CHAPTER 16 ( A_RIDE_TO_YERWA)

27 2 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

Da yawan mutane are either tired of canned drinks ko basu son su sbd kullum taste Daya ne ga health issues kullum kullum ☹️
Wasu kuma basuson gas din da keh a ciki ne 😏
Wasu kuma kawae basa burgesu ne sunfi son natural abubuwa😗

Ko kunsan wann matslar duk ta rashin iya mocktails haddadu ne?😱 Made from natural abubuwa irinsu Mangoes, Strawberries, Pineapples etc
Wanne ne yasa na shirya mana shararraren CLASS da zaki koya hadaddun mocktails to replace those drinks 🥳💃🏼💃🏼💃🏼

Zaki koyi....
📌Ynda Ake hada Pineapple spritzer🍹
📌Ynda Ake hada Watermelon wonder🍸
📌Ynda Ake hada Mongo mojitos🍹
📌Yanda Ake hada Virgin Kiwi🍸
Wann class da Harshen Hausa ne, kuma KYAUTA. Yes FREE
Join through the Link👇🏼👇🏼👇🏼

https://wa.me/message/W56IOTHO6JIJB1

CHAPTER 16 ( The_ride_to_Yerwa).

Daga ranar basu sake had'uwa ba har su Suliem suka d'aga suka bar k'asar, ta so yi musu rakiya sai dai ba ta samu damar hakan ba don an dakatar da rakiyar kowa daga su sai drivern da ya kai su. Tayi takaici ta ciji yatsa musamman da Aunty Fadwah tace mata wai ai saboda ita ne aka hana, a lokacin ta fara gajiya da kad'aici ga Hajjah da ta kasa ta tsare ta hanata zuwa gida. Ga meeting da ake shirin yi nan da kwana biyu, ga kewa ita d'aya. Yau kam da tunanin gidan ta tashi, ko breakfast ba tayi ba ta kwad'a kiran Hajjah tana mai shirin sa mata kuka.

"In ni ba zaki bari in fito ba ai sai ke kizo ko? Haba don Allah ". Ta furta tana kukan rigima, murmushi Hajjahr tayi tana cewa " in ce ke kika zab'i zama a gidan ke d'aya da yanzu ai kina can kina yawatawa ". Tura baki kawai tayi jin maganar Hajjahr dama ga su Suliem kullum cikin tashin kanta sukeyi a story, tace " ni dai ba wannan maganar ake yi ba Allah Hajjah ina son in fito ke kuma kullum cewa kikeyi ba yau ba".

"Maganar nan dai da ba kya so ayita Lele dole ita za ayi, shin kin manta da abinda na fad'a miki ne? Na gaya miki yawan kusanci a tsakaninku shi zai harfar da shak'uwa mai k'arfi har soyayya ta shigo ciki amma me kika yi Lele? Fatali fa kikayi da damar da aka baki ". Ta k'are da k'wata, ajiyar zuciya ta sauke ta san maganar Hajjah gaskiya ne amma kuma ta ina za ta fara mata bayanin shi wanda akeyi don shi ne yace bai buk'ata? Bayan da kanta tayi shelar ita ce bata da ra'ayi?.

A hankali tace " Ai a gidan ma ana samun shak'uwa ba sai an fita wajen ba, besides ma ai zamu je umrah. Yanzu ni dai ki sa a kawo min car keys d'ina zan zo in ganki duk da dai na lura kin daina so na".

"Ban daina sonki ba Lele saiti nake nemar miki a gidan aurenki ba komai ba, key kuma sai in kin zo ki tafi da kayanki". Tab'e baki tayi tana mai jin kamar ta sa kuka, dabara ce ta fad'o mata murmushi tayi ta katse wayar ba ta ko yi sallama da Hajjahr ba. Number Umma ta lalubo tana danna mata kira.

D'agawa tayi cikeda soyayya tayi sallama, amsawa tayi a kunyace tana mai cewa " ina kwana Ummanah?". Murmushi tayi tace " lafiya lau my daughter, ya gidan?".

"Alhamdulillahi Umma, ya su Abba da Yaa Safwaan?". Ta tambaya tana saukar da murya, amsawa tayi da kulawa " suna lafiya ya naji muryarki so low kina lafiya kuwa?". Murmushi tayi tace " Allah lafiyata k'alau Umma kawai dai kewarku ce ba komai ba ".

Murmushin manya tayi tana cewa " gida kike son zuwa Lele?". Shiru tayi bata iya amsawa ba, sake cewa tayi " toh kiyi wanka ki shirya zaki zo gida yau okay?". K'iris ya rage ta sa ihu sai dai ta daure ta hana kanga yi tace " toh Umma nagode sosai ".

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now