16

24 4 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
16

______________________________________
ABUJA

Katafaren palorn Arc.Lawal masaukin baki babba ne ɗauke da kaya na gani na faɗa, falon ya ɗau gyara da tsabta, kamshin turaren wuta ne ke ta faman tashi duk dama tagar falon manya manya dogaye a kulle suke ruf, labulaye ne aka bubbuɗe kawai,

Bakin suna zaune a gefe ɗaya na bangaren da 3 sitter take suna shakar numfashin a.c yayin da aka kunna musu t.v abokin hira duk dama su damuwan su su ke yi.

Suna jiran shigowan Daddy, suna ta faman tattaunawa akan wani batu suna kus kus abin su wanda yake zaune a falon ma ba lallai yaji ba balle kuma na waje,  an kawo musu ruwa da kayan marmari...basu taɓa komai ba su dai jira kawai su keyi mutanen gidan su shigo, illai kuwa sai ga Daddy ya shigo ta kofar ciki da sallamar sa yana basu hakuri ashe ya san da zuwan su.

Ya samu guri ya zauna sannan ya gaishe da su cikin girmamawa ba wasu bane illa shugaban campanin I.B WORLDSWIDE CON'S LIMITED da kanin sa da kuma yaran sa guda biyu.

Daddy ya ce,"Barkan ku da zuwa"

Suka amsa da yawwa Lawal, fatan mun same ku lafiya?

"Lafiya lau, ai na ɗauka kun koma London saboda naga an gama signing contract ɗin tun ranar juma'a, sai jiya kuma Abdulrazaq ya kira ni yana shai da min cewa kuna son gani na a gida na" Yaɗan tsagaita kafin ya cigaba da cewa, "Fatan dai komai lafiya ko"

"Lafiya lau" Shugaban ya amsa sannan ya ɗaura da cewa,"Wato wani babban al'amari ne ya sa mu jimawa a Nigeria, da yanzu mun koma tun da har an gama signing project ɗin kuma sun tafi da shi muna jiran feedback ne ma daga wajan su, ya ɗan tsagai ta kafin ya cigaba ......  "To amma ba wannan matsalar bace take tafe damu"

Daddy ya ce,"Ma Sha Allah, Allah ya sa muji alkhairi, "Wata matsalace take tafe da ku kuma *Papa*" ya tambayar kamar yadda kowa yake kiran sa, Allah yasa zan iya warware ta"

"Wato Arc. Lawal ,  "Ahmad ɗan ka yana mana mugun kama da ɗana Ibrahim, kuma nayi tsananin bincike akan sa da kuma neman ɗana daya jima da barin a halin sa tun kuruciya kasan da haka tun da ka san Ibrahim farin sani" cewan shugaban.

Duk da sanyin a.c dake hura falon amma sai naga Daddy ya soma zufa ta goshin sa, yayi shiru jin wata sabuwar magana, tabbas ya san batan Ibrahim amma bai isa ya faɗi dalilin ɓatar abokin nasa ba, ta iya yuwuwa matsalar tasu ta gida ce, tun da bayan yayi aure kawai aka neme shi aka rasa.

Amma yana da yakinin babu wata dangantaka da ta haɗu tsakanin su da Ɗan sa Ahmad, duk da bai san su waye asalin mahaifan Ahmad ɗin ba,

Yayi ma Mummy alkawarin maganar cewa Ahmad ba ɗan su bane ba zai sake fita ba daga yau, Da kyar ya buɗi baki ya ce,"Tabbas ni ko na san Ibrahim domin kuwa abokina ne tun kuruciya, kamar yadda kuka rasa shi haka nima na rasa shi, sai dai ni ban ga wata kama ba a fuskar Ɗa na Ahmad da aboki na Ibrahim, domin kuwa Ahmad ɗa na ne na ciki na, zai iya yuwu wa kamanni ne kawai" Shawaran da zan bayar ita ce da zaku dage akan nemo inda Ibrahim yake da shikenan matsala zata warwaru, amma bana son abin da zai tayar ma iyali na da hankali Papa"

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now