CHAPTER ONE (REJECTION)

48 4 1
                                    

NISFU DEENIY.......!

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER ONE ( REJECTION).

This chapter is wholely dedicated to nisful hayatee, qurratu ayniy the woman behind my success. My Mom my wonder woman, without her by my side I won't be where I am today thanks for everything Mammah. Allah ya albarkaci gabanki da bayanki ya kare mana ke a koina, lafiya da nisan kwana Hayatee❤🌹.

https://chat.whatsapp.com/HHFgiJEtgxTBRNR9aEDZv9

Zaune take a gaban madubi tun d'azu da ta fito wanka d'aure take da towel a jikinta, kallon creamy soft skin d'in ta takeyi a zahirance. Amma a bad'ini tunani mai zurfi ta tafi, yayinda fuskarta ta cika da mayalwacin murmushi wanda ba komai ya assasa shi ba face ganin burinta yana kan gab'ar cika a yau d'innan.

Tun d'azu take tsaye a kanta amma bata sani ba saboda zurfin da tayi a duniyar tunaninta, dafa kafad'arta Hajjah tayi hakan ya sa ta juyo a d'an firgice ganin wacce ta tab'ata ne ya sanya ta tale baki a shagwab'e tace " Alah kàrwùkámmà! ( kin tsoratani!)" Haratarta tayi kafin tace " kin zauna tun d'azu a nan ai dole kiji tsoro".

K'aramin bakinta ta tura sama ba tai magana ba Hajjahn ce tace " wai kin tashi kin shirya ko sai yazo ya ganki haka a zaune?". Dafe k'irji tayi tace " ina jin tsoro a k'asan raina, I don't know what it means" dafata ta kuma yi cikin muryan rarrashi tace " ba abunda zai faru habibtie, ki kwantar da hankalinki". Gyad'a mata kai tayi kana ta janyo cream ta fara shafawa jikinta.

Cikin doguwar riga nude color ta shirya, coffee brown d'in veil ta yafa a kanta wanda hakan yai exposing brown well oiled hair d'inta. Turaruka ta shafe jikinta dashi kafin ta fito, a parlor ta tarda Hajjah zama tayi kusa da ita tana d'aura kanta a kafad'anta tayi shiru. Patting bayanta tayi a hankali a kunnenta tace " Álà kámbò ( Allah mai girma), yau Lele ce take jin tsoro?" girgiza kai tayi kawai amma bata tanka ba.

Janta tayi da hira har sai da ta d'an sake kad'an, suna zaune a wurin akai honk a gate baa jima ba motar ta shigo gidan. Hakan nema ya sanya ta tashi zaune, Hajjah tace "
ákkònjú ( ga shi nan yazo), ki tafi a natse kar ki bada mata " dafe k'irjinta da ya k'ara bugu daga shigowarshi gidan tayi tana cewa " in shaa Allah Hajjah, you too should pray for me". Cewa tayi " you have my blessings dear, Allah ya sa a dace".

A dai-dai lokacin wayarta yai k'ara tana dubawa sunanshi ne ke yawo a screen d'in picking tayi tareda mak'ala wayar a kunnenta. Cikin kamammiyar voice d'in shi yace " I'm outside", kafin ta samu zarafin amsawa ya katse hakan yasa ta mik'e a natse ta kalleta " ya na waje barin ganshi", jawota tayi tana cewa " a haka zakije babu abun tab'awa?, ki d'aukan masa ko ruwane mana".

Girgiza kai tayi tace " No lemme see him first, may be ma ciki zan shigo dashi ", ok tace alamar fahimta yayinda ita kuma ta fita zuwa wajen.

A zaune a cikin motarshi yake yana mai kallon entrance door d'in, tsaki yayi ganin bata fito ba kuma ya tabbatar ta ji zuwanshi ba dai tana nufin shi take jira ya shiga daga ciki ba?. Hakan ya sa ya d'aga wayar shi number ta dako saving baiyi ba ya latso ringing biyu ta d'aga ba tareda ya bata damar magana ba don ko sallama bai mata ba yace " I'm outside" ya katse wayar ya na cewa ' I'll surely deal with you today, stupid!' In a bitter tone.

Ko bayan kiran nata sai da tayi kusan 3 mins kafin ta fito, yayi tsaki ya gaji don gani yayi kamar 30 tayi a ciki. A tsanake ta doso shi zura mata idanu yayi trying to figure how could she be beautiful yet d*mb, he knows she's so clumsy and spoilt but never thought she can stoop this low. " Vanity" he muttered!.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now