CHAPTER 22 ( NO, I DON'T)

26 5 1
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

An ce wai ni duk book sai nayi dedicating wa Jasmine chapter, kuma har book guda fa nayi dedicating mata. Ko wani chapter sunanta ne yake yawo a kai, ni ko nace ai ko duka writing career na zan dedicating ma ta ai bai kai ya nuna girman ta a gare ni ba kuma ban fad'i ban in dai na tuna ma'anar kalmar halacci. Yoh so na take yi sosai da duk wani abunda ya shafe ni, in na nuna nawa da iya abinda nake da shi shin laifi ne?. This chapter is also yours Masoyi Allah ya kare min ke a koina kike a cikin duniyar nan ya tsare gaba da bayanki ya kuma d'aura ki bisa abin k'i, ya hana mahassada ganin abin fad'i a tsakaninmu ya bar mana zumuncinmu har gaban abada😍❤. I too love you aradu🥺.

CHAPTER 22 ( NO, I DON'T!!)

Kwanciya kawai yayi yana mai juyi yayinda yake jin mugun haushin Nadeefahr da period d'in na ta, tsaki yayi yana mai ayyana yanda ya sa rai amma ta b'arar masa da komai. Shi sai yanzu ma yake nadamar k'in bata magana da bai yi ba, ai ya tabbarar akwai maganin da zai iya sa jininta ya ragu amma ya k'i sai ga shi yanzu shi abun yake cuta kuma tunda dai shegen abun ya k'i tafiya. Doguwar tsuka ya ja yau ta ja ma kanta ko d'an kiran da aka saba mata na dare ta kwana a room d'in ba a yi ba, duk da kuwa kwad'aita masa hakan da zuciyarshi take yi.

Ita ko bayan wucewarshi da wayarta da Suliem kwasar 'yanmatan k'afafuwanta tayi zuwa d'aki, shirin bacci tayi duk da dare bai wani yi sosai ba haka ta kwanta. Sai dai kamar yadda shi ma ya kasa ita ma kasawar tayi, da ta gaji da juyi sai kawai ta mik'e artroom d'in ta ta shige ta fara zanen duk abinda ya zo kanta. Ta na yi ne but hankalinta yana kan shi, tunaninshi take da halinda yake ciki amma kuma ta san zuwanta d'akin tunzurashi zai yi ba komai ba shiyasa kawai ta dake da sunan za su had'u da safe. Wannan rashin zuwan ko ba k'aramin k'ara masa takaici yayi ba, don ya gaji da duba hanya har ya saduda ya kashe wuta kawai ya cigaba da juyin da ya saba har Allah ya taimake shi ya samu bacci da wuri.

Ita ma ba ta wani dad'e ba ganin ba wani abu mai hankali take zanawa ba kawai ta wuce ta kwanta, tunanin maganar Suliem ta tafi a take tayi amanna da suggestions d'in nata ta yanke hukunci kawai gwara a yi ta ta k'are ta ba shi abinda yake so ko dan tabbatar kwanciyar hankali mai d'aurewa a tsakaninsu a kuma samu tsiron k'aunar da su d'in suke fata.

Da safe fayau ya tashi don har da kiranta da asuba wai ta tashi tayi sallah, da murmushi ta amsa tana sake ta'ajjubin halayyarsa he's very dynamic ba ka isa ka gane inda ya dosa ba. Ta ga kamar ta san shi ashe da sauranta tunda kusan kullum sab'awa tunaninta yake yi.

Sallahr tayi ta koma ta sake kwanciya don baccin bai isheta ba, alarm tayi setting sai 7 ta tashi. Daily cleaning routine d'in ta tayi ta had'a musu breakfast na French fries ta had'a ketchup da mayonaise wuri d'aya da d'an paprika ta jujjuya ta sa a wani k'aramin bowl ta sa a fridge, sai kuma pancakes d'an kad'an da tayi musu wanda bai shige 10 pics ba. Ta dafa ginger tea ta had'a komai a kan dining ta ajiye, wanka ta koma ta yi taking her time as always wurin pampering jikinta. Shiryawa tayi cikin lace mara nauyi plainburnt orange color d'inkin top da skirt da ya samu jikinta yayi hugging da kyau ta fito cas kamar 'yar tsana, ba ta shafa powder ba sai kwalli da ta sa a idanunta kamar kullum.

Turare ta zuba a kowace sak'o na jikinta kafin ta nufi d'akin na shi, bedroom d'in sa ta nufa daidai da fitowarshi daga toilet. D'an dakatawa tayi ganinshi a hakan, shi ko ko a jikinshi sai ma hannunshi da yake ware mata. Cikeda kunya da aji ta nufi inda yake a tsaye, sanyata yayi cikin k'irjinshi tayi luff tana shak'ar k'amshin bathing soap d'in shi da turaren wankanshi mai k'amshi.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now