CHAPTER 15 ( HONEYMOON)

25 2 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 15 ( Honeymoon).

"Beautiful nonsense " shi ne kalmar da ya jefeta dashi yana k'wata, ruwanshi ya shanye yayi jifa da gorar kafin ya nufi d'akinshi. Wanka yayi ya fito yana kallon time, ganin da d'an sauran lokaci kafin magrib ya sanya shi zama a gaban mirrorn. Dangwale-dangwale ya din ga yi, ya mittsikka wancan ya goga wancan. Sai da ya gama kafin ya nufi gadon da towel d'in jikinshi ya kwanta ba bacci yayi ba, dogon tunani ya tafi na rayuwa.

Kiran sallah ne ya katse mai tunanin da ya keyi, toilet ya koma ya d'auro alwala kafin ya fito ya shirya cikin jallabiya. Turare ya fesa ya fita daga d'akin zuwa masallaci.


Masalllacin a nan farkon street d'in su yake, kusan 'yan familyn ne suka cika masallacin sai na d'aid'aikun mutanen da suke zaune a unguwar. Duk da gidajen layout d'in yawanci mallakin 'yan Yerwa ne but kasancewarta sabuwar unguwa ya sanya suka sai da filaye da yawa ga sauran jama'a bayan an cirewa duka mazan filin da zasuyi gini in sun tashi aure kuma har yanzu suna kan siyarwa don unguwar babba ce sosai duk da bata kai Yerwa estate girma ba shi ma ba isu-isu bane akwai wasu jama'ar da aka zama kamar 'yan uwa.

Basu baro masallacin ba sai bayan ishai, bayan fitowarsu sun jima a tsaye suna tsokanar junansu shi da su Farhaan. In da suka d'an gaisa da yayyinsu da suma sun zo masallacin kafin su rankayo zuwa gida, suna tafe suna cigaba da hira tsayawa sukayi wurin mai tsiren dake gaban masjid d'in kad'an Farhaan ya siya musu kowa leda d'aya kafin suka wuce zuwa gida.

Na shi part d'in ya shige sai da yayi al'adar rayuwarshi kafin ya kwanta bacci, yau ma dai tunanin Suliem ya hanashi runtsawa sai da ya had'a da istigfari kafin baccin ya d'aukeshi a wahale cike da sak'e-sak'e.

Ita ma dai yau da sak'e-sak'en ta kwana, a jiya ba ta da damuwa gani take kamar hak'arta ya kusa cimma ruwa. Amma a yau reality ya sark'afe ta, ta wartaske daga tunanin da anyi aure shikenan. Ta gane ashe da sauran rina a kaba, da kuma buk'atar ta natsu wurin shiri mai kyau a zamantakewarta da shi. A yau ta amince ba ya sonta kuma k'ok'arin cusa masa sonta ta k'arfin tsiya ba shi ne mafita ba it requires patience and determination, wanda take fatan ya zame mata makami mai k'arfi wajen yak'i da k'iyayyarta. Yanzu lokaci ne da zata fahimceshi da abinda yake so, but how? Shi ne abinda bata sani ba sai dai kuma zata bi shi a yanda yake so d'in taga mai hakan zai haifar.
'Uhmmm' wai in ji mai ciwon hak'ori.

Washe gari haka ta tashi wasai abunta, bak'i ta cigaba da yi kamar yadda gidan amarya yake tarawa. Har su Abba da Umma sun zo gidan, time d'in baya nan dama Abban yace ba wurinshi yazo ba ai ko ta sha gata ranar Abba ya sake jaddada mata akan in yayi mata ba dai-dai ba ta sanar masa. Umma kuma tace " zata kawo mata 'yar aiki" toh kawai tace haka suka tafi suka barta cikeda kewa, haka su Safwaan da sauran samarin familyn su Maheer, Zaheer da sauransu duk sunzo. Suma sun dad'e suna shak'iyancinsu kafin suka tafi sai sauran matan masu aure da kusan a nan unguwar suke zaune.

Abbu ma yazo shi da su prof da Daddy senator da sauran iyayensu maza, basu wani dad'e ba nasiha sukai mata kowa yana maimaita mata muhimmancin hak'uri da kawaici. Hakaza sauran iyayen nasu mata ba su dad'e ba suka tafi suka bar ta a gidan mijin nata.


Two weeks later.

Rayuwarta take ita d'aya kamar ba ya gidan, kamar yadda ya fad'in mata, hakan ko ya sama mata salama a rai da zuciyarsta. Ba ta san fita ko shigar shi ba don ta k'ofarshi yake hidimarshi, though ta kan ji shi a main parlor yana kallo ko wasu ayyukan. Ta kan kuma tararda takeouts d'in shi idan tazo shara da safiya meaning shigo da abinci yake yi hakan ne ma ya sanya dakatar da Umma daga kawo musu.



NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now