CHAPTER 4 ( HOW I WISH....)

21 2 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love story )

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER FOUR ( HOW I WISH...)

Kasancewar ta kwanta da wuri ya sanya tana asuba ta kasa komawa bacci, zaman lazimi tayi da ta idar kuma tayi tilawa san da ta kammala har 6 tayi ruwan d'umi da zuma ta sha kafin  ta shirya cikin wata farar top da ash d'in track suit, bak'in joggers ta sanya tana tufke gashinta ta rufe shi cikin bak'ar hula. Jogging take son fita don saurin gajiyar nan da take yi tasan ba komai bane face rashin motsa jikin da ta kwana biyu bata yi ba, har nauyi-nauyi takejin jikinta na mata.

Fitowa tayi zuwa room d'in Hajjah a dadduma ta tarda ta, zama tayi gabanta cikin sanyin murya tana gaisheta da ka amsa mata ba tare da ta bud'e baki ba. Sanin in tana lazumi bata son magana ya sanyata nufar k'ofa tana ce mata ta fita motsa jiki, tana fita ta ciro iPod d'in ta ta mak'ala a kunne tana sanya wak'a a wayarta ruwa mara sanyi ta d'auka a kitchen kafin ta fita.

Tun daga gate ta fara jogging taje farkon street d'in ta dawo zuwa k'arshe, ta sake komawa farko daga nan kuma ta mik'i main titi kamar zata fita daga estate d'in. A hanya tana ta had'uwa da d'aid'aikun 'yan familyn da suma suke fitowa motsa jiki, gaisawa sukeyi kowa ya cigaba da abunda ya fito bata had'u da su Suleim da Zulfaa ba saboda su d'in basa fita motsa jiki har sukan tsokaneta da cewa wai ita d'in da bata da kauri ne take fita motsa jiki to me take son ragewa bata kula su don tasan amfanin motsa jiki ba sai ga mai k'iba ba Aa kowa ma yana da kyau ya dinga koda 15 minutes walk ne saboda ayi maintaining homeostasis.

A dai-dai Yerwa court ta hango su sanye da armless shirts da dogayen wanduna, basketball suke bugawa cikeda k'warewa yayinda kowannensu ya jik'e jargab da zuwa su uku ne Farhaan Aliyu Yerwa, ElSadeeq Yusuf Yerwa sai kuma Burhaan Abdullah Yerwa wainda suke kusan kai d'aya duk cikinsu Burhaan ne babba don ya girmewa ElSadeeq da kusan 5 months while ElSadeeq d'in ya bawa Farhaan 3 months Sannan ElSadeeq d'in ya fisu haske sosai while Burhaan is bit tall and well built than them.

Tsayawa tayi ta na kallonsu a zahiri a bad'ini kuma Burhaan take kallo yayinda har k'asan ranta son shi yake d'ad'a hank'oro da hauhawa, a jikinshi yaji ana kallonshi waigowa yayi yaganta tsaki yaja a zuciyarshi a zahiri kuma cira idanunshi yayi yana k'wace k'wallon daga hannun Farhaan cike da zafin nama ya daka tsalle yana cilla k'wallon a kwando.

Gwalo yayi musu yana d'aga hannunshi alamar ''I gat it", yanda yayin kuwa ya k'ara masa kyau a idanunta he looks so adorable kamar ta sace shi. Yippee ta furta da k'arfi ba tareda ta sani ba hakan nee ya ankarar da su Farhaan d'in isowarta wurin, waigowa sukayi a tare banda Burhaan.

Farhaan ne yace " wai ke har yanzu baki hak'ura da motsa jiki ba ko?, can't you see that you are  getting slimmer as days goes by?" Ya k'arashe yana isowa gabanta ya rik'e siririn hannunta dake nan as soft as a baby's, k'wace hannun tayi a shagwab'e tace " I'm not complaining ai " ta k'arashe da murgud'a baki.

Harararta yayi yana cewa " why will you complain?, ko fa kinyi ba riba dole kiyi hak'uri ba k'ibar zakiyi ba". Turo baki tayi tace " oho dai a hakan ake gani a rikice kuma ba samu zaayi ba, I know what's paining you sorry ehn", juyawa tayi tana gaishe su duk suka amsa da sakin fuska banda Burhaan.

Yayinda shikuma Farhaan ya cigaba da tsokanarshi yace " ai kema kin sani yarinya,,,,yawwa Lele zo kiji! Guys ina zuwa" Ya k'arashe maganar yana  fitowa yayi daga court d'in, a d'an tsorace ta sa k'afa zata gudu tunaninta ko wayo zai mata. Cafko hannunta yayi yana cewa " ke matsoraciya, magana fa zamuyi ", ajiyar zuciya ta sauke tana tsayawa har tayi k'ok'arin zame hannunta sai dai waigawar da tayi taga dukansu kallonta sukeyi ne yasa ta k'yaleshi don so take shi ma Burhaan d'in yaji kishi.

NISFU DEENIY.......!Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