CHAPTER 30 ( HURRICANES)

48 5 5
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

Thanks for all your duas and a very big Ameen to it Allah ya saka da mafificin alkhairi ya bar zumunci mai d'aurewa har gaban abada Ameen ya rabb.

Ummu nashwah wannan shafin na ki ne ke d'aya, Nadeefah na godiya da kyautar suruka da aka ce za a bata tace kar ki ji kin damu ko ba a ba wa ta fari ba za a haifar mata wani mijin😂. Allah ya sassaka ya bar mu tare.

CHAPTER 30 (Hurricanes).

Fad'ar irin wahalar da ta sha b'ata baki ne, don tun tana kuka da k'araji har kukan ya d'auke sai cije bakin da azaba take yi tana kiran sunan Islaam da Hajjah kamar zata fasa asibitin. Suleim da ke gefenta rik'e da hannunta na hagu ne tace " Lele kiyi addua ne please, ki kira sunan Allah ".

"Toh na ji Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, la ilaha illal lahu muhammadur-rasulullah sallallahu alaihi wa sallam !".

"Ki dinga fad'in summas-sabila yassara".

Shi ma sai ta kama ta na ta yi ba k'akk'autawa sai kuma ta ce " kai Suleim wallahi bai yi fa, wayyoni Allah ku kira min Ummuna zan mutu".

Duk yanda aka yi da Nadeefah ta k'i bada had'in kai don sai ihu kawai take yi ta kuma k'ank'ame jikinta, ba su wani dad'e sosai ba Burhaan ya iso da YaMalli da yaje ya d'auko a gida tare da kayan baby. Kusan a tare suka zo da Umma da Mommy da duk suke a rud'e sanin halin rakin Lelen, ai ko sun zo sun tarda a na daga da ita sosai.

Burhaan ne ya shiga labor room d'in don akwai physios d'in da ake yin har theater da su saboda complications na haihuwa, da shi da Dr. Bisola da wasu nurses ne suka rufu kan ta sai dai ta fa k'i ba su had'in kai ko kad'an wanda hakan zai iya affecting babyn ko ma ya mutu ga shi Drn ba ta so ta k'ara ta da kanta gwara babyn ta bud'e ta da su suyi.

A lokacin ran Islaam d'in ya fara b'aci don gani yake da gangan take yi, nan fa ya fara mata fad'a kamar zai ari baki. Dr ce tace " sir fad'an nan fa d'aga mata hankali zai yi wlh, ka barta ta ji da d'aya please".

"In bar ta kina gani tana shirin kashe kanta da babyn?".

Shafa mata kai Suleim tayi tana cewa " Lele please ki saki k'asanta ki kuma din ga nishi wannan d'auke numfashin will only hurt you kin ji love".

"Suleim Mutuwa fa zan yi, wayyoni Allah nah ".

Mommy da duk turka-turkar da ake yi tana ji ne ta shigo cikin d'akin, Islaam da yake muzurai ta fara korawa waje a cewarta da wanne za taji da ciwon nak'uda ko da bambaminshi. Bai so fita ba amma saboda bai iyawa Mommy musu ya sa shi fita daga d'akin, in da yana fita Umma ta rufe shi da na ta masifar akan don me zai rufeta da fad'a ko an gaya masa a yanzu tana a hayyacinta ne?.

Mommy ko ruwan da tayi tofi a ciki ta kafa mata a baki, sai ko ta shanye tas ko kad'an ba ta rage ba. Wet towel ta kai goshinta ta goge mata zufa sannan ta gangara wurin K'afafunta ta bud'e su da kyau da ido tayi wa Dr su cigaba da aikinsu ita kuma ta dafe su, duk yanda ta so ta k'wace ta kasa tana jin ana sa mata hannu a k'asan wanda shi ne abinda yake sake tsorata ta ba komai ba.


Nan ko abu ya sake tasowa gadan-gadan a k'idime tace " zan yi fitsari Mommy".

"Ki yi a wajen kar ki damu".

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now