13

27 3 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
13

______________________________________

Ya salammm!!!!!!! Shugaban ya faɗa ya cire glashin fuskar sa ya mike tsaye yana kiran sunan Allah a bakin sa haɗe da furta sunan ɗan sa mafi soyuwa a zuciyar sa....mamaki yake shin ina Ahmad ya samu exact idea irin na Ɗan sa, abin da yake nufi shine..................

Kwakwalwar sa ce ta fara juyawa kan sa ya fara ciwo tsabagen girgiza da yayi saboda ganin Ahmad, tamkar ɗan sa na cikin sa....shin waye shi wannan ɗin?
Ko dai yana da alaqa da ni ne?
Amma nayi bincike kuma na gano Ɗan LAWAL ne wato Arc.Lawal amma me yasa yake kama da jini na?

Duk tambayoyin nan da ya keyi babu mai amsa masa, babu kuma mai fahimtar abin da yake yi, jama'an hall ɗin sun gan shi ya mike sun zata ko zanen ya burge sa ne shiyasa ya mike tsaye.....yana nan tsaye Ahmad ya gama ya dawo saman kujera mai kallon kujeran shugaban ya zauna.

Yace,"Duk wanda yake da magana yayi maganar sa"

Gaba ɗaya hall ɗin tafi kawai suke yi....lallai sun yaba da ilimin Ahmad da kuma baiwar da Allah yayi masa, ba kamar Daddy da zaune yake yana ta murmushi ji yake kamar ya tafi ya rungume Ahmad ɗin.

Shugaban ya ɗauki mice yayi magana ya tsaida ranar da turawan zasu zo su kar ɓi zanen, cikin satin nan sannan kuma ya sallami kowa....ana ta watsewa masu yaba zane suna ta yabawa ƴaƴan shugaban campanin kuma sai suka tsaya kusa da Baban nasu tabbacin suma sun hango abin da babansu ya gani, kaf ɗin su babu wanda baya tunanin shin ya akayi Ahmad ya ke yin komai irin na ɗan uwan su.

A ranar shugaban campanin I.B Worldwide ya baza masu bincike su duba masa kaf garin Abuja ko za a samu ɗan sa wan da ya jima da rasa shi da girman sa don har aure yayi......

WEEKEND

Ranar asabar Mummy da Daddy suna ta faman shirye shiryen visiting ɗin Nurain, Daddy ya sa masu aiki suka yanka rago aka soya masa rabi, rabi kuma akai masa jar miya, sannan aka yanka kaji biyar akai masa farfesu da biyu uku kuma aka masa paper chicken duk a daren Mummy tai ta ɗawainiya har da yima shalele chin chin da ring fluffy doughnut da cupcake saboda dama ta ɗauko caterers masu yin kayan snacks, karfe sha ɗaya sha biyu ana abu ɗaya daga karshe sai da Mummy taga an ci rabi da kwatan aikin kafin taje ta kwanta ita da Nadiya.

Duk dama su baza suje ba, Ahmad ne ya ce shi kaɗai zai kai masa kowa yayi zaman sa ya huta tun da wancen zuwan kowa yaje.

Ranar Sunday

Washe gari suna tashi, karfe takwas daidai Mummy ta gama haɗa komai har abinci ta masa kala uku, motoci biyu ɗaya na Yaya Ahmad ta bayan kuma a ciki aka haɗa masa provision da komai da komai.

Ahmad shi da Josiah a mota ta gaba sai driver da yake tuka motar bayan su...suka kama hanyar kaduna.

______________________________________

Daddy na zaune tare da iyalan sa, Mummy, Nadiya, Ahmad kam yana kaduna sun gama waya da Mummy ta ji ko ya isa lafiya.

Suna zaune gaba ɗayan su suna hutawa sai mai aikin su wanda suke aiken ta idan bukatar hakan ta taso, suna zaune a filin shakatawa suna shan kayan marmari da kayan makulashe  suna ta wasa da dariya, Daddy na basu labarin years back shi  da wani abokin sa Ibrahim lokacin da suke karatu a BUK ƴan mata na bin su tsabagen kokari da ilimi da kuma baiwar da Allah yayi wa Ibrahim wato abokin Daddy kenan.

