03

39 4 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo
PAID BOOK


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

Free page
03

______________________________________
ABUJA
Maitama

9:00am

Katafaren gidan Arc.Lawal Muhammad dake cikin unguwar maitama cikin birnin tarayya wato abuja, Gida ne na alfarma, mutane ne masu ganin mutuncin alumma talakawa da masu kuɗi duk nasu ne.

Arc. Lawal Muhammad haifaffan garin KANO ne anan ya tashi da iyayen sa, Iyayen sa suka nuna masa gata, Suka nuna masa so da kauna ta hanyar sanya shi a makaranta tun daga kan primary, secondary daga nan ya tafi jami'ar BUK yayi karatun Architecture fannin zane.

Allah yayi ma Mahaifinsa rasuwa dama kuma shikaɗai mahaifiyar sa ta haifa hakan yasa ya fara neman aiki kullin cikin jajircewa yake akan neman na kansa, Tabbas abin da Daddy yake so ne Architecture sosai amma Allah bai bashi wannan baiwar ta zane ba duk yadda zai zana abu to ba lallai yayi ma kowa kyau ba.

Allah cikin ikon sa sai ya samu aiki a wani Construction Industry company da yake tashe a garin Abuja mai suna I.B WORLDWIDE CONSTRUCTION LIMITED wannan company ɗin shi yayi leading ɗin sa to so many successes daya samu a rayuwa ya samu alkhairi wanda bayan shekaru goma Allah ya buɗa masa ya bar I.B WORLDWIDE CONSTRUCTION LTD..... Allah mai kowa da komai ya bashi arzikin da shi ma ya mallaki nasa Construction industry din mai suna LAWAL CONSTRUCTION LTD kuma ya sanya Babban ɗan sa Ahmad as CEO .

Sannna ya gina babban gida ya ɗauko Mahaifiyar sa Hajiya Nusaiba wanda suke kira da *Nene* ya gina mata filin bayan gidan sa ya zuba mata komai na rayuwa sa'annan ya kewaye mata har da gate ta hanyar baya, amma ya mata karamin kofa ta cikin gidan sa.

Daddy matar sa ɗaya Hajiya Na'ima yaran su huɗu
Ahmad
Kamal
Nadiya nd Nurain

Kamal matashi ne wanda yanzu ma ya shiga jami'a inda yake karanta MEDICINE wato karatun likita shi yake so, yana UK yana shirin dawo wa gida hutun level 1, Session ya kare yace shi gida zai dawo yayi hutun sa.

Nadiya yanzu take gama secondary school she is just 16years old suna jiran a fara rubuta waec, Sai Nurain da ya gama primary school, Secondary zai shiga.

Ahmad kyakkyawan saurayi ne mai aji da ƙasaita, bai cika yawan magana ba, Allah ya zuba masa baiwar zane iri da kala, shi yake kara janyo hankulan mutane zuwa company ɗinsu, ga ilimi domin kuwa PHD gare shi...Daddy yayi masa auren wuri tun yana shekara 25 ya auri Nasreen, ita kuma tana 17, amma Allah yayi mata rasuwa, Nasreen ƴa ce ga kanin Mummy mai suna Abdullahi shine suka musu auran zumunci.

Auran su shekara ɗaya Allah yayi mata cikawa sanadiyar haɗarin mota tun bayan rasuwar ta, Daddy da Mommy suke bin sa Allah da Annabi ya kara aure yanzu ana neman shekaru biyar da rasuwar amma yaki yadda yayi wani auren...... Ahmad is just 30 duk sanda Daddy da Mummy suka bata masa rai akan maganar aure fita yakeyi ya kwana a hotel tun bai fara neman mata ba har ya fara sha'awar neman mata.

So da dama idan ya kira mace in batai masa ba zai bata kuɗin ta, yace mata "Spent the night and leave"
Wasu ƴan matan idan suka amshi kuɗi suka ga babu alamar zai kwanta da su tafiya suke yi.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now