20

50 2 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


ALMAJIRA
PAGE 20

______________________________________

Na kai duba na ga dogon saurayin da suka shigo da Laila sai naga wani irin kama da suke yi da Ahmad, su kan su kallon kallo suke yi, shin ta yaya akayi suka yi kama da juna haka?

Ban samu amsar tambaya ta ba, kamar munafukai haka Laila da masu tsaron ta suka fita waje.

Ahmad ya sa mu ka kwashe kaya ya ɗauke mu ya mai da mu gida, zai fita kenan Anna ta yi saurin dakatar da shi ta ce," Yau zan baku labari na"

Baffah ya fito yana tambayar me ya faru ne a asibitin?
Ni na sanar dashi tiryan tiryan, Baffah ranshi ya baci matuka, ya dafe kan sa kamar me nazarin wani abu.

Anna ta ce," Shekaru sama da talatin da suka wuce kamar ba ayi ba.

Kakana na wajan uba, Christain ne kuma haifaffan ɗan ƙasar america yankin ƙasar wales, anan yayi aure kuma suka haifi mahaifina mai suna *Charles Cherie*

Kakana ya mutu a lokacin mahaifina ya gama jami'a karatun degree ɗin sa na ɗaya sai ya ɗaura kasuwanci daga in da Mahaifin sa ya bari, yana zuwa kasashe daban daban don cimma kasuwar sa, ya fara da zuwa Nigeria in da ya haɗu da sabon abokin chinikayyar sa wato Kakana ta wajan uwa.

Hmmm Anna ta murmusa ta ce,"Hadiza bani ruwa na sha"

Na bata ruwa na koma na zauna don jin labari da kyau.

Shekara ɗaya Mahaifina Charles yayi a kaduna sai ya samu riba mai tsoka, hakan ya bashi damar siyan babban fili a Unguwar rimi kan titin Abubakar tafawa balewa way, Marafa estate a cikin marafa anan ya siya fili ya kuma gayyato turawa da suke america suka yi masa tsarin ginin mansion na gidan saurata na america, ginin ya bada citta makura kowa magana yake yi shin wani billionaire ne ke gini a kaduna haka, hakan yasa mahaifina yayi suna sosai aka san shi, Mahaifina ya gina campanoni biyu a garin kaduna wanda ake kawo furnitures ɗin sa da turarukan kampanin sa.

Wata rana mahaifi na yaje gidan Kakana tawa jen Uwa kenan, ya je gaishe sa kasancewar ya jima a kwance bai da lafiya, gidan kakana babban gida ne a halin gidan basu da yawa yawan cin su suna germany, malaysia da sauraran kasashe kasancewar suma suna da ƴan uwan taka da kasar waje, yasa babu mutane da yawa a gidan, Kakana ne kawai da Matar sa sai ƴar su wato mahaifiya ta ita ce auta a cikin su shidda sauran duk suna waje da iyalan su.

Mahaifi na ranar ya fara haɗuwa da Mahaifiya ta kuma ya nuna ya ga matar aure, amma basu amshe shi ba sai da ya musulunta ya koma musulmi.

Sunan mahaifiya ta  *Qibdhiyah* ya samo asali ne daga sunan Mariya, Mahaifiya ta akwai ilimin addini dana turawa, addinin yafi zurfi a ciki domin a Islamic University na ƙasar saudiyyah tayi karatun ta....Mamana ta zaba ma Babana suna Aminu amma ɓoyayyan sunan shi Charles Cherie yana nan.

A lokacin suka zauna a gidan Mahaifi na mai ɗauke da mansions biyu, akwai guest house daga gefe, da kuma flat biyu masu kyau, Shi mutum ne mai akidar america wa, duk da babu kowa a ciki amma haka suke rayuwa kamar suna kasar waje har wajan wasan yara, garden/ wajan shakatawa da swimming pool da sauran su.

Ko wanne sashi ya zuba ma'aikata ana gyara sashin yau da kullum duk da babu mai kwana a ciki amma an zuba kayayyaki kun san abin ku da mai kirkirar furnitures ɗin, babu in da ba a sa kaya ba tamkar dai akwai mutane a ciki.

Babban mansion ɗin da yake tsakiyan filin anan Mahaifiya ta da Mahaifi na suke rayuwar su, har Allah ya basu ciki na suka haife ni anyi babban shagali a garin kaduna wanda ya jawo hankulan mutane gare mu, Sunana *Amina Aminu Cherie* inkiya ta kuma shi ne *Anna Cherie* Amina suna ne ga Kakata ta mace wajan uwa ta.

Na tashi tamkar sarauniya a gidan mahaifi na, ina rayuwa ni kaɗai rayuwar gimbiya nake yi, Mama na ita ke karantar dani a gida daga bisani aka kai ni makarantar Almannar wanda yake karshen titin Abubakar tafawa balewa way Unguwan rimi.

Boko kuma mahaifina ya ɗauko malaman turawa gudu biyar suna koyar dani british english da sauran abubuwan turawa.

Nayi karatu mai zurfi addini babu abin da ban sani ba, boko kam ba a magana malaman maza da mata suna kula da yadda nake speech, ko hausa lokacin bana ji,  iya larabci da turanci kawai na keyi, duk bayan shekara ake sauya min malamai a tura waɗancen wasu sabbi su zo.

Ina gama sakandiri na islamiya na rubuta jarabawa kuma naci....amma mahaifi na sai ya komar dani america, ya bar mahaifiya ta saboda ta shiga wani kungiyar foundation na taimakon mutane sai ya kasance abubuwa sun yi mata yawa, sai yaje america yayi wata uku, wata huɗu har wata biyar ma, yana kasuwanci wani lokacin Mamana tana zuwa ta duba mu suna rayuwar su gwanin ban sha'awa sosai suke birgeni saboda ba sa faɗa, ban taɓa jin wata bakar magana ta fito daga bakin junan su ba..suna matukar hakuri da juna.

Ina da shekara goma sha shidda amma idan ka ganni zaka yi tsammanin ban kai ba, saboda yanayin jikina bani da girman jiki sosai....kwatsam Mamana tazo ta koma sai Babana ya haɗu da wata sabuwar abokiyar kasuwanci sun yi kasuwanci sun gama, amma daga baya sai ta fara bibiyar rayuwar mu, tana bibiyar mahaifi na, ina makaran ta lokacin na koma Ss1, ita ke zuwa ta kai ni makaran ta, ta ɗauko ni, kullin cikin hiɗima take dani, duk da ina da masu yimin komai amma sai tayi kane kane ta nuna tana kauna ta har cikin zuciyar ta.

Tun mahaifina baya saurarar ta har ta kai ma wani abu ya shiga tsakanin su, abin ta kai cin shi ne sun aikata fasikanci sai Allah ya kawo rabo suna rayuwar su batare da Mahaifiya ta ta sani ba har matar ta haifi ƴa mace, Babana ya matukar jin haushin samun ƴa macen don yayi tsammanin Namiji ne.

Da kan sa ya raɗa ma jaririyar suna LAILA.

______________________________________

Thank you all for reading my novel.

ALMAJIRA
STORY, WRITTEN AND EDITED BY
FADILA IBRAHIM
07031086858, wattpad
@DielaIbrahim

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now