CHAPTER 10 ( SHE'S BACK)

14 3 2
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 10 ( She's back!)

Runtse idanu yayi yana mai jin damuwa yayi mai yawa, Abba ne yazo ya amshi Hajjah a hannun shi yana cewa " I've told you in wani abu ya sameta sai nayi sharia da kai,,,,,now ka fita ka nemo min ita" ya k'arashe a tsawace. Mommy Kuura tace " Yaa abi a hankali dan Allah in ya fita yanzu ina zai fara nemanta?".




Cewa yayi " duk inda zai shiga ya shiga damuwarshi ce ai shi ya san inda ya ajiye ta". Daga haka ya wuce da Hajjah da duk ta susuce hankalinta ya tashi, su Zulfaa ma anci kuka ita da Suliem idanun nan luhu-luhu. Musamman ma Suliem ta kira number yafi sau adadi amma baa picking, har ta kai ga ta daina shiga ma saboda yawan kiran da ake ta mata. Ga kiran da Elsadeeq yake ta jero mata ta kasa picking, don bata a nutsuwar da zata iya d'aukar wayar har message ya turo yana tambayarta ko yayi laifi ne ko dubawa ba tayi ba ta notification bar ta ga message d'in.


D'an saita kan shi yayi yana komawa motar shi, Farhan ne ya biyo shi motar ya shiga d'ayan side d'in. Yana zama yaji ya zauna akan abu, hannu ya sa a inda ya zaunan wayar Lele ce da take jone a jikin power bank d'in ta. Yayinda misscalls rututu sukai masa sallama, kallon Islaam da yake sharara gudu har sun kai gate d'in fita daga estate d'in yace " Dude ina ka baro ta ne wai? ba zan tambaye ka dalilinka ba don nasan baka abu sai da solid reason but babu wani hujja a duniyar nan that can justify what you just did".



Yawu ya had'iye yana mai sak'a abubuwa a ran shi cewa kawai yayi " ba zata b'ace ba, ba kuma abinda zai faru da ita In shaa Allah " ajiyar zuciya ya sauke kawai yana kallon hanyar da suke bi, ganin kamar bai san inda za shi bane ya sanya shi cewa " mu je muyi reporting a PS kawai ".

Har zai yi gardama don ya san definitely shi zasu yi blaming, and he's not ready for their tantrums sai kuma yace " ok " kawai yana karya mota tuni nearest PS. Ko da suka je can d'in abunda ya gudan ne ko ya faru, rufe shi sukayi da fad'a bai ko kalli inda suke ba takaici ya sa DPO cewa " ba zamu sake ka ba, we'll press charges against you saboda kai ne no. 1 suspect d'in mu".

Kallon banza ya bisu da shi arrogantly yace" ni zaku rufe or who?". D'an dafa shi Farhan yayi a hankali yace " Dude please". Kana ya juya ga DPOn yana cewa " Ba ma sai an kai nan ba yallab'ai shine fa wanda zai aureta kuma ko babu aure k'anwar shi ce kaga babu ta inda zai salwantar da rayuwarta y'ar rashin fahimta ce aka samu ba komai ba".

DPO yace " tunda shi zai aureta kuma abune na gida toh ina ganin babu buk'atar mu shiga cikin abun sai ku magance matsalar in-house zai fi, Allah ya bayyanata you can excuse us zamu fita duty". K'ask'antacce kallo ya bishi dashi yana shirin magana Farhan yayi saurin cewa " ba haka bane y'allab'ai consider us please, the life of our sister is at risk".


Cewa yayi " ai naga baku buk'atar sa hannunmu a ciki". A gaggauce yace " no sir, ba haka bane kawai dai kamawar da kace ne yayi nauyi" tsaki yayi yana tashi daga kujerar sosai ran shi ke b'aci, ji yanda Farhan yake zubar musu da mutunci har haka. The way he's begging this low ranked officer kamar basu ke da manyan officers na k'asar ba one call kawai ya wadatar duk inda take sai an nemo ta, amma ba zasu yi haka ba sai in abun yaci tura.

DPO yace " in dai har zamu saka hannu a lamarin nan then he must be arrested ASAP saboda babu yanda zaayi mu k'yale suspect a cikin case ya tafi scotfree until he's proved innocent amma ni I'm doing this grace na k'yale ku ku tafi not because ina tsoron wani abu da zai faru but saboda naga darajarku tafi gaban hakan but my condition stands in kaga na shiga case d'in nan toh an kama shi ne" tun kafin ya kai k'arshe a maganar shi har ya nufi k'ofa.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now