02

47 3 0
                                    

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

ALMAJIRA Sabon Salo
PAID BOOK

In the name of Allah, The beneficient, The merciful

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai jinkai

_GODIYA_Ina godiya ga Allah maɗaukakin sarki, Mai kowa da komai, Sarkin da babu kaman sa duk faɗin duniyar nan, Ina kara godewa Allah da ya ara min lokaci kuma ya bani ikon rubuta wannan littafi don faɗakar da al'umma baki ɗaya.

Allah ya bani ikon isar da sakon da yake cikin sa, Allah kuma ya baku ikon karantawa.

ALMAJIRA Sabon Salo
Free page
02

LABARI DA RUBUTAWA FADILA IBRAHIM


______________________________________
ZAMFARA STATE
BAKURA

BRAND NEW DAY
Wayewar gari da sanyin safiya Hadiza da Sofia sun tashi suna kakkarwar sanyi, alamar ruwan saman da akayi ya saukar da sanyi sannan sanyin ya ratsa jikin su yana niyar yi musu illa, gata da karamar yarinya, bugu da kari tana ɗauke da ciki.
~~~~~~~~~~~~~
Da kyar nike iya ɗaga kai ina kallon masu wuce wa a kan hanya yayin da nike zaune daɓas a kasa Sofia na kwance saman kafata yau bana da kuzarin da zan iya ɗaukar ta har mu tafi filin da mabarata ƴan uwan mu suke bara,....bama iya wannan kaɗai ba zafin da jikin Sofia ya ɗauka tamkar dai kwan dake kunshe cikin makwancin kaza shine babbar matsalar da ta sanya ni tunani haɗe da zubar da kwalla saboda halin da muke ciki.
          
Bara nikeyi cikin zazzakar murya ta, Yayin da mun fi awa ɗaya duk muna tsaye gaban ƴan mata masu robobin kosai, awara taliya da wake da manja...amma ko asi bamu samu ba a galabai ce na samu jikin bango na tsugunna haɗe da kunce goyon da nayi ina share wani zufa da yake keto min babu kakkautawa....tagumi na zuba ina takaicin rayuwar da muka tsinci kan mu babu gata ko kaɗan in ban da kaddarar rayuwa kuma dole mu karɓe ta hannu biyu don samun salama a wajan ubangiji domin kuwa shi daya bamu wannan rayuwar shi yafi kowa sanin halin da muke ciki,shiyasa kullin babu abin da nike ambato sai sunan sa don samun sassauci.

Ina kallon kyakkyawar kanwata Sofia wanda a ka bar ni da jagorancin rayuwar ta, hakika wahala ya sa ta dafe hasken fatan mu dama ba ɗaya bane ita ainihin fara ce mai yellow, yanzu kam babu shi ta dafe tsabagen wahala, sai yala yalan gashin kanta dogo wanda nayi mata kitson kalaba sune suka sassauko gadon bayan ta don Allah ya bamu gashi kamar na ƴan ethopia, kamar kuma bororo wato fulani kamar kuma na buzaye
*Ni Diela nace,"Amma gashin ku yafi kama dana ƴan ethopia to ko ma dai daga kasar kuke don zubin ku zubin ƴan ethopia ne sak, ni dai ina ta sake sake a zuciya ta, kamar almara naga an miko ma HADIZA take away na abinci, kamshin shinkafa da jar miya ne ke fitowa daga cikin take away ɗin*.

Duk da muna cikin matsanancin yunwa amma hakan bai sa na karɓa da wuri ba, sai ma ɗagowa nayi ina kallon mai miko min abincin wanda tuni ya ajiye min a kasa ya juya ya tafi ganin zan ɓata masa lokaci, suit ne a jikin shi bana iya hango fuskar ta shi sa'annan har ya shiga wata zukekiyar mota, ban hakura ba na bisu da kallo cen naga sun kuma tsayawa wajan mabarata suna raba take away...wanda na gansu makil a bayan wata toyota da alama wanda ya saba raba abinci ne duk ranar juma'a... Na ɗan yi murmushi ina cewa Allah ya saka da alkairi.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now