CHAPTER 14 ( DAY ONE)

15 2 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

Sai kuka ji ni d'iff jama'a kamar an aiki bawa garinsu, yoh ai ni jama'a baku gaya min haka ake shan wuya a hidima ba sai da nayi na ji a jikina. Waiiii, Allah ya bada zaman lafiya amma mun cud'u jiki yana gaya mana kam ainun, ranar nace zanyi typing ina farawa words suka gudu na rasa mai zan rubuta. Sai kawai na rufe wayar tunda I'm not making sense amma ga compensation page nan kafin in typa main one d'in.

Love you loads

CHAPTER 14 ( Day one)

Baccin da bai yi da wuri ba ya sanya shi makara sosai, don bai iya tashi ba sai after 6. Time d'in gari yayi haske tarwai a d'aki yayi, yana idarwa da k'yar ya iya azkar ya koma ya kwanta yana mai dafe kanshi da har yanzu bai daina ciwo ba.

Baccinsa ya sake komawa sab'anin dare yanzu kam bacci mai dad'i yayi, kuma da d'an natsuwa. Kiran da ya shigo wayarshi ce ta sanya shi bud'e idanu cikeda kasala, hannu ya kai ya janyo wayar tsaki ya sanya ganin videocall ne.

Picking yayi ya zura musu idanu ba tareda yace uffan ba, Farhaan ne ya kwashe da wata muguwar dariya yana cewa " da alamu guy d'in nan k'aramin kai ne dashi, jibi yanda yayi wani laushi". Sadeeq ya kwashe da dariyar shima yana mai cewa " kamar ba sir BAY the great ba".

"Falling heroes ba!!'' Cewar Farhaan.

Dak'uwa yayi musu yana cewa " ku dai an yi lalatattu, gwara da akayi muku aure da wuri gudun yin abun kunya".

Farhaan da ya ajiye wayar a gabanshi ne ya fara tafa hannaye har da rik'e hab'a wurin cewa " ai kaine shugaban lalatattu, wa yayi maganar wani abu yanzu har ka fassara mutane? kace ba k'aramin rigakafi akayi ba da yanzu ka bi kwalta".

" Banzan yaro" ya furta yana gyara zama.  "Wai Islaam me kakeyi ne har yanzu a kan gado.....?". Hararar shi yayi kana yace " I'm doing what they married me off for..." Ya k'arashe har da masa gwalo, ai ba Farhaan ba har Sadeeq sai da suka sanya salati don ya musu bazata shi kam ko a jikinshi doguwar mik'a ma ya sanya yana cewa " wannan fa shiga hak'k'i ne, ya kamata ku san time d'in kiran mijin aure".


Yanzu kam Sadeeq ne yace " Burhaan kar ka manta fa I'm your in-law". Ware idanu yayi cike da shak'iyanci yace " kai ma ai in-lawn Farhaan ne yet a gabanshi kake min zancen banza ". Harararshi Farhaan d'in yayi yana cewa " har ya wuce wanda kake yi? Toh ka dai bi Lelen Hajjah a hankali don wallahi kayi rawan kai zata gyara maka zama ne ahh toh ".

"Ai matata ce ba na wani ba and ba wanda ya isa ya min doka da gidana ehh he". Ya furta har da murgud'a baki, mik'a ya sake yana tashi daga gadon slippers masu taushi dake zube a gaban gadon na Nike farare tas ya zura yana nufar parlorn ba tareda ya sa riga ba.

Main parlor ya shiga da wayar yana mai basu amsa, fuskar a d'an sake. Turus ya tsaya da maganar da yakeyi " ku dai kun shiga uku fallasa sirrin gidan aurenku a duniya......". Sakamakon kyakkyawan ganin da yayi da Nadeefah sanye cikin d'anyen voile fern color anyi mata surfani mai stoneworks a hannu da wuya, rigar ba fitted bace but straight ce ba shape ba komai but yayi mugun yi mata kyau ga mugun k'amshin turarenta ga na wanda take sawa a burners a kusurwan parlorn mai sanya natsuwa a zuciyar mai shak'arshi banda humidifiern da ta kame d'akin gwanin sanyi.

Mantawa da yana kan waya yayi yabita da idanu, in yace ba tayi kyau ba yayi k'atuwar k'arya but yana ganinta sai ya ganta as Suleim not Lele sai da ya zura ido ne ya dawo kan saiti. Tsaki ya ja yana zama a kan couch, a firgice ta waigo don bata san da fitowasrsa ba sai tsaki taji. Ganinshi da tayi ba riga sai shorts sake firgitata yayi, ai ko da sauri ta maida kanta inda yake amma jikinta yana shirin ba da ita all thanks to his fiercy eyes ta ya zuba mata su cikin wani k'ask'antaccen kallo yana ciccije baki.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now