19

21 2 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


ALMAJIRA
PAGE 19

______________________________________

Ahmad karar wayar sa ya sashi yin shiru ran shi na daɗa dagule wa, ya duba wayar yaga still Mummy ce, ita in ta fara kiran waya shikenan ta dunga kenan, ita ce dama take ta kiran sa akan lafiya taga yayi kwana biyi bai dawo ba, sannan ta faɗa masa cewa idan har bai dawo yau ba to zai gansu a kaduna gobe, ko a ina suke zasu nemo sa, Dole ta sa yau zai kama hanyar Abuja da daddaren nan.

Ya ce,"Baffah Iyaye na suna son gani na, yan zun nan zan kama hanya, amma bayan kwana biyu zan dawo ko da kuwa an sallame ku zan same ku a gida...ya tsagaita. ya ɗaga kai yana min wani irin kallo alamar bai son tafiya amma babu yan da zai yi.

Bugun zuciya ta sai ya tsananta kasancewar jin Ahmad zai tafi ban san dalili ba amma sai na tsinci kai na da kunci, yana ta magana da Baffah kamar ɗa da uba sai kwantar musu da hankali yake yi, suma kuma naga suna jimamin tafiyar na sa.

Ya tashi tsaye ya kura min idanuwan sa duk da fara'ar fuskar shi amma sai da kunci ya bayyana, da kyar ya iya motsa bakin sa ya furta kalmomi kaɗan.

"Khadija ga Baffah da Anna ki kula da su kamar yadda kika saba tun kafin na shigo rayuwar ku"

Har ya kai bakin kofa sai ya juyo ya min murmushi sannan ya ce,"Kimin alkawarin zaki kula min da kanki har na dawo"

Wallahi kunya ta hanani kallon sa wannan karan sai na ɓuya a bayan Anna ya gama kallon da yake min sannan ya wuce, ko amsa ban bashi ba.

Ranar kamar ɗaukewar ruwan sama ɗiɓ haka muka kwana shiru babu mai cewa kowa kala har muka wayi gari da safe.
Satin mu biyu a asibiti, muna ta walwala, Anna taji sauki ta murmure tayi haske, to kullin sai na haɗa mata shayi a kalla sau uku a rana, sa'annan ga breadi, kifin gwangwani, biscuit, cake da su chocolate, kayan shayi kam ba a magana saboda idan kuka gansu sai kun razana, ga maltina katan uku ya siya, da waɗan sh abubuwan da bamu san su ba, hatta kayan abinci dangin su shinkafa taliya, indomie, macaroni, da cous cous, manja, man gyaɗa da maggi duk ya siya da kan sa ya kai mana gida, zuwa nayi kawai naga kayan abinci a cikin ɗaki.

Baffah da Anna albarka kawai suke sanya mishi, Anna alhamdulillah ta samu lafiya kullin ni ke kwana da ita, Baffah na komawa gida shi da Sofia domin kuwa ita ce ganin sa, Sofia yarinya ce mara surutu da magana, amma tana yi da Baffah sosai take nuna masa hanya da zaran ya ɗaura ta saman kansa haka zasu hau napep su sauka suyi ta tafiya suna hira har suje gida.

Mun tashi da safe muna ta haramar haɗa kayyayakin mu domin an sallame mu, Anna ta ji sauki garau, sumul, muna zaune muna karya wa Anna na shan shayi ni kuma na gama ina ɗauraye kofuna a ban ɗakin cikin ward ɗin, ji nayi kawai an turo kofar shigowa da karfi, nayi sauri na fita ina cewa Anna lafiya karar miye naji haka?

Tsayawa nayi cak ganin mutane sanye cikin bakaken kaya sai matar nan ta ranar wacce tai min kama da Anna, gefen ta wani kyakkyawan saurayi ne matashi fari, siriri kuma dogo da alama ba wani shekaru yake da shi ba, ba zai wuce 26 27 ba, ya juya bayan sa hannayen sa sanye cikin aljihun wandon sa.

Matar ta tako har in da Anna take ta kama hannun Anna tana shu'umin murmushi.

Anna ji tayi an kama mata hannu a raza ne ta ke amma sai ta dake, sarai ta gane ko wacece amma sai tayi shiru dama tana gudun faruwar hakan shi yasa tun jiya ta so su koma gida gashi har ta kara ritsa su a asibitin.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now