Hibba
Gabadaya a gajiye nake, jikina kamar an mun duka nakeji, kwana biyun nan bana samun isshen bacci ina nan ina famn jinyar kanina, yau kwana uku kenan ban sanya Hassan ko AK a idanu ba, nasan maybe aiki ne yasha musu gaba but I couldn't help getting a bit worried, na tsinci kaina dajin kewan Hassan dason kwadayin sake ganinsa, zuciyata ta shiga tunani iri iri..ina ya shiga? ya ba'ta shiru? Yana ma tunanina kuwa? na shiga tambayar kaina ina kwance na kifa kaina a gefen gadon Ammar wanda ya samu bacci sosai tun safe yaketa faman baccin, naji dadi sosai at least ya rage complain din ciwon jikin yanzu, a hankali bacci ya soma awon gaba dani.
Bazan iya cewa ga iya adadin dana dauka ina bacci ba amma cikin baccin na soma jin kamshin dadden turare ya cika hancina, ha'de da saukan soft lips yana sumbatar goshina, cikin sauri na farka na ganshi a gefena fuskarsa dab da nawa yana aika mun da tsadadiyar murmushinsa dake ba'lain kara masa kyau, kamar a mafarki nake ganinsa.
"Hello sunshine" naji ya furta yana kallona.
Sai a lokacin na dawo hayacina na tuna ba mafarki nake ba, Hassan ne tsaye a gabana live. Wani irin farin ciki naji ya ratsani hade da jin sanyi a raina. Amma ban nunan masa hakan ba na da'an turo baki ina kallonsa kasa kasa.
"What is it sweetheart? Miss me?" Ya tambayeni still yana murmushi.
Ban ce dashi kala ba naga ya janyo kujera dake gefe ya zauna yana facing dina ya kamo small hands dina cikin lalausar nasa mai kamar auduga, a hankali ya shiga shafawa yana aika mun da wani irin kallo mai tsuma zuciya "I miss you" ya fa'da yana sakar mun kiss a wajen daga bisani ya tallafo fuskata yana kai mun kiss ta ko ina a fuska, idanuna, gefen kumatuna,har zuwa hancina. Wani irin yarr najia jikina gabadaya tsigar jikina suka mimike, nayi saurin rintse idanuna hade da d'an ja da baya ina duban inda Ammar ke kwance naga har yanzu baccinsa yakeyi.
Kallon Ammar shima Hassan yayi daga bisani yace "ya jikin nasa yanzu?"
"Da sauki alhamdulillah" na bashi ansa "Ciwon jikin da yakeji ya ragu sosai"
"Toh madallah haka akeso...I'm glad to see you're doing okay too, sai dai you look exhausted, ki shirya zuwa anjima zan turo driver yakai ki hotel ki canza, we're going out on a date tonight.
Cikin sauri na dubeshi nace "Ammar fa? Wai zai zauna dashi?"
"Don't worry about that, AK is coming to check on him, zai zauna dashi har muje mu dawo"
Shiru nayi inaso nace mishi a'a sai kuma nayi wani tunanin, nasan bazai yarda ba, everything is an order from him, he doesn't take no for an answer don haka na gyada mishi kai kawai.
Murmushi ya sakar mun yana kokarin mikewa, a maimakon ya sakar mun hannuna ya mike dani tare ya sake hade bakina da nashi ya shiga kissing dina cike da shauki kamar zai shige jikina, sai da yayi mai isarsa tukuna ya barni, gabadaya tunani ya kwance da kyar nake fidda numfashi.
