08

30 1 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
08

______________________________________

Ranar da ba zan ta ɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwa ta, garin da Abiy ya ajiye mu, ƴan boko haram suka samu damar shigowa garin suka tarwatsa rayuwar al'umma abin babu kyan gani yayi muni da yawa.

Ummu kwanan ta biyu dama bata lafiya ko hannun ta bata iya ɗagawa rashin lafiya ya kwantar da ita, ba wani abincin kirki sai amai duk abin da taci amai take yi.

Hayaniyar da yayi yawa, Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un abin da kowa yake faɗi kenan, hargitsi, tashin hankali da tarzoma ya fara zuwa ta in da muke, Harbe harben bindiga da hayakin bomabomai shi ya turnuke ko ina, jama'an gari kowa yana neman ta kan sa, kana gudu kana neman maɓuya sai dai kaji harbin bindiga a jikin ka....Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un, wannan tashin hankalin dame yayi kama ni Hadiza.

Muna cikin rumfar mu, mun dukun kule juna a wani kusurwa cikin rumfar tamu Ummu na babu abin da take sai kuka tana bamu hakuri, cewa, "Hadiza kinyi girman da zaki mallaki hankalin ki Hadiza ki kula da kanki kuma ki kula da kanwar ki, Don Allah kar ku bari ruɗin duniya ya rufe muku idanu, ku kasance masu tsare mutuncin ku a duk in da kuke, ke yarinya ce da Allah yai miki baiwar sura da kyau Hadiza don Allah ki zama mai ɓoye surarki da kyan ki ko da kuwa bara za kiyi  shine zaki ci ribar rayuwa" ta tsagaita saboda aman jini da ta keyi, hankali na ya kuma tashi kuka sosai na keyi, Ummu na cewa "Ku gudu kar suyi muku wani abu.

Har na goya Sofia na ɗauki kullin kayan mu sai naji hawaye na bin kumatu na, ina takaicin wai ni na bar Ummu cikin wannan halin naji ba zan iya tafiya na bar Ummu na halin ba.

Muna zaune kuwa sai gasu sun iso, ganin kyayun da Allah yayi mana yasa suka tarkata mu ni da Sofia suka sanya mu a mota, har mun yi nisa sai na ji harbin bindiga a ta rumfar Ummu na, Ina tunanin sun kashe min Mahaifiya ta tun a wannan lokacin.

Kuka ne ya kwace min na tsagaita ina kuka mai tsuma zuciya sosai Anna take rarrashi na, sosai Baffah yake rarrashi na, shima tausayina ya mamaye mishi zuciya.

Na tashi na debo ruwan sama cikin randa na dawo na zauna sai da nasha na kwalkwala sannan na sauke nannauyen ajiyan zuciya kafin na cigaba da cewa,

"Karfin hali da jajircewa irin nawa na sauka daga motar da gudu naje ina duba rumfar danna tabbatar da abin da kunnuwa na suka jiye min.

Labari ya sha banban domin kuwa babu Ummu na babu alamar ta a rumfar ko ɗigon jini ban gani ba, sama da kasa, lungu da sako babu ita na duba gabas da yamma babu wata mai kama da Ummu na....da karfi naji an jani aka sake wurga ni bayan motar toyota tsohuwa wanda bayan ta abuɗe yake, idanuwa na suna kan rumfar tamu ina mamakin ina Ummu na? har mu kayi rumfar ta ɓace wa gani na.

Tafiya mai tsayi mu ka yi, ayi a huta har muka kawo wani gari wai shi sakkwato/Sokoto daga nan aka yada zango a wani daji wanda ko hayaniyar mutane ba kaji sai kukan tsuntsaye.

Ranar dai kaddara ta faɗamin domin kuwa, a cikin ƴan mata sama da goma da suka sace, sun yi ma shidda fyaɗe ciki ma har da Ni.

Tsakar dare kowa ya rintsa, na daure na tashi na goya Sofia wacce take gefena tana ta baccin wahala, karamar yarinya wacce bata san komai ba a rayuwa tana ta fuskantar tashin hankalin da bata taba gani ba, wallahi a gaban idanuwan ta su kayi mana kacha kacha, ina jin sautin kukan Sofia tsoro na Allah tsoro na kar suyi mata wani abu.... shiyasa na goya ta, saɗab saɗab na bar wajan duk da ina jin ciwo a kafa na, amma haka na ɗaure ina ta falfala gudu a cikin jeji wanda bana ganin komai sai duhu.

ALMAJIRA ✔Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin