3

605 25 2
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

      EPISODE 3️⃣

        ✍🏻M SHAKUR

4 daidai tashiga wani babban kanti na abinci irin local restaurant din nan, wata katuwar mata dake zaune a tsakiyan shagon kan kujera ga lalitan uban kudi a hannunta tana kirgawa ne ta kalleta tace "Allah yasoki baki latti ba" batace komiba kai tsaye tace "ina wuni Maman Miwa" batare data amsaba tace "nidai je ga wanke wanken ki chan na jiranki" bata damu da yanda tamata maganan ba dudda akwai mutane a shagon sunacin abinci tace "bari nai salla naje nayi" bata jira amsanta ba tawuce ciki chan bayan gidan shagon bayi taje tacire kayan jikinta tafito da dogon riga na abayan dake jakanta tana neman gyalen ta tuna tabawa mutumin nan tsayawa tayi chak sai kawai taja gajeren tsakiya saurin datake tazo nan yasa ta manta bata amsaba, karamin farin hijabin tasaka ta dauro alwala tafito tasami waje tai salla sannan ta cire hijabin tasa kan igiya fari ne batason ruwan wanke wanke ko mai ya bata mata taje gaban makwarara, ga wanke wanke zaka dauka na gidan biki ne ga manya manyan tukunyan abinci, omo ta dauka ta tara ruwa abaho dukta kawo sannan ta dauki wayanta kirar vivo duk taci screen tasaka earpiece ta danna waka ta soke wayan aljihun dogon rigan tashigayin wanke wanken da sauri sauri dan tanada kuzari sosai batada kasala ko son jiki.
Wata yar budurwa ce tazo wajen ganinta tana wanke wanke tana waka kasa kasa like zero worries dinnan yasa ta harareta tajuya tafito tadawo cikin shagon tazo gaban mahaifiyarta dahar lokacin take kirga kudi tace "wai Mama Yar gidan HIV dinchan kikesa take mana wanke wanke har yanzu banace ki sallameta ba gashi gashi abinda ake cewa ita da Mamanta sunada shi" batare da maman ta kalletaba tace "koyar gidan kanjamau ce ba HIV ba ina ruwana ko kinada wanda zaki samo dazatamin wanke wanken nan ta share ko'ina har zuwa katon shagon nan akan dubu biyu kullum aduk fadin garin kanon nan?" Baki yarinyar tabude zatai magana Maman Miwa tace "kinga ki kyaleni fa, nagadai nace kiyi aikin nan bayi zakiyi ba" dasauri yarinyar tace "Mama ni kyamanta nakeji wlh, sunada HIV tana mana wanke wanke" dasauri Maman Miwa tace "wai sau nawa zan gayamiki Maman ta kedashi ba itaba yarinyar datake karatun likita, to koma tanadashi me ruwana nagadai ciwon nan ajini yake kuma baya kwarara acikin ruwan wanke wanke ko? Miwa dan Allah ki barni na kirga kudin nan kinatasa ina mance abinda na kirga" tsaki yarinyar tayi tawuce tafita daga shagon cikeda bacin rai.
Kafin 1hr tagama wanke wanken nan tass, tukunyoyin har bayansu ta wanke kal sai kyalli suke ta share ko'ina tashigo shagoma ta share tsaf tai mopping lokacin biyarda rabi sannan takoma baya tasa hijabinta tadauko jakanta ta goya abaya tafito tazo gaban Maman Miwa tace "nagama" kallonta Maman Miwa tayi tace "ohh kudinki ko"? Gyadamata kai tayi, kudin hannunta Maman Miwa tashiga kirgawa taciro 10k tabata tace "gashi na litinin zuwa yau juma'a" murmushi tayi for the first time dan gaskiya she hardly smile kaganta tana murmushi ko dariya to sai in tana tareda Mamanta, takirga kudin tass dubu goma chip chip tace "nagode Allah yabiyaki" tajuya tawuce kallo Maman Miwa tabita dashi ance duk muguntan ka kaji an maka wani addu'an saikaji ranka ya sosu harta fita waje Maman Miwa tace "Rasheeda!" Dasauri yarinyar tajuyo jin an kirata, komawa cikin shagon tayi tace "na'am gani" kallon sales girl dinta Maman Miwa tayi tace "samata shinkafa da tuwo a takeaway takaima Mamanta" wani kalan murmushi tayi dayasa wani hot dimples suka lotsa a kumatunta Ya Allah! She looks damn beautiful dasauri tace "nagode sosai, nagode nagode" Maman Miwa sai kallonta take dan wlh today is the first time in almost 3months data fara musu aiki take ganinta tana murmushi, yarinyar kam badai kyauba, ta tabbata badan cutan su ba da tuni wani babban Alhaji ya aure ta, kawomata abincin akai a leda ta amsa wannan karan saida ta duka tace "nagode sosai Maman Miwa" murmushi Maman Miwa tamata tace "sai Allah yakaimu  gobe" gyadamata kai tayi tafice Maman Miwa tabita da kallo wani zubin she wants to be wicked amman kuma indai kai ba shaidan bane u can't be wicked to this girl cus zata maka aiki tsakani ga Allah dabazaka taba ganin abinda zakai complain akai ba, wanke wanke take maka tsaf, tai shara tai moping kaga ko ina na kyalli, banda haka  daidai da tsinke bata taba sata a shagon ba wlh ko kwayar magi bai taba bataba dudda ko basudashi, kowa ya tsaneta kowa kyaranta yake sabida Mamanta but if u look at it ciwo nakan kowa, zata gudu tabar mahaifiyarta ne sabida tabada HIV? No, ba HIV ba ko HIVVV uwarta kedashi uwarta ce, dudda ma taji labari ance mai kudi mahaifiyarta ta aura but taje tai fasikanci tasamo HIV yakorota yace cikin ma ba nasa bane, hmmm tasauke ijiyan zuciya tace "Allah ya kyauta dai".

SANYI DA ZAFIWhere stories live. Discover now