CHAPTER TWO (IF ONLY I CAN LET GO)

30 3 0
                                    

NISFU DEENIY..........

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER TWO (IF ONLY I CAN LET GO..... ).

The whole chapter is dedicated to Abubakar Ismail( Yaya Abba), my number one supporting system, Allah ya kare mana Kai ya biya maka mafi kyawun buk'atunka. Ya baka mace ta gari.

https://chat.whatsapp.com/HHFgiJEtgxTBRNR9aEDZv9

Grill🌺🌼
Too much of something is not good🌚.

Ko data idar da sallahn bata fita ba, saboda bata san ta ina zata fara sanarwa Hajjah abunda yai mata ba hakan yasa tayi kwanciyarta. Waya ta d'auko ta kira Suleim sai dai ba tai picking ba murmushi tayi kawai ta kunna data, Pinterest ta shiga tana pinning latest arts d'in ta tareda duba downloads d'in ta da kuma likes. Murmushin jin dad'i tayi ganin zanenta yana samun karb'uwa, fita tayi ta koma WhatsApp ignoring messages tayi sai da ta turawa Lovien nata message d'in ban hak'uri kafin ta fara duba wasu ta na replying.

Sallahn isha'i ne ya tadata sanda ta idar zama tayi tayi tilawar haddarta kafin ta tashi, komawa gado tayi ta na kiran Ummu video call. Sun dad'e suna hira da iyayennata har ta ringa jin wata zazzafar kewarsu ta na kamata, har ta yanke shawarar ko 2 weeks bata k'arawa a Kaduna za taje gida hutun ai ya isa haka nan.

Around 9:30 Hajjah ta shigo da sallama bayanta kuma Yanah mai aikinta ne hannunta d'auke da tray madaidaici, wanda ba shakka abinci ne. Tana a kwancen da take amma yanzu k'afarta ta zuro ga rug d'in gaban gadonta sai bayanta ne kawai a kan gadon, ta na mai kallon sama har lokacin chat takeyi a school group d'insu.

Ko da suka shigo bata tashi ba sai da Yana ta ajiye kayan hannunta, ta fita kafin Hajjah ta zauna a gefenta wayar ta zare daga hannunta kafin tace " b'oye-b'oye ba shi zai fisshe ki ba Lele, don yanayinki kawai ya nuna ba a samu nasara ba wacce kuma na tabbatar na shaida miki rashin tabbas d'in ta".

Tashi zaune tayi tana jingina da board d'in gadon tabbas Hajjah ta gargad'eta a kan tunkarar Islaam da maganar soyayya amma tayi biris da gargad'in. Har gani take kamar babu mahalukin da zai tab'a rejecting d'in ta ashe motar alfa ta hau, gashi ta d'ebe ta ta dire a kwanar da babu rumfa balle ta samu mafaka.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin cikin murya mai cikeda fargaba tace " Hajjah kema kina ganin cewa wahal da kaina nakeyi ko?". Gyad'a kai tayi ta bata amsa da " ba zance wahal da kai kike ba but kusan hakan ne kuma ba zan lamunta sa kanki a damuwa da zakiyi a kan Burhaan ba".

Idonta ne ya kawo ruwa ta shanye da k'yar tace " ba zan iya jure rabuwa da shi ba Hajjah!". Dafata tayi tace " hakan kuma ya zamar miki dole, tunda dai ba manema kika rasa ba ki bawa wani dama kawai", girgiza kai tayi tace " a baya na gwada yin hakan sai dai ko iyawa banyi ba na gaza, Hajjah son da nakewa Yaa Islaam mai zafice irin wacce ban tunanin zan iya dainawa ko me zai min kuma zan daure".

Kallon mamaki da tausayi ta bita dashi under her breath tayi muttering " Álà bárgà càkkó ( Allah mai girma)". Nisawa tayi tace " nima kuma ba zan jura ganinki cikin damuwa a silar shi ba....." Katseta tayi da cewa " then help me have him,,,,that's all I want", shafa kanta tayi tace " ki natsu ki kuma nemi zab'in Allah ki sawa kanki salama idan babu alkhairi a tattare daku sai ki yakice shi a rai da rayuwar ki".

"In kuma shine alkhairi fa?" Ta tambaya cikin sanyin jiki, ajiyar zuciya ta sauke don ita a kullum mamakin irin son da Nadeefah takewa Burhaan take yi wacce bata tab'a jin irinta ba sai a hikayoyi ko k'agaggun labarai tashi tayi tace " shi ma sai ki rok'i Allah na tabbatar zai fito miki da mafita". Murmushi tayi kafin tace " kece mafita ta Hajjah, kuma nasan kinsan yanda zakiyi".

NISFU DEENIY.......!Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum