SOFIA

35 0 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
_Shafin farko Tsokaci_

As we all embark on this amazing journey, the journey will surely make you laugh, cherish, and it may make you cry as well as it take you to different planet of your own imaginations.

*SOFIA mabiyin ALMAJIRA ne, ban sani ba ko zaku iya sanya shi a matsayin cigaban labarin amma SOFIA sabon labari ne mai ɗauke da sarkakiya da kuma kaddarar da ta shafe ko wacce kaddara zafi da ciwo a duk lokacin da mutum ya tsinci kanshi a irin wannan yanayin sai ya gode ma ubangijin halittu, domin kuwa shiya fi kowa sanin halin da bawa yake ciki*


Bismillahi_Rahmanir_Rahim

2005

CENTRAL MARKET DUTSE JIGAWA STATE

7:30am
Sanarwa!! Sanarwa!!! Sanarwa!!!!!

"Sanarwa jama'an jahar Dutse, yau akwai dare biyu ma'ana kusufin wata, kowa ya zauna a muhallin sa, masu zuwa makaranta yara da manya ku zauna a gida, masu zuwa aiki yara da manya kowa ya zauna a gida" Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!! "Yau da misalin karfe goma akwai kusufin wata, muna rokon kowa da ya zauna a gida, kada kowa ya fita yau"

Wata karamar radio mai area wacce take jingine da bango a kan teburin wani baba tsoho mai dabino da kwakwa yayin da wasu daga cikin masu shagunan da teburin sa yake jingine da wajan yanzu suke zuwa wasu kuma suna gida, da yawa sunji sanarwan, wasu kuma basu ji ba hakan yasa ake ta fita domin kowa yayi hiɗiman gaban sa.

"Da alama yau baza a cika a kasuwar naa ba" Cewar mai dabino da kwakwa.

"Nifa kasan Allah ado, yau da gangar na fito don ni bana yadda da abubuwan taurarin da masana kimiya suke faɗa" cewar wani mai kayan koli ya kimtsa kayan sa a baro yana ta faman kakkaɓe kakkaɓe.

Wani daga cen nesa dasu ya ce,"Ilimjn taurari fa gaskiya ne, wani abin kuma su kan su basu san shi ba amma sai ayi ta nanatawa"

Ado mai dabino ya ce,"Ni wallahi bana so na rasa costomomi na ne na karfe takwas ɗinnan kuma da alama yau Yarima zai zo cin dabino saboda jiya ban gan sa ba"

"Dallah ka ishe mutane da wani yarima, idan Yarima na son dabino to su shuka bishiyar mana a farfajiyar filin masarautar mana, ko ba haka ba da zai fi ai"

"Kai Shu'aibu ka iya bakin ka, ina ce idan yazo kafi kowa ƴar murya don ka samu a samma ka wani abu, amma kana nan kana maganar banza akan sa".........Ado mai dabino ya rufe baki kenan suka ga tsayuwar motar Dakaru ne suka fito suka amshi mudu biyu aka bashi dubu biyar batare da an tambayi canji ba.

Har bakin motar yaje yana godiya, yayin da ko gilashin motar ma ba a ɗaga ba suka ja motar suka tafi...ya koma yana murna yace,"Na gama aiki na na yau, tun da dama akwai dare biyu kafin yazo bari na kama kai na"

Mai kayam koli ya zumbure baki yana hararar sa, ɗayan kuma yana musu dariya, Ado maj dabino ya kwashe dabinon sa ya kife teburin sa sannan yace,"To jama'a Allah ya bamu alheri sai kuma gobe idan Allah ya kai mu"

Mai kayan koli kam bai kula sa ba, saboda shi dama ainahin sa mai hassada ne.

Islamic Standard Comprehensive School Dutse.
8:00am

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 17 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now