PROLOGUE ( TEASER)

100 7 0
                                    

NISFU DEENIY.......!

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

ELEGANT ONLINE WRITERS (E.O.W)

Ga sabon labari ga maabota bibiyar littafaina, wainda suke bibiye dani tun daga WASU DANGIN, WANI RABON toh an fa riga ya an samu rabon har ta yi masa lak'abi da cikon rayuwarta kuma Rabin Addininta....Nisfu Deeniy labarine akan wata zuria mai girma da tushe wacce ta ke gab da rasa zumuncin da aka dad'e ana yi sakamakon kuskuren y'ay'ansu sai dai kuma hakan bai faru ba saboda tubalin da aka gina zuriyar tafi k'arfin turewa. Amma still sai da suka fuskanci k'alubale sakamakon laifin d'an su ga 'yar lelen su.....

Me labarin ya k'unsa?!
Kuna son sani?

Toh ku kwantar da hankalinku don nesa ta zo kusa domin ko in rabbi ya ara mana numfashi nan da bayan sallah zamu sanya d'amba a tafiya zuwa Yerwa domin binciko wannan sirri.

Tuna da sunan NISFU DEENIY......!!!❤

Dedication

This whole book is dedicated to all Kanuris out there....been one of you is the most beautiful gift ever. I love the fact that I'm blessed to be one of you and I'll proudly shout it to the whole world.......Kanuri to the world.

This whole work is with love Ayusha Adam ( Ayshacool) soyayyarki gareni ta daban ce Allah ya k'ara girma da arziki ❤

Forward
In the name of Allah the most beneficent the merciful may the peace and blessing of Allah be with his most beloved messenger prophet Muhammad SAW his family and his companions and his saints and those that follows his path until the eternal road end.

Allah ka bamu ikon ganin dai dai mu bita ka kuma rabauta mu da ganin akasin hakan mu guje mata. Allah kasa mu sak'a Alkhairi ka rabemu da sharri a koina, a kowani hali.

Allahumma inna nas'alukar ridhaka, wa ridha nabiyuka, wa ridhal ashyaku wa ridhal walidin....

Allahuma j'al ma nuhibbu fima tuhibbu wa tarda....Allahuma j'al fi ikhtiyarina ikktiyari ka wala taj'al illa ilaika id'd'irarina.

Ya rabbana ya khaliqul awalim...kul bainana wa kulli zaleem.

Wajzi li kulli man ilaina ahsan wa jazihi anna zaahal ahsan...bil mustafal shafi'i yaumil mahshari khairil waraa man qad hubi bil Khausari...
Wal jam'a liy fil husnaa....wal katma liy fil husnaa.❤
Wala haula wala quwatti illa billah.

Author's note :

All the characters places ideas and events mentioned in this book are purely fiction and does not relate to any living or dead
All the story setting and other elements are nothing but imaginations and fictional any resemblance to any person's life is coincidence.

©deejasmah 2023❤🌹

PROLOGUE

Gyara zama yayi yana nazartar kalamanta a hankali. Sake tambayarta yayi " lele, kin amince in miki zab'i?,". Kai ta gyad'a kafin cikin voice d'in ta mai taushi tace.

"Na'am Baba na amince da kowa apart from him ". Hararta Abbu yayi yana mai jin tamkar ya tokare ta ta wuntsula. Wai shin ita ce aka tab'awa laifi da ba zata iya yafewa ba?, ina hak'urin da kowa ya shaide ta da shi?. K'wata yayi a hankali ya na mai sauraron Yayan nasu.

Murmushin girma yayi kafin yace " ki kwantar da hankalin ki lele, zan miki zab'in da zakiyi alfahari da shi". A take gabanta ya yanke ya fad'i sai dai kuma ta na k'arfafan kanta da ta daure, ta nuna masa muhimmancinta da martabar ta. Tafi gaban wacce ya keta a baya, ko zata samu tagomashin motsa kambunta a kan sa. Kwatsam ta jiyo muryan Baban ya na cewa.

" Na zab'a miki Farhan a matsayin mijin da zaki aura and I'm very sure ba zaki k'i zab'in da nayi miki ba....." D'ifff duka parlorn ya d'auke tamkar anyi ruwa an d'auke. D'agowa tayi tana mai jin girman furucin na shi.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now