Hibba
A gaban wata hada'diya restaurant mukayi parking, ya jani muka karasa ciki, tun daga gate din shiga aketa mika mana gaisuwa har muka karasa.
Muna shiga ciki wata yarinyar ce yar'budurwa tazo ta tarbe mu, cikin harshen turanci ta soma gaishe da Hassan inda ya gyada mata kai, kalma da'ya kawai ya furta mata "Mufasa"
Nan take ta fahimci abunda yake nufi tace mu biyota ta kai mu wata hadadiyar staircase muka soma haurawa, komai cikin wurin tsaf gashi an zagaye da abubuwan gargajiya, wurin shiru babu hayaniya ko kadan. Gaban wata kofa ta kaimu taja ta tsaya cike da girmamawa ta mana nuni mu karasa ciki. Tare muka karasa ciki da Hassan yana gaba ina biye dashi a baya, muna isa na jiyo muryar wani mutum yana fa'din"Hassan... finally you made it, ai mun zata bazaka zo ba"
"Mmmhm.." kawai Hassan ya furta muka idasa karasawa sai a lokacin na hango mai maganar, Mufasa ne zaune yana ganin mu ya mike ya karaso cike da fara'a ya mikawa Hassan hannu suka soma gaisawa, ya dawo da dubansa gareni "kace tare da gimbiya kuka zo, well I'm glad you brought her" ya fada yana kare mun kallo da murmushi bisa gefen bakinsa.
Saurin hadiya nayi ina kallon waenda suke zaune can gefe idanuna suka sauka kan Lukman wanda yake kallon Hassan da wani irin expression a fuskarsa yana aika masa da wani irin kallo, a gefensa wani mutum ne da ban san dashi ba ya mike shima cike da fara'a ya karaso yana mikawa Hasaan hannu suka soma gaisawa "kwana dayawa Hassan... how have you been?"
"I'm good" Hassan ya bashi ansa
"Kazo mana da yarinya kenan". Ya fada yana kashe mun ido daya
Kafun Hassan ya bashi ansa naji muryar Luqman yana fadin "Hibba zo ki zauna kusa dani".
Tense Hassan yayi a gefena, ya juyo yana duban Lukman dake zaune idanunsa kyam akaina, wani irin kallo mai sa hantar cikin mutum kadawa Hassan ya watsa mishi mai tattare da warning. Mufasa ne ya da'an saki dariya yana fadin "zo Hibba ga special table nan, you can enjoy yourself there"
"She's not going anywhere, she's sitting with me" Hassan ya fa'da musu cikin kakausar murya, cikin sauri na da'go na dubeshi naga ya kara hada rai, ya kara matso ni kusa dashi.
Dariya Mufasa ya kuma sakewa, bai ja da Hassan ba muka karasa table din muka zauna, Hassan yana fuskantar lukman direct, ni kuma ina zaune a gefenshi, sai faman harar juna sukeyi shida Lukman daga gani babu jituwa sam a tsakaninsu kuma gashi abokanai ne. Hassan da Lukman kusan yanayinsu da'ya sai dai hasken da Hassan ya fishi kasancewar Lukman black handsome, they stood out among the four of them seated there, harta yanayin shigansu da suit din dake sanye jikinsu kusan iri da'ya ne, na tabbata duk inda suka shiga sai yan'mata sun juyo sun kallesu.
Muryar Mufasa ne ya fargar dani duniyar tunanin dana afka inda yake fadin "Hibba kin ta'ba shan Amaśi?"
Cikin sauri na girgiza masa kai, ni ban taba jin sunan bama sai yanzu.
Murmushi ya sakar mun "then you're in for a treat" ya fada yana kiran waitress din tazo ya fada mata abunda zata kawo mana, ya juyo yana duban da'yan abokin nasu wanda ya kira da "Ussy... kai nasan ba sai na tambayake ba nasan kai mayan Amasi ne"
Dariya Ussy ya sake yace "dan ubanka waya koya mun shansa, among the five of us you're the king of Amaśi"
"Five" na maimaita a raina, ina kallonsu don su hudu ne kawai anan, sai kuma na tuno Ak a raina nace kilan shine na biyar a cikinsu. Ina cikin wanan tunanin sai ga waitress din ta karaso da abinci kala kala tazo ta jera a gabanmu, abincin da drinks din komai cikin kwanun gargajiya. Na kurawa abincin dake gabana ido, sam ba irin abincin dana saba ci bane
"Wanan abincin shi muke kira waankye a Ghana" Mufasa ya fada yana mun bayanin abincin dake gabana, shinkafa da wake ne da kuma wata kalan miya haka kamshin abincin dake tashi ya cika mun hanci, ya dauko wata kofi mai kama da kwarya ya cigaba da mun bayani "wanan kuma ademkum, dashi muke..."

YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...