CHAPTER 28 ( PROUDLY HIS❤)

49 4 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 28 (Proudly his❤)

And today a queen was born, happiest birthday Deejasmah❤

" kar ki damu wife, nan fa gidanki ne so kina da right da duk wanda ya ga dama zai iya kawo mana ziyara as long as bai sab'awa sharia ba. So, calm down go and meet your friends but get ready for me idan sun tafi" ido ta rufe tana murmushi cikeda kunyar abinda yace.

Sake ta yayi ta sake lafewa a jikinshi cike da kunya, duk'awa yayi saitin kunnenta yace " seems like you want it right now, okay bari in ce musu su jira mu kawai ko?".

Ai da sauri ta janye jikinta tana cewa " sai ka fito Yaa" murmushi kawai yayi ya bita da idanu, yana tariyo yanda ya hango damuwa a idanunta a kan zuwan k'awayenta. Is he that special to her or she's just so perfect and unique a cikin mata da ba ta son damuwar shi ko kad'an ko kuma dai tsabar tsoronshi da take ji ne?.

San da ta fito parlorn suna zazzaune abunsu hankali kwance, suna ganin fitowarta suka fara mata tsiya Sophia tace " matar nan kiji tsoron Allah, wa to har da safe ma kina hanyar turaka".

"Ba ga shi nan kina gani an samo tsarabar turakar ba" cewar Ayush tana dariyar mugunta Heedayah ce tace " haba ku kuwa aikin Allah ne fa take yi, ya zaku saka ta a gaba ne ".

Kallonsu tayi tana cewa " wallahi yaran nan kun lalace tabbas, sai fatan shiriya".

"Su waye yaran?" In ji Jam-Jam cike da taajibi, Deeyah tace " ba dole a ce muku yara ba ta shiga in da ko a mafarki ba ku tab'a shiga ba, Allah na gode maka muma nan da 2 months an wuce wurin" kasancewar itama bikinta kafin babbar sallah ne.

Shewa suka saka gabad'aya kamar wasu manyan mata, Nadeefah tace " oho dai ai mun rigaku shiga d'in". Cewa tayi " abinda ita dai turaka ba ta da gwani? K'arshenta dai a labor room ake k'arewa kema kin kusa ai ga su Nana can anyi haihuwar asuba".

"Dan Allah dai, Nana ta haihu? Yaushe?" ta tambaya don ba ta sani ba, ta dai san tana da ciki don ma tayi b'ari sai wannan ne ya tsaya da yanzu ai tayi kusan 3 months da haihuwa tunda an riga bikinta da su.

"Ai ke yanzu kin zama sai Allah ya kawo d'auki kawai, yau da asuba ta haihu Baby girl mai kyau wallahi" In ji Sophia, cewa tayi " Allah sarki Nancy, lemme call her now".

"Ki dai bari zuwa anjima don yanzu dai tana bacci ne, d'azun ma Saudah muka yi magana da ita wai ta ji jiki ne sosai wajen haihuwar" Cewar Deeyah. Cikeda tausayi tace " Allah ya bata lafiya, wayyo Nanata mai sona".

"Saura ke ai kina zare idanu, zaki ga k'arshen so ai ".

"Ku bakinku bai da kyau wallah, sai mugun fata kukewa mutum thank god dai ban da komai balle ku saka ni a ashanar tashi".

Sophia ta bud'e baki zata ba da amsa kenan suka jiyo sallamar Burhaan a parlorn, dukan su natsuwa sukayi suna gaishe shi amsawa yayi a d'an sake ba yabo ba fallasa. Sai dai har da tambayansu ya suke, daga haka ya koma ciki dama bai zauna ba. Bin shi a baya tayi don ya mata alamun fita zai yi, a k'ofar fita ta garage ta gan shi kuwa gabanshi ta k'arasa tana cewa " zaka je gidan Umma ne?".

"Gidan Yaa Budu zan je, sai ki shirya in sun tafi sai ki kirani mu je gidan Adnan ".

"Okay Yaa sai ka dawo Allah ya tsare hanya" Ameen ya amsa sai da yayi kissing d'in ta kafin ya wuce, komawa parlor tayi tana blushing ba ta ko zauna ba ta shiga kitchen ta fara serving d'in su samosa ta d'an sa a mai ta soya ta kawo shi a plate d'in shi daban. Barin su tayi suna ci suna hira ita kuma ta koma kitchen d'in tana d'aura girki fried basmati rice ta musu da dama shi tayi tanadin yi yau yaji vegetables sosai yayi kyau ta zubo ta fito da shi, daga nan suka dasa hira don an dad'e ba a had'u haka ba tun zuwan da suka yi washe garin aurenta. Sauran had'uwar sai a office d'in ta ko ta bi su gidansu don ba laifi tana da zumuncin k'afa sai kuma ta waya.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now