CHAPTER 13 ( #BECOMINGMRSBAY)

33 2 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 13 ( Becoming Mrs BAY)

Mun dawo jama'a ya sanyi?

This page is wholely dedicated to Zeelah Thanks for you duas and well-wishes Allah ya saka da khairan Nadeefah tana gaisheki ainun yaushe zaki je zaman d'aki🌚?

Shirye-shirye aka cigaba kamar ma ba a yi wata magana ba ko da yake ba wanda ya ji ko ya gani balle maganar ta isa ga masu shirin, a hankali har aka shiga satin biki. A lokacin ba k'aramin had'uwa amare sukayi ba ko makaho ya shiga inda suke ya san akwai amaren gata a wurin balle masu idanu da ba wanda yake iya ganinsu bai tanka ba, su Aunty Fadwaah kam har da cewa an nuna musu wariya ai ba irin haka akai musu da biki ba ita dai Hajjah sai dariya tayi ta musu bata ko tanka ba don ta san tayi musu gyaran da ya kamata kawai hange ne yake damun su Najmahn ba komai ba.
Monday

A yau aka fara gabatar da event na biki inda aka fara da bridal shower isu-isu y'an matan da friends d'insu sun ci kyau ainun amma basu yi makeup ba sun ci sunsha sun kuma yi raha a tsakaninsu da friends akayi video aka watse.

Tuesday kuma family hangout/get-together aka yi a Yerwa Gardens. inda kowa ya ajiye aikin gabanshi suka had'u aka yi raha da nishad'i k'aida ne duk biki sai anyi irin wannan had'uwar ba kakanni ba jikoki babu tattab'a kunne kowa sai yazo picnic d'in ba biki kad'ai ba every year sukan yi irin zaman musamman in ba su da shaani. Zama akayi na yini d'aya akayi lunch da dinner tare sai ten suka koma gida, irin zaman ba k'aramin bond yake k'arawa a tsakanin juna ba ko zaman shiru akayi yana sa sabo balle anyi fira an dara sun yi sallahr Zuhr, Asr, Magrib da ishai tare. Anci abinci a circles dukan su an tsokani juna ta hanyar wannan ya d'auke naman gaban wancan wancan ya kwashe abincin wancan abun dai sai san barka babu abinda ya kai zumunci dad'i shiyasa duk da cewa they are quite diverse amma kuma kan su a had'e yake akwai kuma shak'uwa da respect mai yawa tsakanin juna.

Wednesday da safe akayi hair dressing da spa a Yerwa's touch, inda aka gyara kan kowa for free harda amaren da kayan gyara masu tsada sannan suka dawo gida.

4;pm akayi friendly match a Yerwa Court inda aka yi k'wallo tsakanin team Brides da aka bawa sunan Team(SNZ) wato first alphabet na sunan su. Against team grooms Team( BSF) suma haka. Seven aside akayi Mazan family suka shigan ma amare su kuma friends suka shigar ma grooms. Brides maids suna ta cheering Team SNZ inda suka cinye Team BSF 5-3 aka basu trophies aka watse.

Thursday akayi sa lalle wato Nalle inda duka aka taru a gidan Hajjah, Mommy ce ta kawo kayan lallen dukansu. Nan aka shafawa amaren kamar yadda al'ada ta tanadar. Taron yayi armashi sosai saboda isu-isu ne y'anuwa ga amare sun sha kyau cikin atamfarsu mai matuk'ar tsada sai k'amshi yake tashi ta kowani sashe yadda kasan anyi b'arin turare.

Amaren an sanya sun tuk'a tuwon biski aka sanya man shanu, kowa dake wurin sai da yaci aka sha kunun gyad'a mai kyau da gard'i sai sauran kayan alada dai.


Washe gari friday aka yi wushe-wushe inda zamu iya fassara shi da kamu a hausance but su suna fassara shi da " barka" ( barkanku da samun juna a matsayin ma'aurata, barkanku da barin gwauranci da kuma sanya albarka ga maauratan da fatan Allah ya sa mutuwa ce zata raba tsakani). A nan Yerwa hall suka yi amma a outdoor d'in inda akayi decorating d'inshi sosai.

A ranar kam amare sun yi kyau cikin kyakkyawan Gambarar su inda shahararriyar makeup artist da suka d'auko ta tsantsara musu kwalliya, dama ga jiki ya samu gyara komai ya fito.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now