CHAPTER 18 ( HER EFFECT)

26 2 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 18 ( Her Effect)

Our own Barr. Aunty Maryam this page for you your comment and love for this book is a motivator for this chapter, go on soar higher and be someone we'll all be proud of. Allah ya tsare mana ke a duk inda kike ya kuma ba da nasara ga abinda kika sa a gaba, be safe out there and always remember that we are all looking up to you.

I love you much🥺😍❤

A yau ma shirye-shiryen meeting suke yi, ga shi ta tashi a makare wanda ba ta san dalili ba. Wankan ma a gaggauce tayi sannan ta tsaya shiryawa, lokacin har ya fito yana zaune a parlor amma babu mai kama da ita. Kallon agogo yayi ganin har goma saura minti bai fi biyar ba, tsaki yayi ya tashi da shirin kiranta ne sai ga k'amshinta da ya haddace nan alamun ta iso. Kallon inda take yayi nan numfashinsa ya kusa d'aukewa ganinta da wata fitinanniyar riga da skirt da suka kamata tsam.

Tsayawa yayi yana kallonta, in ba gizo idanuwanshi ke masa ba sai yace har hips yaga tayi. D'aure fuska yayi ganin ta k'araso gabanshi tana cewa " I'm sorry Yaa, wallahi ban san ya akayi na makara ba". Bud'e baki yayi da niyar yace mata " amma kin san baki isa bi na da wannan kayan ba ko?" Sai ya ga tana warware lafaya ajiyar zuciya ya sauke, sai kuma ya kawar da idanuwanshi daga gareta.

Ita ko gaban madubi ta isa kawai ta fara k'ok'arin nad'awa, cikin lokaci k'ank'ani ta kammala. Kallon kanta tayi a madubin tayi kyau ainun don ruwan lafayar bak'i da zubin zuma da aka k'awata shi da shi ba k'aramin hawa yayi da kalar jikinta ba. Murmushi ta sake yi da ya k'awata fuskarta sai ta saita wayar ta fara snapping kan ta, har ma da Aortan nata ba tareda ya sani ba ma.

Isowa wajen da take yayi dan ya gaji da jiranta, damar da tayi using kenan tayi snapping d'in su wani hoto mai d'an karen kyau. Bai tanka mata ba sai agogon hannunshi da yayi mata nuni alamun time ya na tafiya, kana ya juya zuwa waje murmushi ta bishi da shi sannan ta bud'e fridge d'in dake dining milk drink ta d'auka da bag d'in ta.

Kamar kullum addua ta tofe d'akin da shi ta kashe kayan kallo, ta kuma rufe koina sannan ta rufa mai baya. Lokacin har ya tada motar, bud'ewa tayi ta shige shi kuma ya ja motar suka bar gidan. Babu mai magana cikinsu shi idanunshi suna kan hanya while ita tana sipping drink d'inta cike da yanga tana latsa waya.

A gaban hall d'in yayi parking kusan a tare suka fito ita da shi, hakan ne ya sanya suka jera wurin shiga cikin hall d'in. Su na shiga hankalin kowa ya komo kan su don yanda suke tafiyar kamar irin shahararrun masoyan nan, dukda yanayin fuskar Burhaan d'in babu walwala amma hakan bai hana fitowar k'ayatuwar tasu ba.

Zulfaah ce ta fito da waya ta fara d'aukarsu hotuna, don sun mugun birgeta ba kad'an ba. A haka har suka k'araso wajen iyayen, a tare suka dinga zagaye tables suna kai gaisuwa har kan yayyinsu na gaba kafin suka zauna. Rungume juna sukayi ita da su Suliem a kunne ta rad'a mata "you look good together". Murmushi tayi tana mai cewa "thanks love" daga haka suka cigaba da gaisawa da sisters d'in da ke table d'in su.

Zaman su babu jimawa su Hajjah suka iso kamar yadda ta saba haka tayi, sai da suka zazzauna kafin aka kowa yaje ya kai gaisuwarshi. A haka har aka kammala daga nan Baba Tijjani ya tashi ya bud'e taro da addua, tareda gabatar da agendar zama. Sosai aka tattauna akan muhimman abubuwan dake fuskanto su da kuma yin tituna da street lights a sabuwar unguwar da suka siya a wurin rigasa. Gabad'aya meeting d'in ranar akan business ne sai kuma d'ad'd'aikun matsalolin da ba su da wahalar shanyo kai, Zuhr aka tashi kowa ya tafi yin sallah.

NISFU DEENIY.......!Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu