17

37 4 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

LAST PAGE OF FREE PAGES

PAGE 17

______________________________________

Waye kuma *SAGEER*?

Ahmad ya bukaci tambaya jin cewa wai yana kama da Sageer, don yaji maganar ta na karshe daya fito daga bakin ta tace,

"Kai haba it's a lie wallahi ya a kayi kuma naga suna kama da Ɗana *SAGEER*

Kwata kwata bata san cewa maganar ta fito fili ba, ita kawai ta faɗa kogin tunani shin waye wannan da yake tare da Anna kuma mai Kama
da Mujaheed da Sageer kamar su ma ta bace da sageer kaman ƴan biyu, ko dai Mujaheed ɗin ne ma, ta cigaba da tunani a cikin zuciyar ta.

Da Ahmady zai ɗauki Anna ya canja  mata asibiti amma sai ya gwammaci gwara ya nuna musu rashin tsoro, ya kuma gwada masu shi waye, kuma 44 ɗin za ayi mata treatment, waya kawai ya ɗauka ya kira Daddy, jim kaɗan sai ga wasu jerin sojoji na gaban su babban likita ne sanye da kakin soja amma ya sanya labcoat a sama, suka iso inda su Ahmad suke tsaye.

Kafin na girga uku, ya faɗa yana takawa zuwa inda motar sa yake, yana pito irin asalin ɗan tashan nan, duk da sauran sojojin basu san ko shiwaye ba amma suna tsoron gwamnati taji abin da suka yi idan matar nan ta sheka to wallahi zasu fuskanci kalubale babba duk da Madam ɗin su tana kokarin biyan su kuma tana kare su akan dukkan wani matsalar da zata same su.

Matar nan ta jima tsaye tana kallon shi ta kasa aiwatar da komai, Ahmad ya ja tsaki kafin ya kalli jami'an dake wajan ya ce,"Dukkan ku idan na so yanzun nan za a kama ku a kulle ku a dark room, wallahi babu ruwa na da wai ku sojoji ne dukan tsiya zan muku matukar baku ɗauki matar nan kun kai ta ɗakin taimakon gaggawa ba"

A daidai lokacin Anna ta farka don dama ta fara bacci tun muna barau dikko, tiryan tiryan haka na zayyana mata abin da ya faru sai naji Anna na cewa "kayya kayya me yasa kuka kawo ni asibiti da kun bar ni a gida, Ɗan nan baka ji ba ina magana na ce "Ku mai da ni gida don Allah"

Amma ko kaɗan Ahmad baya sauraran Anna sai da ya gama sille su da faɗa tas ya razana su kafin ya fara
kirga ɗaya, ya kirga biyu....Bai ankara ba kawai sai ganin su yayi sun kawo gado sun ɗaiki Anna cak su ka kai ta A &E anan aka bata taimakon gaggawa, Ni dai ina biye da su Ahmad yana rike da Sofia ta ɗayan hannun sa kuma ya tamke mun hannu na muna zaune a gefe ɗaya na wani gado muna kallon Anna.

Ita ma Anna tunanin mu ta keyi ta hakika yau ita rana ta farko da wani ya kwatan mata ƴancin ta a wajan muguwar matar nan, tun bayan rasuwar mahaifin ta, ta girgiza kai tana tausayin Ahmad tabbas yau ya kira ma kan sa ruwa tun da ya tsokano ta yanzu tana cen tana wani sake saken mugun ta, amma bata son wani abu ya samu ɗan mutane shiyasa tun farko taso ya saurare ta, da ya maida ita gida amma ya ki ji...tana wannan tunanin ne aka tsira mata allurar bacci har baccin ya ɗauke ta.

Suka gama mata komai Ahmad ya biya hospital bill ɗin sannan muka jira muga ya saukin nata zai kasance saboda an mata allurar bacci tana ta shan bacci abin ta.

Bayan sallan la'asar sai Ahmad ya ce min naje in da Baffah yake na taho da shi, ya bamu kiɗin Napep.

Zan tafi ya rike min hannu ya kura min idanu yana min wani irin kallo ya kunshi ma'anoni da yawa, ya sassauta murya a hankali wan da bakin shi kaɗai ne yake motsi amma baka isa kace kaji abin da ya furta ba,

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now