18

27 2 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


ALMAJIRA
PAGE 18

______________________________________

Yayi relaxing a kan kujeran dakalin ya zauna very confortable ya mikar da kafafuwan sa, sannan ya nannaɗe hannayen sa akan kirjin sa ya lumshe idanuwan sa yana tunani.

Ina gefe duk ina kallon sa sai naga ya birge ni karo na farko kenan a rayuwa ta da naga wani ɗa namiji ya birge ni, na zuba ma kwantaccen sajen sa ido da lallausan bakin gashin kan sa tamkar na lararabawa tsabar laushi da taushi da kyalli da komai ma, kamannin Anna ne sak a fuskar sa, ban san lokacin da nace," Amma kasan kuna yanayi da Anna ko?

Ko gizau kuma bai ko buɗe ido ba balle ya kalle ni, idanuwan sa suna a rufe sai naji sautin murmushin shi mai sanyaya zuciyar mai sauraro, sai Ya ce,"Na sani khadija, amma kin san wani lokacin dama kana haɗuwa da mai kama da kai kuma sai kiga ma babu abin da kuka haɗa da shi" ya faɗa daidai lokacin yana kokarin tashi don zuwa yin sallar magriba, ina kallon sa yayi alwala a famfo ya dawo waje na ya ce,"Khadija, bari naje masallaci na dawo, ke ma ki tashi kiyi naki sallan"

Na gyaɗa kai nima na tashi na nufi wajan fanfo, na gama alwala na dawo wajan na shimfiɗa kallabi na, na fara sallah.

Ina zaune a wajan har ya dawo ya iske ni ina addu'a zama yayi yana mai ɗaga hannu shima ina tofawa shima ya tofa yana cewa,"Amin ya rabbi Allah ya karɓa addu'a"

Murmushi nayi kawai na ɗan kalle shi a sace...Kamar almara sai naji ya ce,"Kallon ya isa haka *ƴar buzuwa na* "

Ya faɗi sunan da ya sani saurin kallon sa da mamaki a fuska ta, sai ya tuna min da mahaifiya ta, duk dama da wasa ya faɗi hakan amma sai naji wani iri a zuciya ta ina tunanin ko wani hali take yanzu oho sai Allah, wata kil ma ta rasu tun da jima wa...Hawaye ne suka sauko ɗigo ɗaya na sa hannu na share gefen kumatu na.

Na buɗe ido sai na sauke su tangaran a fuskar sa babu yabo babu fallasa yana kallo na, idanuwa na suna kasa sai naji tattausan hannayen sa suna share min hawayen fuska ta.

"Ki dena kuka kinji, ba kina da Anna ba?

Na gyada kai kamar wata ƴar yarinya hawayen na kara sauka a idanuwa na.

Ya sake ya ce,"Ba kuma kina da Baffah ba?

Na sake gyaɗa kai na sa hannu ina share guntun hawayen ina sauraran sa.

Ya sake sunkuyo wa daf da fuska ta idanuwa na suna kallon idanuwan sa, ina jin numfashin sa na fita ta siririn hancin sa, Ya ce,"Sai wa kuma?

A daburce na ce, "Sai Sofia"

Ya sake marairaice fuska Ya ce," Sai wa kuma"

Wannan karan shiru nayi dukkan jiki na kyarma ya ɗauka, ni kam ya fara bani tsoro, miye kuma haka yake yi?

Ni kam ta shi nayi da sauri zan bar wajan sai naji ya rike min hannu ya taso ya dawo ya tsaya in da nake, na runtse ido na shi kuma yana kallon fuska ta,

Ya ce,"Kin fara tsoro na ko?

Da sauri na buɗe ido na sauke su akan na sa kamar zan yi kuka, ya karanci zuciya ta, na daure na ce,"Don Allah Yaya..........ban kai ga karasa wa ba sai naji hannun sa akan baki na yana girgiza kai yana cewa,"Zan dena kinji" 
Na ɗaga kai na kalle sa sai naga yana ɓalle boturan hannun rigan sa shirt ne dama da wandon jeans, ya sanya tun da safe da yayi wanka....Ina kallon nasa sai naji ya kuma cewa,"Amma sai dai idan zaki raka ni wani waje yanzun nan"

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now