05

32 3 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo
PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGE
05

______________________________________
KADUNA STATE
4:00pm

Da misalin karfe hudu na yamma motar tamu ta iso kaduna Allah mai kowa da komai yau gani kuma a garin kaduna, garin da ban taba tunanin zan zo ba nayi saurin yin addu'a cikin zuciyata nace,"Ya Allah sarkin sammai da kassai, sarkin da babu kamar sa duk faɗin duniyar nan, Allah gani kuma a garin da babu kowa nawa, babu Uwa babu Uba sai kai mahalicci na, Allah ka tsare mu da ni da kanwa ta kamar yadda ka tsare ni a garin BAKURA, Allah ka kare mana mutuncin mu ka kuma bamu ikon tsare imanin mu" adai dai lokacin na ji Mai tuka motar yana cewa "Jama'a muna ainahin gadar kawo wa zai sauka mai motar ya ji shiru, hakan ya bashi damar shiga wani tasha wai NURTW ana kiran tashar da tashar kawo nima dai nan na sauka ganin duk mutanen sun sauka, nai musu godiya na kama hanya ta zuwa bakin titi.

Tun da na fara bara ban taba ji an kira ni da sunan Almajira ba in ba HADIZA ba, amma muraran yau naji ance ALMAJIRA yaki zo ga sadaka.....ji nayi gaba na ya faɗi warwas, lallai fa na shigo kaduna dama ance garin kazo na zo babu kara ko kaɗan,

Na wai ga don ganin me kirana, sai naga wasu samari masu shan sholisho da wee wee  da taba sun haɗa dabarsu suna yafito ni da hannu, Ban san lokacin dana ci tuntuɓe ba na faɗi kasa jikina na rawa na tuna abin da ya taba faruwa dani tun bayan rasuwar mahaifiyata, haka na daure na mike tsaye na ɗauki kullin kaya na na bar wajan da gudu ina rufe Sofia wacce take baya na, don ko da wasa bazan taba bari wani yaci zarafin kyakkyawar kanwa ta ba, gudu nake a hankali har na isa daidai karkashin gadar wato abin da idanuwa na suka gane min shi ya sa ni tsayawa ina daɗa kare ma wajan kallo, ban san lokacin da kwalla ta soma zubo min ba ɗaya bayan ɗaya hawaye kuka kawai nake yi, ina tausayin rayuwar mabarata lallai rayuwar ALMAJIRAN CI abin tausayawa ne.

Wato yawan alumman wajan duk masu bara ne maza da kuma mata, tsofaffi tukuf, dattawa, samari da yan mata,yara yara da jarirai akalla ba a kasari ba zasu kai dubu biyu manne awajan angle angle kowa da kwanon baran sa, wasu guragu, wasu babu ma kafar takawa, wasu hannu ne babu, wasu kuma ciwuka ne a jikin su, wasu makafi babu idanu sai faman yawo da sanda, wasu ko magana basayi kurmaye ne, wasu kuma garau sumul suke.

Ai a jiye kullin kaya na nayi na samu waje na zauna ina kare ma mutane da masu wucewa da motoci manya, buses da mashina, da taxes sai faman kai da kawo su keyi.

Na share zufan data keto min a fuska ta, bayan na sauke Sofia ina ɗan dubawa ko zamu samu masu sai da abinci....Na wai ga gefena sai naga wani bawan Allah an sanya mishi drip yana kwance ga wani karamin yaro yana rike da drip ɗin a hannu da alama duk ya gaji, ban tanka su ba ni dai Sofia nake son ba ma abinci na san taji yunwa rabon mu da abinci tun jiya da yamma, sai ruwa kawai muke ta kwalkwala.

Sai da naje tsallaken titi kafin na samu masu sai da abinci na siyo mana na dawo na iske safiya zaune wajan mara lafiyan nan, dama nan na barta, na zauna ina bata abinci kamar kullun sai da ta koshi kafin nima naci nawa, daga bisani muka zuba idanu muga yadda Allah zai yi da rayuwar mu gamu dai a tsakiyar titi karkashin gada muna ta shan inuwa.

**********

ABUJA, Maitama_____________________________
7:00am


Ahmad mutum ne mai faran faran da sakewa da ƴan uwan sa da kuma jama'ar sa, yana da son mutane sannan yana son kyautata wa mutane waɗan da basu da shi, ma'ana yana son taimakon na kasa da shi, sai dai akwai halin sa guda ɗaya wato Zuciya.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now