko waenan mutanen da sun capketa sun tafi da ita, zasu iya forcing Ammar ya fito duk inda yake su tattara su biyu su kashe, kuma babu wanda ya isa yayi wani abu akai, tunda haka duniyarsu take operating, shiyasa yana ganin haka he had no choice but to brand her as his, da zaran sunsan Hibban tana tare dashi, zasu ja baya, baza suyi gangancin tukarnta ba don suna mugun shakkansa,

Muryar Faheema ce ta fargar dashi inda take fadin "Daddy please try and bring her as soon as possible, I can't wait to se her" ta karasa maganar tana sakar masa yar karamar dariyarta.

Shima dariyar ya sake yana mamakin yanda yar'sa ta damu sosai akan kasancewa da Hibba, ko dayake ba abun mamaki bane tunda yarinyar tanada shiga rai, shi kanshi kallo da'ya ya mata ya gigice yaji ta tafi da imaninsa, a hankali ya murmusa yace "Faheema?"

"Na'am daddy" ta bashi ansa

"Are you in bed?"

"Yes daddy"

"Okay good....Daddy bazai samu dawowa gida ba for a couple of days. I have business okay?"

"Oh" yaji ta furta kamar bata so hakan ba

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now