Mummy ta tura baki irin kishin ta ya motsa ɗinnan, Nadiya kuma ta kwashe da dariya tana cewa,"Eheen  Daddy akwai abin da nake son faɗa maka dama"

"Yes ina sauraron ki ƴar Daddy faɗi damuwar ki ni kuma in share miki hawaye"

Nadiya tayi dariya tana cewa "I knew it, I'll always be your favourite daughter Daddy" ta faɗa tana ɗan dariya

Daddy ya ce,"Yes yea and no one can come between me and my favourite daughter"

Nadiya ta sake lumewa a cinyar Mummy tana murna ta ce,"Daddy akwai wani matashin saurayi da yake so na yana london a cen yayi karatu kuma yake aiki infact yana zaune da iyayan sa ma a london amma state of origin ɗin su Nigeria ne, Daddy wallahi dana gan shi so ɗaya naga yana kama da Yayaa Ahmad fa, like twin brother"

Daddy yana kishingiɗe ne bai san lokacin da ya taso ya zauna daram da ɗuwawun sa ba yana cewa "Ehnnnnn me kika ce ƴar Daddy"

"Daddy kamannin su ya baci dana Yaya Ahmad nima ban gane ba kawa ta Surayya ita tai ta faɗa min cewa yana kama da Yaya na, ban  ɗauki maganar da muhimman ci ba kuma tunanin hakan bai zo min ba sai bayan da kuka faɗa cewa ba ku bane asalin iyayan sa....ta cigaba da cewa "May be kuma kamanni ne kawai"

"Tohh Allah kaɗai ya san ɓoyayyan al'amarin daya ɓoye, dama mun san ƴan uwan Ahmad ɗin ne da sai muyi masa magana zamu bincika saurayin muji"

Mummy tace,"Uhm ni kam zan so Ahmad ya gana da iyayen sa na gaskiya amma ba zan so ya bar mu ba saboda soyayyar da nake masa ya wuce abin faɗi a baki" "Ni kam Daddy don Allah kar na sake jin wata maganar wai bamu ne iyayen Ahmad ba, a rufe maganar idan Allah yayi zai haɗu da mahaifan sa to, idan kuma Allah bai yi ba shikenan tun da yana da mu a rayuwa me ya rasa? Mummy ta faɗa.

Daddy ya buɗe baki kenan zai yi magana sai wani ma'aikaci ya zo yana sanar da su cewa sun yi baki, duk da Daddy bai san su waye ba sai ya ce,"Kai musu iso zuwa bangaren baki.

Ina ALMAJIRAN MU?
______________________________________
KADUNA

Ranar lahadi zani makarantar islamiyya misalin karfe bakwai da rabi mun gama cin abinci da komai ma har wanke wanke sai da nayi muka fito tare da su Anna su zasu wajan bara ni kuma zani makaranta.

Kasancewar ba hanyar mu ɗaya ba sai suka sha kwana ni kuma na mike hanyar unguwar dosa kenan ina takawa a hankali har na isa makaranta.

Karfe goma muka tashi lokacin tara kowa ya fita don zuwa shakatawa daga masu zuwa gida sai masu zuwa yawo...hakanan na tsinci kai na da zuwa wannan makarantar bokon duk da ban sani ba ko yau akwai mutane ina sha'awar inga ɗalibai suna sanye cikin kayan makaranta abin burgeni yake yi, ban tashi sanin nayi nisa da barin makarantar islamiyya ba sai da na ganni a kofar makarantar bokon, motocin masu kuɗi manya manya sune suke ta shiga ta babban kofar makarantar, ɗalibai na hango daga ciki suna ta jin daɗi wasu suna tsallen ganin ƴan uwan su da iyayen su anan na gane ashe makarantar akwai na kwana ma na samu gu na zauna ina ta kare ma ɗaliban kallo ina ji a zuciya ta ina ma nima hakan ta kasan ce dani.

************************************
Too short so sorry na gaji da typing ne and bana so na karya alkawari yau nace zan yi update.

Much love my fans

______________________________________

ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now