NISFU DEENIY 32 (BROKEN)

58 6 2
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 32 (Broken).

Nan idanu suka mata caaa kamar ita d'aya ce mutum a hall d'in yayinda k'ananun maganganu suka fara tashi, Suleim dake gefenta ne ta rik'e mata hannu ganin yanda jikinta yake rawa sosai. Wani d'aci take ji a kan harshenta tare da wani mugun haushi da tsanar Islaam, Idan ma auren zai yi ai ba sai ya biyo ta wannan sigar ba can't he just go to Baba su yi magana a gida?.

Ita ko Umma mik'ewa tayi tana tafiya tana cewa " ai kya ce kin amince mana saboda I'm sure ba ki san abinda ke miki ciwo ba, dubeni nan Nadeefah ko kin amince ni ban amince ba" ta rik'eta itama a lokacin da ta k'araso.

"Toh Sato ba gwara ta amince ba da wannan tijara da yake janyo mata? Wannan ma dan ba ki san kalar rashin mutuncin da yayi mata ba ne a gida" in ji Abba a harzuk'e.

Lumshe idanu tayi tana lallasar zuciyarta da kuma idanunta kar su ba da ita, don ta tabbatar ta sake tayi kuka yau toh akwai matsala. Cikin dauriyar tace " Umma kace-nace d'in nan ne bai da wani alfanu, musamman akan abinda halal ne hanawar kuma sab'o ne babba so I'm begging you all ku kawo k'arshen maganar nan a je a nema masa aure don Allah!".


"Ni ma ina rok'onku please kar ku hana Islaam yin aure don in aka masa haka an shiga hak'kinshi" Ummu ta furta cikin son shanye damuwarta sosai.

Maganar da ta fad'i ne ya k'ara sa d'akin ya d'auki zafi side talks d'in da ake yi kuma suka koma hayaniya don ba ma ka jin abinda ake fad'i ko kad'an, kai kuma ya rabe gida biyu don daga Abbu, Baba Tijjani sai Daddy ne kawai suka goyi bayan yin aurenshi sauran kuma yara da manya kowa yana nuna ba sa tare da shi su kuma matan auren suna gudun kar ya zama silar fara musu kishiya a na zaman lafiya.

Hajjah ne ta dubi su YaMara da kamar 'yan d'akin sun manta da zamansu a wurin tace " a k'yale shi mana yayi aurenshi, wannan ai ba wani abun hayaniya ba ne".

"A k'yale waye Ya Hajjah? Ai bai isa yayi wani aure ba in ya ga dama kar ya hak'ura" fad'in YaMara tana huci kamar ita za a yi wa.

Ya Madari ce tace" Aa wannan rashin adalci ne bayyananna, kuma k'in yin auren matsala ne mai girma don tunda ya dage in aka hana shi ya na iya shiga wani yanayin da zai iya saka mu dana sani gabad'aya".

"Ni ma abinda nake hanga kenan, maimakon nuna k'iyayyarmu ga lamarin me zai hana mu yi adduar mafi alkhairi a auren da zai yi".


"Babu fa wani alkhairi a auren nan, kuma har abada ni dai ba zan amince da wata mace a gidan Islaam ba bayan Nadeefah me yarinyar nan ta mai da zafi ne har haka da ba zai iya zama da ita ba? Haba Hajjah kowa fa ya san hak'uri take na zama da shi ko cikin saointa da suka yi aure rana guda ban tunanin akwai mai rabin hak'urin da baiwar Allahn nan take yi sai a bar shi ya auro wata ya zo yana had'uwa da ita ya cusguna mata su kashe mana ita?".

"Ai shi aure d'an hak'uri ne in dai ta daure ta shanye sai ki ga Allah ya dubi sadaukarwarta ya mata zab'i mafi alkhairi sai ma ki ga auren ya sa shi ya fara kyautata matan da kuke ganin bai yi".


"Sosai kuwa, don Allah mu had'u mu k'arfafa musu guiwa dukansu namu ne ba wanda ya fi wani. Kar kuma mu sa son zuciyarmu sai Allah yayi fushi da mu" in ji Ya Madari, had'uwa suka yi da Hajjah suna ta tausarta har tace "Allah ya sanya alkhairi" ba dan tana so ba don kawai ba ta da yanda za ta yi da su.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now