1

97 8 0
                                    

SABUWAR SHEKARA SABON SALO
WACCE KUKA FI SANI DA FADILA IBRAHIM TA ZO MUKU DA SABON LABARI MAI SABON SALO

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

ALMAJIRA Sabon Salo
PAID BOOK

In the name of Allah, The beneficient, The merciful

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai jinkai

_GODIYA_Ina godiya ga Allah maɗaukakin sarki, Mai kowa da komai, Sarkin da babu kaman sa duk faɗin duniyar nan, Ina kara godewa Allah da ya ara min lokaci kuma ya bani ikon rubuta wannan littafi don faɗakar da al'umma baki ɗaya.

Allah ya bani ikon isar da sakon da yake cikin sa, Allah kuma ya baku ikon karantawa.

ALMAJIRA Sabon Salo
Free page

LABARI DA RUBUTAWA FADILA IBRAHIM

01

______________________________________

SHINFIƊA

Kauyen Bakura, wani kauye ne ko ince wata "ƙaramar Alkarya"da yake tsakanin Zamfara da Sokoto wanda kauyen Bakura yana karkashin jihar Zamfara state.

Mutanen Garin mafi a kasarin su Hausawa ne sai Fulani kalilan, Babbar sana'ar mutanen garin shine Noman rani duk dama karamin gari ne ba kasafai suka cika yin kasuwanci ba.

Bakura local government suna da makarantun allo ta almajirai, wanda mafiya a kasarin yaran garin, samari da ƴan mata, yara yara duk shi suka fi zuwa. Tsiraru ne ke zuwa makarantar bokoko wanda sukai mishi lakabi da "karatun nasara"

************************************
BAKURA LOCAL GOVERNMENT
ZAMFARA STATE
14 AUGUST __________________________
10:00am

A bamu na Allah "babiya Allah"
A bamu na Allah "babiya Allah"
Muna bara a bamu don Allah
"babiya Allah"
A bamu don Ma'aikin Allah
"babiya Allah"
A bamu don Mahaliccin mu
"babiya Allah"


Babban titin dake garin Bakura ta hanyar da zai sadaka da babban masallacin juma'a wanda yake kwalli ɗaya tak a cikin garin.

Cike yake da Mabarata wa'inda babu ruwan su, sudai bara kawai su keyi daga wannan kusurwa zuwa wancen kusurwa.

Mabaratan a kalla ba'a kasari ba sun kai mutane ashirin ko fiye da haka ma kowa da irin lalurar da yake ɗauke da ita, wasu lalurar gaskiya wasu kuma lalurar karya,
Shiyasa suke bara don samun kuɗi da kuma abin da zasu ɗan ci su da iyalensu, duk dama da muryoyi ɗaya ko ince a tare suke jero wakar barar sai dai wata zazzakar murya wacce ta fi kowacce murya daɗin sauraro, kana iya jiyo muryar amma yawan al'ummar dake zazzaune wasu suna tsaye ba lallai ka gane wacece mai muryar ba.

Gefe ɗaya kuma ko in ce tsallaken titi masu talla ne, tallan abinci kala da iri, masu soya kosai da kunu, masu awara da dai sauran su wanda mafiya akasarin mabaratan suke musu chiniki daga safe har dare.

Wata babban mota ce kirar toyota baka wuluk ta kunno kai a daidai layin mabaratan, Nan da nan wasu daga cikin mabaratan suka nufi inda motar take, kasancewar ko da yaushe idan ya zo wuce wa yana ra ba musu ƴan hamsin hamsin sabbi dal.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now