CHAPTER 9 ( THE RIDE)

18 2 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 9 (The ride....!)

Da sauri ta waigo  yana a yanda yake ko motsi bai yi ba, kamar ma bashi yayi maganar ba. Ta gaji sosai ba kuma ta da energyn yin magana a halinda take ciki, dan haka ta juya da nufin barin d'akin " tabbacin zaki aure ni bai isheki bane har sai kin cusa kan ki gareni, don't tell me tun yanda you are trying to seduce me?".



Cak ta tsaya bata yi gaba ba, ba kuma tayi baya ba. Yanzu kam ta yarda bai sonta in ba k'iyayya ba ya d'anuwanka zai dinga jifarka da muguwar kalma kamar bai san daga inda ka fito ba. A take jikinta ya fara rawa tana jin kamar guyawunta ba zasu iya d'aukan nauyinta ba, hannunta ta sanya tana dafe cikinta a hankali tana addua.


Jin motsin shi a bayanta ya sanya ta waigo ta na mai fuskantar shi, tsaye yake a bayanta gab hakan ne ma ya sanya ta d'an matsawa baya. Biyota yayi sai da suka kai jikin k'ofar kafin ya dakata cikin husky voice d'in shi yace " I've been warning you to stay off my lane amma na fuskanci kunnen k'ashi kikeda, well ba zan kuma kuma warning d'in ki ba cos it is quite time you start paying for your recklessness".


Matsar da fuskarta take k'ok'arin yi don yanda ya matsota ya fara wuce k'aida hatta da numfashin shi a fuskarta yake sauka and it's making her feel unease, bata da ko kalma d'aya da zata gaya mai don harshenta yayi nauyi kuma bata da yawu. Lura da yanda take mar-mar da idanu yasa shi ware idanu, ba dai yarinyar nan tana tunanin banzanta bane. Kallon yanayin su yayi ai da sauri ya matsa yana mai istigfari a zuciyar shi.


Spitting yayi kafin yace " and ki daina yaudarar kan ki da tunanin you have anything da zai iya sani falling miki, Kaduna ko? To kizo mu tafi amma duk abinda ya biyo baya then you have yourself to blame,,,,,,,,excuse me!". Daga haka ya juya ya barta a wurin cikeda jin haushin yanda tayi mai banza yana ta zuba, so yayi ta tanka ya gaggaya mata maganar da da kanta zata fasa bin shi. But sai ta manna masa hauka which ya sanya kalamai da yawa guduwa daga kan shi, tsaki yayi ya wuce cikin bedroom d'in yana banging k'ofa.


Jin buga k'ofar shi ya sata ajiyar zuciya, wannan lukutar masifa har ina. Tana hankalce da shi yana son jin ta bakinta ne ba kuma zata bashi abinda yake son ba kuwa, tayi alk'awarin in dai suka rabu ba zata sake bayyana kanta a gaban shi ba har sai randa aka kaita gidan shi, in ya so in kasheta zai yi yayi juyawa tayi ta koma inda ta fito.

Ko da dare k'in zuwa kai masa abincin tayi sai maids suka kai masa, suka fito da na rana bai ko tab'a ba. Hasalima ba ya gidan ya fita bin titi, ana gama cin abincin ma ta gudu part d'in su wai bacci take ji.

Haka tayi ta wasan b'oyo da shi, duk wata inuwar da ta san zata iya had'a su bata bi. Da safen k'in tashi tayi wai tana azumi, sai da ya bar gidan kafin ta iya fitowa d'aurewa tayi da azuminta ta wuce office don ya fi mata komai musamman da gobe Sunday zasu wuce garin gwamna.

Ta riga ta had'a jakarta tsaf dama ba wasu kaya tazo da su ba, ba ma dasu zata koma ba wasu ta d'auka da 'yan abubuwan buk'ata.

Kasancewar yau d'in sai da ya shiga cikin gari ya sanya basu taso da wuri kamar yanda ya so d'in ba, sai 2 kafin ya fito. Parlorn ya shiga Ummu yayi ma sallama don ita kad'ai ya tarda, ya riga yayi sallama da Abby da ya fita tarar ambassadors da suka iso daga Santiago. Sama ta haura inda ta tarda Lelen tana bacci kamar ba yau zasu tafi ba, d'an bubbuga mata pillow tayi ta bud'e idanun da suke cike da bacci.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now