"I'll see you later tonight " ya fa'da hade da karasawa wajen kofa, Kafun ya bude naji yace "Oh and ki duba kan table ga sabuwar waya nan na siyo miki da sim card a ciki, ki tabbatar yana tare dake at all times, expect messages from me" kafun nayi wata magana har ya fice ya barni tsaye jiki na kyarma, da kyar na karasa wajen table din na dauko ledar wayar, na bude na ciro kwalin ina kare mata kallo, IPhone ce sabuwa dal na soma tunanin tsadarta, meyasa zai siyo mun waya mai tsada irin wanan, ni tunda nake ban ta'ba rike waya mai tsada ba, daga ni sai yar Nokia dita banida number kowa sai na Ammar da kuma madam dinmu na wajen aiki a Maiduguri. Cigaba da kallon wayar nake cike da sha'awa na cirota daga cikin kwalin na kuna, ina rike da ita kamar kwai. Bayan ta kunnu na duduba naga numberashi ne kadai a ciki inda yayi saving da sunansa Hassan. Ajiyar zuciya na sauke na mayar da wayar na ajiye ina tunani iri iri.
Sai da Ammar ya farka tukuna na soma sanar dashi zuwan Hassan da kuma bukatarsa na komawata hotel na shirya zai fita dani, Ammar bai ce komai yace naje, na nunan mishi in har it's not okay with him zan zauna tare dashi, Ammar yaki kememe yace naje kawai. Na lura cikin yan kwakin nan akwai abunda ke damunsa cikin zuciya amma yaki ya fa'da mun, jiya ma nayi kokari ya sanar dani yace mun babu abunda ke damunsa he's okay, haka na hakura na kyaleshi. Muna cikin haka sai ga AK nan yayi sallama ya shigo, sanye yake cikin suit yana tafiyan nan nasa cike da kasaita, yana karasowa muka gaisa yana tambayar jikin Ammar, Ammar idanunshi biyu yace mishi da sauki alhamdulillah, godiya sosai Ammar ya shiga masa na ceto ransa da sukayi, AK yace bakomai, na lura AK yana son Ammar kuma yana nuna damuwarsa sosai akansa, ya mayar dashi tamkar wanda suka fito ciki da'ya sam baison yaga yana cikin damuwa, yanda naga yakeyi da sauran boys dinsa ba haka yakeyi da Ammar ba, yana dan sakar masa sosai, harda janshi da wasa, a raina nake fa'din jinisu ya hadu ne kam tunda har AK yake sakewa suyi hira harda zolaya, shima Ammar na lura duk ya soma sabawa da mutumin don harda dariyansa lokacin da yake zolayensa.
Mikewa nayi na soma dan' tatara kayana nace da Ammar zanje na dawo, zan shirya daga nan na debo wasu kayan, Ammar ya gyada mun kai yace sai na dawo, nace ya kula da kansa, yace insha Allah ya'ya Hibba, haka nayi sallama dasu na fice, Habib ne ya kawoni hotel din, zuwa lokacin yamma ya soma gabatowa ina isa apartment din na tadda babu kowa, na karasa cikin daki, ko ina fess kayana kamar yanda na tafi na barsu haka na samesu, komai neat, akan gadon na hango wata hadadiyar Abaya deep blue mai ratsin cream coloured stones da flowers, da kuma takalma high heels a gefen, a hankali na karasa na da'go takardan da aka dora akai ina karantawa "wear this sweetheart make sure you look pretty and expect me soon".
Wani irin abu ne naji ya tsargar mun ban san sanda na saki murmushi ba ina jujuya takardan a hannun daga bisani na dauko tsadadiyar abayar ina kare mata kallo, Hassan yana son ganina cikin Abaya, dukda waenda nake dasu sai daya sake karo mun wani, kuma daidai size dina. Ba tare da ba'ta lokaci ba na karasa cikin bayi nayi wanka na cu'de jikina da kyau, bayan na gama wanka na dauro alwala na fito na tadda sallar magrib, na iddar na cigaba da zama akan sallaya ina lazimi har sanda naga lokacin isha yayi na mike na gabbatar da sallar isha'i nayi addu'a sosai. Ina addu'a Allah ya dora ni bisan kan duk wani dake son gani bayanmu nida kanina, kuma ya daura mu kan bisa wanda muke tare da, ya cire duk wani fitina da bala'i da nufi na cutarwar daga ransu, ya bamu ikon cin wanan jarabawar da muke fuskanta cikin rayuwa ya hayyu ya qayyum.
Allah yasa mu dace, Ameen❤️
~Sona~

YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...