10

31 2 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
10

______________________________________

Murna ta sani kasa cin abin ci, ina ɗoki na zumbula hijab ɗina da ɗan silipas ɗina, na kalli kanwata Sofia wacce take zaune daga gefen bakin kofar ɗaki tana ta min murmushin ta mai kara fito da asalin kyan da Allah yayi mata.

Na tsugunna na kai fuska ta dai dai saitin fuskar ta na sumbace ta a goshin ta saboda murmushin ta ya wadatar kuma ya fahimtar dani cewa Sofia na min murna zani makarantar islamiyyah.

Baffah ya rike min hannu har muka kure layin gidan na mu, muka isa bakin titin muka tsallaka sannan muka shiga wani layi anan naga islamiyyar kai tsaye kofar makarantar islamiyyar muka tsaya yayin da naga ɗalibai suna ta karatu a ciki.

Sallama muka fara musu kafin akai mana iso ofishin headmaster na makarantar, anan su ka bamu bayanai akan komai yadda za muyi register, kuɗin makaranta, littafai, da kuma kayan makaranta.

Dama kuɗin suna wajen Baffah ya ciro su duka ya mika min yana cewa, "Hadiza ki cire kuɗin makarantar da na littafai ki bayar"

Na karɓa na cire na biya komai aka sani a aji ɗaya saboda ban iya haɗa baki ba da komai ma, har hadda sai da na shiga, suka bamu kyallen yadin makarantar, ash color.

Muna fita muka wuce kasuwan rafin guza anan muka yanki yadin muka bada ɗinki, aka min Babban hijab 4yard da wando da farar riga ƴar ciki.

Ranar dai sai misalin karfe biyar muka koma gida.

Anna na tsakar gida tana ta kiciniyar sauke girkin dare wanda ta gama a murhun itace...Sofia na kan baranda tana wasan ta.

Ni nayi ta wajan Anna da murna ina bata labari abin da ya faru yau..
Baffah kuma yayi ta wajan Sofia da leda a hannu yana kiran ta ƴar baba zo ga tsaraban kifin ki na siyo miki, Haka suka zauna yai ta bata kifinnan har ta cinye.

Kallon su kawai nayi naji wasu hawaye sun zubo min wanda ban san ko hawayen dadin ganin su tare suna nuna tsananin kauna na ƴa da uba a tsakanin su....Na samu waje na zauna ni da Anna ina lissafo sunayen littafan da aka bani na aji ɗaya wanda ta ce ma ita zata rinka kara min karatu idan an mana sai ta sake koya min, hmmmm ni dai na kalli Anna na kau da kai na gefe, Ina mamakin yadda mutum wanda baya gani zai yi karin karatu kuma ma ita Anna me ta sani, duk tunani na ya na bani Anna bata yi karatun komai ba.

Washe gari ranar lahadi.

Wannan ranar ta kasance rana mafi soyuwa agare ni domin kuwa ita ce ranar da ta kasance wani sashi daga cikin rayuwa ta ya canja launi kwarai kuwa domin na fara karatu wanda a da cen baya ban yi tunanin haka zata kasance da ni ba, ga shi cikin kankanin lokaci Allah ya shafe min wahalhalun da nasha a baya duk da na san bawai rayuwar tawa ta canja bane amma gwara rayuwa ta ta yanzu saboda ko ba komai muna killace a cikin gida kewaye da uwa da uba duk da cewa makafi ne amma sun fi min komai a rayuwa yanzu saboda idan ba dan su ba da ba zamu samu lilliɓi ba.

Babu abin da zan ce wa Baffah da Anna sai dai godiya da kuma addu'ar Allah ya saka musu da mafificin alkhairi.

Yau ita ce rana mafi wanzuwa a cikin ranakun rayuwa ta, na fara zuwa makarantar islamiyya sannan ranar da zan fara haɗuwa da mutane daban daban, yare daban daban kuma hali kowa da nasa, na kudiri aniya In Sha Allah abin da ya kai ni makaranta shi zan yi.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now