06

33 2 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo
PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
06

______________________________________

Duk da Anna bata ganin mu ina kallon fuskar ta, tana facing in da muke naga ta zubar da kwalla tana sharewa, ta tuna shekarun baya ɗata rasa wani abu wanda tafi so duk faɗin duniyar nan Ɗan ta kwalli ɗaya ko zata sake ganin sa Allah kaɗai masani.

Ta dafa kafaɗa na ta ce Hadiza ki kwantar da hankalin ki Allah na tare da ke, duk wata wahala da kika sha da sannu zaki ga haske a cikin rayuwar ki.

Na ɗan matse hawayen da ya zubo min ina daɗa jin ciwo, mara na yana murɗa min cikin dauriya na ɗaga kai nai musu murmushi " daga bisani na koma gefe na kurɓi maganin masu ciki ina daɗa kiran sunan Allah....Yau ma anan muka kwana, kuma cikin Ikon Allah ciwon maran ya lafa sai rikewan baya time to time.

Kamar kullin muna zaune a wajan muke kwana mu tashi sai dai idan zamuyi bara ne sai mu ɗan fito bakin titi mu zauna.

Da yamma Anna ta ce mu haɗa kayan mu zata tafi damu....Alhamdulillahi murna kaman zai kashe ni tsabagen jin dadi, abin yana burge ni inga mutane a cikin gidajen su suna rayuwa, ko dan ni ban taso na ganni killace a cikin gida ba.

Da magriba muka isa gidan Anna ta karɓi kullin kayan dake hannu na tana cewa "Yaki nan Hadiza ku shigo ciki akwai sanyi" sakamakon ruwan saman da aka yini tun safe ana yi"

Godiya har kasa nayi wa mahalicci na, nayi sallan magriba ina ma Anna da Baffah addu'a, nayi sallan isha'i ina daɗa kara musu godiya, suna ta cemin sun ji ba sai na ta godiya ba, sun yimin don Allah ne.

Baa zan ce ban huta ba, har ga Allah mun samu wajan kwana kuma wanda ya baka wajan kwana ko da kuwa ace bai ɗauke maka ci da sha ba to fa ana wa tunanin ya gama maka komai, ballan tana ma Anna da Baffah suna bamu abinci, hakan bai hana mu fita bara ba.

Kwanan mu ashirin da biyar amma babu lungu da sakon wajan bara da ban sani ba a kawo, ni ce dai har wata unguwa wai unguwar dosa, bana tafiya da Sofia kullin tana wajan Anna tare suke zaunen su waje ɗaya, so tari suna riga ni dawo wa gida idan sun jira sun ga ban dawo da wuri ba, wani lokacin kuma na kan dawo da wuri na musu jagora har gida kuma a hakan zan siya mana kayan abinci a kuɗin dana samu kai har nama da kifi siya muke yi, nai mana farfesu sosai ni da Sofia muka mai da Anna da Baffah tamkar iyayen da suka tsugunna suka haife mu....Tabbas rayuwar ta canja don har fatar jikin mu ya canja saboda wahalar da muka sha a baya yanzu bama shan ta.

A wani taɗi da muke da Anna tana cewa Lallai haɗuwar su da mu alkhairi ne, saboda Allah ya buɗe musu kofofin samu ta hanyoyi daban daban idan sun ga dama ma sai suyi sati basu fita bara ba saboda baffah na siyan kayan abinci daidai gwargwado suna da kayan abinci kuma akwai kuɗin siyan kayan miya, tun da wallahi a sana'ar bara baza muce bama samu ba, idan ko muka ce bama samu to bamu da godiyan ubangiji"

Wata rana naje bara nice har gaba da badarawa ina yawon bara, Malali yayin da naga an tashi daga wata makaranta yaran suna fitowa abin gwanin ban sha'awa.

Na ɗaga kai na ina karewa gate na makarantar kallo an rubuta FGC Malali kaduna, sai dai ni kuma ban iya karatun ba duk da an rubuta wani abu a kasa, na haɗiye yawun daya tsaya min a magogwaro ina daɗa kwaɗaituwa da son ilimi...Na koma gefe na karaci bara na, misalin karfe uku na hau mashin aka sauke ni a kofar gidan mu sai da na fara siyan sabulu da klin kafin na karasa gida... babu kowa kasancewar su Anna sun fita bara, na tuɓe kayan jiki na nayi wanka na canja kaya, na kwaso kayan wankin mu baki ɗaya har da nasu Baffah na dama mun tari ruwan sama, da shi na zauna na yi wankin tas na gama na shanya su misalin karfe biyar na ɗauro alwala nayi sallar azahar da la'asar sannan na haɗa wuta na ɗaura mana abinci shinkafa da wake, na soya man gyaɗa, na daka barkono sannan na shiga ɗaka na zauna ina tunanin wata islamiya dana gani a hanya ta ta dawowa ina kan mashin, islamiyyan a cen  saman layin mu yake ni ko miye ma sunan oho don ba iya karatu nayi ba, hawaye ne suka gangaro kumatu na tuna baya da nayi, ina tsananin son ilimi tun tashi na.

