11

31 4 2
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
11

______________________________________

Mummy where are you?

"Yes Ahmad ya naga ka dawo da wuri yau hope everything is fine? Mummy ta fito daga kitchen tana tambayar sa, bayan ta zauna akan ɗaya daga cikin jerun kujerun palorn ta masu tsada da ado.

"Eh lafiya ba lafiya ba Mummy" ya mayar mata da amsa yana kokarin kwantawa a cinyar ta bayan ya zauna kusa da ita saman kujera.

"Menene? ta tambaya

"Mummy wacece Daddy yake so na aura naji kun ce haɗin gida, Ina fatan ba su yusrah da sajida kuke son makala min ba"

Mummy tayi murmushi....Yusrah ƴar kanwar Mummy ne wanda suka haɗa uba da ita, Sajida kuma yarinyar brother ɗin Mummy babban brothern ta wanda suka haɗa mama da baba, Nasreen marigayiya ma yarinyar kanin Mummy ne wanda suka haɗa baba da mama ɗaya, sai dai ita Nasreen duk ta fi su natsuwa kuma bata da son abin duniya su kuma akwaj kauɗi da nuna son abin duniya shiyasa ko sun zo gidan basa shiri da shi.

Mummy ta ce,"Nooooo ba su bane Ahmad, na san har cikin ranka ba kwa shiri da su shiyasa ma bamu zaɓa maka mata a cikin su ba.

"To Mummy wa kuka zaɓa min? ya tambaya yana daɗa ya mutsa fuskar shi kamar wanda yaga kashi.

"Ka bari idan lokacin yazo zaka san komai Ahmad...Mummy ta ɗan tsagaita tana tapping bayan sa cikin natsuwa da nuna tsananin kulawar ta gare shi.

Ahmad yayi shiru na ƴan mintuna har bacci ya ɗauke shi, Mummy ta ce,"Ahmad kenan sai ka dawo mun tamkar lokacin da kake karami, halayen ka suna nan basu can ja ba"

Jin yayi shiru sai ta duba taga ashe bacci yayi, murmushi tayi ta gyara zama tare da ɗauko wani novel na turanci daga gefenta dama ganin Ahmad ɗin ne ta ajiye, ta cigaba da karatun ta.

1week later

Yana sanye cikin suit mai tsada navy blue hannun sa rike da briefcase ɗin sa gefen sa Josiah ne secretary sai employees ɗin sa managing director da sauran empoyees biyu suka fito daga cikin babban motar company ɗin su, suna harabar parking lodge na  I.B CONS.....LTD, kunnan sa bluetooth ne yana waya da Daddy, Daddy na kara jaddada masa yan da plan ɗin yake saboda yau shugaban company ɗin yazo Nigeria kuma yace dole yau zaiyi meeting da Lawal CONS.....LTD.

Suna shiga aka karɓe su hannu biyu sannan akai musu iso zuwa babban conference hall da suke meeting, kowa ya hallara a meeting ɗin gaba ɗaya sai ya ga wasu daga cikin ƴaƴan mai company ɗin sun mike tsaye cike da mamaki kamannin ɗan uwan su sak a fuskar ahmad kara ra.

*Ahmad ya gaishe su da turanci, a zabure suka amsa suna daɗa kwaɗaituwa su san labarin sa shin ko dai Ɗan dan uwan su ne.*

A dai dai lokacin shugaban ya shigo farin balarabe tsoho ne mai ran karfe kuma ainahin suit ne a jikin sa masu tsada maganar sa da sauri sauri kamar ɗan america duk da ma dama daga cen ya fito kasar america ba ka isa kace ba bature bane, amma asalin sa ɗan Nigeria ne.

Ya samu waje ya zauna ya ba ma kowa umarnin zama sannan ya fara magana.

"Fatan kowa yana lafiya? uhmm dalilin haɗuwan mu anan shine saboda state contract ɗin da London suke so company ɗina tai musu. Tabbas sun nemi irin wannan aikin shekaru fiye da talatin da suka wuce kuma an samu mishkila, yanzu kuma sun dawo akan suna son ayi musu, so fa suka same ni da maganar sai nayi research na gano Lawal cons...ltd suna aiki irin na company ɗina so kuma na san idan muka haɗu mu kayi wannan aikin In Sha Allah za'a samu reward fiye da yan da kowa yake zato.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now