CHAPTER 20 ( SHE'S TO SOFT)

37 4 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

Alhi wattpad sannunku da k'ok'ari tunda 'yar comment da vote d'in ma kun daina sai dai reads but ba kwa rating storyn mutum, shiyasa ma nayi posting 17 na manta da ku, a dai gyara gaskiya ko in k'yaleku in dawo WhatsApp in tare abuna.

Wannan shafi tukuici ne ga all team Nadeefah living out there, make you guys make some noise let's scare team Burhaan, wato soyayyarku daban take ita ce ma ke bani energyn typing ko ban shirya ba💖.

Na san page d'in nan yayi kad'an in zayyano kalar so da k'aunarku but i'll take my time and start appreciating your efforts daga chapter 21 da zai zo anytime soon but kafin nan ku had'u k'asan page d'in nan ku wataya😘😂.

CHAPTER 20 ( She's too soft)

A firgice ta bud'e idanu jin saukan wani abu mai d'umi da danshi akan lips d'in ta, nan tayi arba da fuskar Burhaan da ya lumshe idanu yana k'ok'arin kissing d'in ta. Janyewa ta fara k'ok'arin yi ta hanyar matsar da fuskarta baya, amma unfortunate for her ya riga da ya dafe kanta ta baya bud'e baki tayi da niyyar magana ai ko hakan ya zama tamkar wani dama ta bashi don ko claiming bakinta yayi da kyau yana yanda ya ga dama da ita.


Tun tana mutsu-mutsun k'wacewa har ta saduda ta zurawa sarautar Allah idanu, yayinda hawayen da ba ta san ko na menene ba suka hau aikin zarya akan kuncinta suna sauka akan lips d'in ta. D'and'anonsu da yake ji bai sa shi janyewa ba sai ma manne mata da ya sake yi, sai da yaji kamar numfashinsa zai d'auke ne sannan ya janye gasping for air. Time d'in ita ai nata yayi k'aura har ya dawo ba tareda ta sani ba, yana sakinta ko ta fad'a kan gadon lak'waf don tuni ya riga ya rabota da kan stool d'in da take zuwa kan jikinshi.


Maida numfashi sukeyi ita da shi kamar wainda sukayi gasar tsere, sun d'auki lokaci mai d'an tsayi a hakan kafin ya bud'e idanun shi da ciwo da jaraba ya sauya kamanninsu ya dubeta. Ware idanu yayi ganin har lokacin hawayenta suna zuba, hannu ya kai ya tab'o su sannan ya bud'e muryar da ta riga ta canja kamar ba tashi ba yana cewa.

"Wannan dai kukan munafunci kike ba komai ba, abinda fa kika dad'e kina kwana addua shi na yi miki then what's the big deal ko dai kukan murna ne kike yi?" Da sauri ta bud'e idanunta tana kallonshi da mamaki, waro mata mayun idanunshi yayi ya sake furta '' yes you've been praying for this very moment, ga shi kuma na baki abinda kike son. So you should be thankful to me for that don na baki cikon burinki kin ga ko yanzu kika mutu you are contented, so chill taimaka miki nayi ". Daga haka ya sauka daga gadon with zero to little energy ya nufi hanyar toilet, da idanu ta rakashi cikeda alajabi.


Sai kuma ta saki murmushin tuno kalamanshi, wai taimaka mata yayi ko dai ya taimakawa kan shi?. Ta san tabbas tana son shi tana kuma adduar daidaituwar zamansu cikin lokaci k'ank'ani but bata tab'a exceeding limit d'inta ta hanyar tunanin kasancewarsu a yanayin d'azu ba, abu ne da ya fi k'arfin tunani ko lissafinta yau sai gashi ta farka cikinshi amma kuma ya wani lak'a mata. Cije leb'e tayi tana sake zurfafa a tunaninta kan shi da lamarinshi, hakan ya sa bata san fitowarshi ba sai saukar ruwa da taji a kan fuskarta.

Da sauri ta kalle saitin da ruwan ya feso mata, shi ne tsaye shamelessly sanye da towel fari k'al. Yana jifanta da wani irin kallo saurin kawar da fuskarta tayi, shi ko tab'e baki yayi cikin ko in kula yace " wai ke hala ba kya sallah ne? Tun d'azu muka tashi amma kina kwance sai juyi kike akan gado. Bayan kin gama cin barci kamar ba jinyar mutum kike yi ba har shi patient d'in ya riga ki, ko haka ake jinya a garinku oho ". Ya k'arashe yana mai juya mata baya, kallon agogon dake mak'ale a bango tayi 6:28 da sauri ta tashi tana mai istigfari a ranta.


NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now