______________________________________Abuja

Misalin karfe takwas na dare 8:00pm ranar asabar gaba ɗaya zuri'an gidan Daddy su na dinning, suna cin abinci.

Yayin da Nurain yana ta faman shiri domin kuwa washe gari za a kai shi boarding school, Mummy da Ahmad suna ta taya shi haɗa kaya, yayin da Nadiya da Kamal suna ta tsokanar sa shi kuwa kaman yayi kuka bai ɗau ka haka zai tsinci kan shi ba. Ashe dai zai yi kewar ƴan uwan nasa.

Ahmad yana haɗa kaya yana faɗa wa Mummy cewa "Mummy burin ku na fitar da matar aure ko?

Mummy tayi murmushi domin kuwa tafi kowa son ganin jikan ta, tayi saurin gyaɗa kai tana cewa "Amma kai ko zancen aure ma baka so Ahmad na rasa dalili wallahi"

"Hahhhhh to ku kwantar da hankalin ku In Sha Allah zaku ganta, Ina son zuwa zamfara gobe flight zan bi da safe In Sha Allah.

"Yin me? Daddy ya tambaya daidai lokacin da yake shigowa bedroom ɗin shima sanye da kayan baccin sa irin na manyan masu kuɗi ɗinnan...Cigaba yayi Daddy da cewa, "Me zaka yi a zamfara, am asking you?

Ya shafa suman kanshi yana daɗa kwantar dana bayan keyar, Ya sani ba zai basu amsar tambayar su ba yanzu sai dai kawai ya musu karya, ya fison yaje ya taho da ita su ganta da idanun su, yana da tabbacin Daddy da Mummy baza su hana shi abin da zuciyar sa ke so ba, beside aure ne kuma suna son yayi aure.

"Yaya Ahmad, Daddy na ta magana" yaji muryar Nadiya wacce ta katse masa tunanin sa, ya ɗaga kai yana cewa Daddy zanje na taimakawa wasu mutane ne masu tsananin neman bukatar taimako, tun zuwa na na lura dasu......" ya tsagaita daga nan.

"Daddy ya gyaɗa kai, yayi magana kasa kasa yana cewa "Kar kuma aje a ɓige da soyayya don na riga da na yanke hukuncin haɗa ka da na gida"

"Mummy ta ɗaga kai ba tayi tunanin Daddy ya amince da shawaran da ta bayar ba tun sati biyu da suka wuce, tayi murmushi saboda tabbas tana son Ahmad ɗin ta ya auri jinin ta, tun bayan nasreen take ta saka wannan lamarin a zuciyar ta burin ta kawai ya kasance gaskiya saboda Ahmad Ɗa ne wanda kowani uba ko uwa za su so samun ɗa mai irin halayen sa na biyayya, beside ita tayi tarbiyar abin ta.

Daram gaban Ahmad ya buga jin zancen Daddy, ya daure ya ce,"What Daddy auren gida kuma, wa kenan?

"Nooooooooooo don't be faster than your shadow my son, cewar Daddy "Ka bari ka dawo za muyi magana kaji, Allah dai ya tsare mana kai"

Ahmad dai al'amari ya lalace sulalewa  yayi ya zarce ɗakin sa babu abin da yake yi sai tunani kala kala, ko kaɗan ya kasa rintsawa har asubahi idanuwan sa sun gagara bacci haka ya sanya kayan jogging ɗin sa bayan ya dawo daga masjid ya tafi yayi jogging 2hrs, bakwai da rabi ya dawo ya watsa ruwa ya shirya tsaf cikin bugaggiyar shaddar sa gezner mai tsada da hula zanna, ya sanya black cover shoe da wrist watch ɗin sa black ya fito yana ta zuba kamshin turarukan sa signature *miss anna cherie*  Ko gaisawa da ƴan gidan ya kasa yi tsabagen ran shi a bace yake kuma ba zai samu sukuni ba har sai ya yi tozali da *Khadija* sunan da zuciyar sa ta aminta da ya kira Hadiza da shi.

______________________________________

ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

Madallah.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now