07

32 2 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo
PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
07

______________________________________

Cikin rantsatsiyar motar sa kirar mercedes, baka wuluk da tinted, yana hakimce a seat ɗin baya yayin da yana ta danne danne a wayar sa iphone 11pmax, ba wani gudu Josiah yake yi ba, a tsanake yake tuka ogan nasa ganin ko magana ba yayi har suka isa airport.

Ya fita da sauri jin ana ta kiraye kireyen suna alamar jirgin ya kusa tashi, tsayawa yayi yana cewa "Josiah keep your phone very close to you because I may call you any moment"

"Okay sir" Ya amsa yana cewa "Safe trip sir"

"Thank you" Ya faɗa a hankali yana tafiya da ɗan sauri sauri.

9am
Karfe tara da ƴan mintuna ya isa zamfara, sai da ya hau motan kasuwa aka kai shi har Garin Bakura, Zuciyar sa fal damuwa, cike da mamakin ganin jama'an garin duk sun ragu ba kamar watannin baya da suka shuɗe ba, Anyi kone konen shaguna da gidajen mutane, He was very shocked, Ya tattara sauran kuzarin sa ya faraf tambaya... Da kyar ya samu amsar iftila'in da ya samu garin.

Zama yayi a wani dakali daga gefen titi yana dafe kan sa da ya fara yi masa ciwo ta forehead ɗin sa, Sake daure wa yayi, ya kuma tattaro natsuwa da sauran kuzarin na sa ya nufi wajan wasu masu bara don ya tambaya ko sun san in da zai iya samun ta.

Ya tambaya, amma ba su gane wacce yake faɗa ba, yana tsaye yaji ana magana ta bayan sa.

"Ko Hadiza mai ciki kake nufi tana goya yarinya karama ?

Da sauri ya ce "Eh, Eh ita nake nufi, ina zan iya samun ta don Allah?

"Gaskiya tabi ayarin da suka riga mu barin garin wata ɗaya kenan, naji dai ance kastina suka je"

"Ahmad ya dafa kan shi ta ina zai fara neman ta a katsina ya salaam, me yasa zai faɗa soyayya da wadda ma bata san yana yi ba, me yasa zuciyaar shi ta amince da wahalalliyar soyayyar Almajira, ya daki wani taya dake gaban sa, idanuwan sa sunyi jazir, Da kyar da karayar zuciya ya nufi park ɗin kai tsaye ya hau mota ya koma airport.

12pm yana gida cikin ɗakin sa lulluɓe cikin lallausan bargo yana kakkarwar zazzaɓi, bacci mai nauyi ne ya ɗauke sa.

______________________________________

Ranar dai haka su Anna suka dawo suka iske ni ina cikin tsananin damuwa na rayuwar da na tsinci kai na, da kyar ta rarrashe ni na ci abinci,

Muna zaune gaba ɗayan mu a barandar ɗakin ta ana ta yayyafi kaɗan kaɗan garin yayi lub lub gwanin ban sha'awa, Cikin hasken farin wata daya fito raɗau da alama ba ruwan sama sosai za a yi ba.

Anna tace,"Bani labarin ku Hadiza"

Na ɗan tsirta yawuu sannan na kalli Baffah wanda ya kafe ni da idanu kamar dai yana gani na....Na ce,"Ina tsananin bukatar mahaifi tun tashina amma bamu san waye mahaifi ba sai dai kalmar kawai muka sani....na ɗan tsagaita kafin na fara bada labari na kamar haka.

ASALIN MU__________________________
Garin Ingall dake Arewa maso yammacin Nijar kamar yadda kuka sani Buzaye ne da Wodaabe

Mahaifi na Sunan shi *Abdul-rahim* balarabe ne, Kamar yadda Ummu na ta faɗa min bata san ko shi ɗan wani gari bane amma ya faɗa mata  kasuwanci ya kawo shi garin Ingall na arewacin Nijar yadda ya sanar da Ummu na, anan ya haɗu da mahaifiya ta buzuwa.

ALMAJIRA ✔Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt